Showing 45001 words to 46557 words out of 46557 words
Chapter 16 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf
Sarham sun jima suna hira, yana zaune dirshan a gabanta. Inna nata kashe zuciyar
Sarham da kalamanta masu nuna hakikanin MOTHERHOOD a kan diyarta Hauwa-Kulu, yau ya
fahimci ba karamin so Inna take yi wa Hauwa ba.
Ya ci tuwon da Inna tayi kafin ya tafi wanda tuwon masara ne miyar yakuwa, ta zuba masa
soyayyen manshanu a ciki da yankan naman rago biyu. Ta kuma hada masa lamurje/zobo mai
sanyi wanda tasa a firjin Hauwa yayi sanyi.
Dr. Sarham tunda ya bar gