Showing 24001 words to 27000 words out of 46557 words
Chapter 9 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf
Zafi kuwa ai yana Saudi
Arabia”, yace “kiyi min alfarma mu Arabian Bride, na san ke dinnan ma’abociyar tsinkaye,
fahimta, da yi min uzuri ce, bazan iya shiga dakin Sumayyah inda kike ba kusa da dakin
mahaifiyata ne, ba zan iya tsallake dakin Mama a gidannan in dinga zuwa inda kike ba, amma
already nayi kokari nayi mana booking na komawa Jidda, don ni garin Kano ya fita kaina, zamu
tashi rana ita yau in sha Allah muje mu ci duniyar mu da tsinke.
Na yanke shawarar karbar aikin nan na Saudi-German”.
Farin ciki mai yawa ya cika fuskar Madinah da zuciyarta, don dama tana cikin tunanin yadda
zata iya rayuwa a garin Kano, ta shiga damuwa akan yadda zata iya rayuwa a Nigeria ma in
general, tana dai daurewa ne albarkacin soyayya da yadda kowa nata ke lallashin ta, yayyenta
kuma suke gaya mata aure babu inda baya kai mutum har bukka a jeji, amma hakika tafi son
cigaba da rayuwa a Jeddah.
A can aka haifeta acan ta rayu, acan ta girma. Abinda ta sani ta kuma yarda da shi kawai
shine; ko a cikin ruga zata iya rayuwa in dai da Sarham Abbas ne, kuma in dai zasu kasance
tare karkashin alfarmar aure da ni’imarsa itada shi har karshen rayuwar su.
Sarham ya katse mata tunani, “kin amince ko?” Da sauri Madinah tace “haba-haba ai nima
zan fi son hakan, da kunya kam mu kebe ko na minti biyu ne alhalin Mama da Abba suna cikin
gidan, Allah ya kaimu lafiya, ni da ka kara mana wani satin ma a kan dayan ya zama munyi biyu
tareda su kafin mu koma”. Yace “no, zamu tafi rana ita yau in sha Allah bana son zaman garin
ne”. Ya tambayi Madinah ko me take yi yanzu? Ta ce ta yi wanka ne zata kwanta, ta gaji sosai,
tace tun saukarsu a Kano bata huta ba. Sarham ya ce,
“ai kuwa baki ga ta barci ba, kamar yadda nima ban ganshi ba. On this special day, ki tashi ki
dauro alwallah ki yi sallah raka’a biyu nima zan yi yanzu, mu godewa Allah da ya cika mana
burin mu da cikar alkawuran da muka yi wa juna yau shekaru goma!
Kada ki manta a cikin sujjadar ki ta karshe ki roka mana ‘long life, prosperity, blessed
children, unending love, and infinite peace. Madinah ina fatan ki zamo min ‘shelter’ kamar
yadda birnin Madinah ya zamowa Annabin mu Shelter, refuge, security, safety and peace!”.
Madinah ta lumshe idanunta cikin farin cikin da bazai misaltu ba, tace “kaima ina rokon
ka roka min aljannah, don Hajjah Ramlah ta gaya min aljannah ta yanzu ta tashi daga
dugadugan su ta dawo bisa dugadugan ka.
Ka roka min ‘ya’ya masu yawa tare da kai kuma masu albarka, ka roka min Allah ya
mallakamin zuciyar Sarham dina, nikadai raina bakidayan ta, don itace kadai ‘weakness’ dina a
duniya (zuciyarsa)”.
Finally, daga yau dai, sunansu ya tashi da ‘honorifics’ tunda ya koma Mr&Mrs. Dr.
Shanono. Bayan tarihin fafutukar soyayyar shekaru goma!!!
**** ***** ****
A kwanaki bakwai din da Madinah tayi a gidansu Sarham, ta saba da kowa, kuma ta
samu karbuwa ba laifi a wurin iyayen sa musamman Abba Prof. da yake ganin girman Kakan ta
mai rasuwa Alkalin Alkalai, duk da ba wai sanayya ce a tsakanin su ba, amma yayi masa farin
sani a matsayin daya daga cikin iyayen Kano. Ta fannin Mama kuma, ta zauna ne daga gefe
tana laqantar Madinah a ma’auni na adalci da son sanin hakikanin halayen ta, inda a dan
zaman su tare ta fahimci Madinah wayayyace, Madinah mai ilmi ce, bata da matsala sai ta
rashin kawaici a kan Sarham, in bata gan shi ba sai ta ishi kannen sa da tambayar ina yake,
wanda ke nuna zata yi kishi akan sa sosai, idan ya fita bazata nutsu ba sai ta ji shigowar sa
gidan, tana da bala’in jan aji amma akan Sarham babu ajin ko kadan, don bata iya boye son da
take masa a gaban iyayen sa da kannen sa.
Gata da halaye na kowa tasa ta fishshe shi, wato halayen nasara, kai bazaka ce girman
kasar larabawa bace, amma kuma duk da haka tana girmama su, musamman su iyayen sa, ta
fahimci Madinah ta san abinda take yi yadda ya kamata, tunda duk rashin kawaicinta data
fahimta, a duka kwanakin nan bakwai data yi tare dasu, bata tsallake su ta kebe da Sarham ba,
ko ta bi shi inda dakinsa yake, ita da shi sai ko a waya, ko in ya shigo ya taddasu duka a falo,
sai ya zauna ayi hirar tare da shi, amma baya sakewa musamman in Mama na wajen, tana
kallon Madinah na kashe shi da murmushi.
Shi da kan sa Sarham ya fahimci wani abu, wato tun bayan zuwan Madinah, mu’amalar
sa da Sumayyah ta ja baya, Sumayyah ta daina shiga sha’anin sa sam, ko wuri ya shigo tana
dariya sai ta daina, ta yi fuska. Ta daina kai masa abinci ko gyaran dakin sa wanda aikinta ne.
A’ah, tun baya damuwa har ya fara tunanin laifin me yayi mata don wannan ba halin ta bane,
me yasa ta daina ajiye masa abinci ko kiransa yazo ya ci, da gyara masa daki alhalin ta san ba
wai Madinah ta tare bane, da zata cigaba da yin wadannan hidimomin da tazo ta tarar tana yi
masa.
Yau ya fita can karshen layin su yana wata irin romantic waya da Madinah, don
hakurinsa kusan ya fara karewa da takunkumin da ya sanya musu, haka suke yi yanzu kullum
da yamma in jama’ar gidan basa nan ko suna wasu sabgogin a kitchen, ko can dare in kowa ya
kwanta, sai ga Sumayyah ta karyo kwana tana tafe cikin nutsuwa, ta zo har inda yake ta gifta
shi bata ce masa ko sannu ba, har ta zarta shi kadan ya kashe wayar ya saka a aljihu, ya ce,
“Sumayyah!”.
Sumayyah ta dan dakata amma bata juyo ba, ta daure fuska sosai, ya ce “ko ba da
Sumayyah nake magana bane?”
Ta dawo ta tsaya a gaban sa tana tura baki gaba, ya ce “kin gama hada kayan naki?” Ta ce
“hada kaya kuma? Ina zani?” yace “eh, Abba bai gaya miki da ke zamu tafi Jeddah ba, zaki
zauna a gida na ki fara MBBS? Tukunnama wai me nayi miki kike gaba da ni haka? What’s
wrong with you?” Sumayyah mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta soma hawaye na
babu gaira babu dalili, tace “wallahi in dai a gidan ku zan zauna to na fasa karatun a can, ni ba
don kai da matar ka zan je Jeddah ba, ba ‘yar zaman daki kuka samu ba, zani jami’ar Sarki
Abdulazeez ne, zaman karatun kaina, kowa yayi rayuwar sa a inda yake zaune duk da muna
gari daya”. Cikin madaukakin mamaki Sarham ya ke duban Sumayyah, da babbar murya yace
“Summy! Kina cikin hankalin ki kuwa? Ko kin fara shaye-shaye ne?” Sumayyah ta murgude baki
gefe tace “Allah ya sauwake in yi shaye-shaye, kawai dai… ni bazan zauna a gidan ku bane, in
ba hostel za’a kaini na zauna ba, to a nema min admission a BUK”.
Cikin kokarin hadiye fushi da bacin rai da ke tunkudo masa Sarham ya ce “to na ji, matsalar
ki ce wannan yin karatu a Jeddah ko barin sa bakidaya, amma ki gayamin dalilin ki na kulla
gaba da ni, da fita sha’ani na alhalin ba haka muke nida ke ba, sai yanzu da na yi aure, bayan
kinsan mata ta bata tare ba balle ta cigaba da yimin hidimar da kike yi min”. Sumayyah ta ce “Bhaiya, kaima gashi nan aika fada da bakin ka, “KA YI AURE!” Tunda kayi
aure ni ba ruwa na da harkar ka gaskiya, kada wataran azo an araba ni dambe da matarka don
na fahimce ta mai kishi ce, sannan na san wannan matar taka mai kama da larabawan
aljannah, ba zata barni da kai ba sai ta raba mu, ga shegiyar kissa da kinibibi da rashin kawaici
a kanka, tana wani kalmashe murya kamar kyanwa, shiyasa tun yanzu na raba kaina da kai, ba
sai ta raba mu in zo ina jin zafin ta ba”.
Sarham baki bude yake kallon Sumayyah, yaki yardarwa kansa bata sha kwaya ba,
yana ji ana cewa wai kanne na kishi da matan yayyun su, bai taba yarda ba sai yau.
Sai ya kwantar da ido da murya ganin Sumayya na share hawaye kuma, tana tuno irin
tsananin shakuwar dake tsakanin ta da Bhaiya, yau ga wata ta zo ta shiga tsakani, ta fita
kusanci dashi, kuma ta san ta shigo rayuwar su kenan har abada, bazasu kara samun kusancin
da suke da shi ba ita da shi yanzu, saboda matar sa. Yanzu kam ya yarda Sumayyah bata sha komai ba, ‘inner feelings’ dinta kenan, wanda
ya sabawa hankali, shi take fada masa ba karya take ba, ba kuma hassada take yi wa Madinah
ba, a’ah tata damuwar ce ta karan-kanta, saboda yadda ta damu da zumuncin da ke tsakanin ta
shi.
Yace “Sumayah kada Allah ya baiwa kowacce irin mace da zan aura iko a kaina, ba a
kan ki ke kadai ba, har iyayena da Surayyah, kada Allah ya dora min soyayyar da zata rufe min
idanu in canza muku da wani abu saboda mace, ko in yanke zumuncin dake tsakanin mu, ko in
kasa kyautata muku da kula da rayuwar ku”. Sarham ya ja mumfashi a hankali, kafin yace “My sister Sumayyah, ki taya ni addu’a kin ji?”
Sumayyah tace “ai son da kake mata yayi yawa ne, Yaya Sarham ban so ka auri macen da
son da kake mata ya rinjayi nata ba, don tsaf! Zata raba ka da kowa naka”.
Sarham yace “Sumayyah wannan tunanin ku ne irin na mata, ki bari ki ga kamun ludayin
Madinah tukunnah, ina tabbatar miki Madinah daban take da sauran mata, don bata tashi anan
ba, kuma bata tashi cikin mata ba sai ‘yan maza, duka wadannan halayen na mugunta bata san
su ba, I assured you. Madinah mai ilmi ce kuma mai hankali, ta san abinda take yi kin ji?”
Da wadannan kalaman ya samu yayi ta lallashin Sumayyah, har ta dan saki fuska ta
daina kukan, amma tayi masa rantsuwa akan ita ba zata zauna a hannun Madinah a Jeddah
ba, a makaranta zata zauna. Sarham yace “in aka barki kika zauna a makarantar shikenan baki
da damuwa?” tace “eh, saboda matar ka ce raina baya so” ya ce cikin rashin jin dadi, “to na
yarda, ban kuma isa in sa ki so ta dole ba, amma don Allah Sumayyah kada ki kulla gaba da
Madinah akan haka, mai son naka masoyinka ne ba makiyin ka ba, ki bata dama ki ga irin
halayenta”.
Sumayyah tace cikin jin tausayinsa “toh!” ya ce “zaki gyara min dakin nawa yanzu? Yau
kwana bakwai baki share min ba, ban ci girkin ki mai dadi ba kanwata ta kaina”, tayi dan
murmushi tace “zan gyara dakin, for now, amma ka cire ni daga dafa maka abinci da gyara
maka daki kaima daga yau, ka koyi cin na matar ka”. Da wannan suka tako a tare zuwa cikin gida. Sumayyah ta je ta gyara masa dakin
sannan ta tafi hada kayan ta da zata tafi da su Jeddah, tana cikin hada kayan Mama ta kirata
tace taje ta zo da Madinah, zasu fita ssallama gidan Hajiya Kulu su kuma gaishe ta bata jin
dadi. Sumayyah ta bata rai, tace “Mama why not Surayyah ta kira miki ita? Tunda tasu ta zo
daya?” Mama ta ce “ke bana son rashin hankali kishin kannen miji, ki raba kan ki da wahalar da
bata da amfani, tunda ke dai bazai aure ki ba, ita din da baki so ita Allah ya halatta masa”.
Sumayyah tana kokarin ta hadiye bacin ranta, ta ce “Mama Allah ya sawwake in yi kishin
Yaya na, kawai ni I DON’T LIKE HER! AND I DON’T KNOW WHY?” Sai tasa kuka.
Mama ta rungume Sumayyah tana lallashin ta, a lokacin tayi ta kokarin ganar da ita hakan
bashi da amfani kuma kuskure ne, in har tana so ta zauna lafiya da dan uwanta dole taso matar
sa wadda bada jimawa ba zata zama uwar ‘ya’yan sa. Ta tilasta mata kan ta je ta kira Madinah
da kanta su tafi Gadon Kaya tare. Ko da ta shiga dakin Madinah na waya da Sarham, ana kalmasa harshe da larabci ziryan,
cikin wani ‘accent’ dinta da shi kadai take yiwa magana da shi. Kyabe baki Sumayyah tayi ta ce,
“in kin gama an ce ki zo mu tafi Gadon kaya”. Ta juya tayi ficewar ta.
Batun yau ba Madinah ta fahimci Sumayyah bata yin ta, ba kuma don tayi mata wani laifi
ba sai don a matsayin ta na masaniya akan halayen mata ‘yan uwanta psychologically ta gane
Sumayyah irin kannen mijin nan ne masu kulafucin zumunci da yayyensu. Wanda hakan ke
sawa su kasa shiri da matan su na aure don a ganinsu zasu raba su, amma ta san Surayyah
sosai take yin ta, halinta daban dana ‘yar uwarta, itace ‘yar dakin ta, tasu tafi zuwa daya, kullum
sai ta zo mata hira.
Madinah tasa a ranta daga yau zata fara kyautatawa Sumayyah. In har kyautatawa na sawa
a so mutum, to Sumayyah sai ta so ta, don an ce zuciya na son mai kyautata mata.
Sun je sun gaida Haj. Kulu Surayyah ce ta tuka su a motar Mama su uku, daga nan
suka dan zazzaga da Madinah taga gari, sune har Gidan Makama Museum da Gidan Dan
hausa, Madinah ta roki Surayyah bayan sun gama zagayen da su je ‘main house’ din su a
SoronDinki. Tun daga gate suka tabbatar sun zo babban gida, kuma tun daga karbar da akayi musu
suka yarda gidan su Madinah gidan karamci ne da karrama baki. Sannan ana ji da Madinah a
family dinta. Basu jima sosai ba tayi sallama da Kakar ta da sauran ‘yan uwan ta suka koma
gida. Washegari ya kama ranar da zasu koma Jeddah, shiri sosai Mama ta yi musu na kayan
abincin da babu a can, su maggi dunkule, ta kuma yi musu dambun nama mai yawa, gasu
alkaki, dubulan, nakiya, bakilawa da gireba na cikin garar Madinah da aka kawo, duk tasa an
shirya musu a jakunkuna daidai kilo dinsu, Sarham yayi sallama da iyayen sa da Kakar sa Haj.
Kulu. Surayyah ta dauke su a motar Mama tayi musu rakiya zuwa filin jirgin malam Aminu Kano,
suka tashi su uku wato, Sarham da Madinah, da kanwar sa Sumayyah wadda zata fara karatun
medicine karkashin kulawar Yayan ta a birnin Jeddah.
****** ***** *****
S
umayyah Allah-Allah take su sauka a Jeddah, ta kama hanyar makaranta, ta kyale Sarham da
matar sa, don ta gaji da ganin salo da rashin kawaici irin na Madinah.
Bayan saukar su a Jeddah hidimar makarantar Sumayyah ya fara yi, tun ma kafin su tare a
gidan su, Madinah ta sauka wajen iyayen ta kafin a gama shirya musu gidan su da
Saudi-German suka basu a gidajen likitocinsu, cikin kwanaki uku da saukar su har Sumayyah ta
fara karatun ta, aka bata daki a hostel din dalibai kamar yadda tafi so, shi kuma yayi
‘documentation’ na karbar aikin sa a cikin kwanakin da asibitin kwararrun ido na Saudi-German.
Dr. Sarham Abbas Shanono ya zama cikakken likitan fidar ido (ophthalmic surgeon), daya
daga cikin manyan likitocin idon da Saudi-German ke ji dasu da alfahari su.
Saida ya kammala ‘documentation’ din sa aka kuma gama shirya musu gidan nasu daga
dukiyar gidansu Madinah, daga nan gidan su ya dauketa suka wuce babban birni wato (Riyadh)
ta jirgin sama domin barje gumin amarci, abinda larabawa suke kira ‘Shahar Al-asal’ wato
(honeymoon) da harshen larabci, inda acan Sarham ya gama gane aya da tsakuwa wato AVM
Alkali bai yi masa barnar da yake tsoro ba, tuni ya ware aka barji amarci gangariya da matar da
yakewa so gangariya, wanda shi kan sa ya san son da yake wa Madinah mai yawa ne, da har
wani lokacin yake tausayin kan sa.
Daga ‘first-night’ din su, Madinah ta idasa tashin kan Sarham, domin abinda yake zato ba
haka ya sameshi ba.
AVM bai yi masa barna ba, bai kuma bar masa sudi ba, domin kuwa shi ya bare alewar sa a
leda.
Suna Riyadh ana barzar amarci a wani babban hotel na kasar, har tsayin sati guda kafin su
dawo Jeddah. Dr. Sarham Abbas, ya kama aikin sa ka’in da na’in a asibitin “SAUDI-GERMAN”.
**** ****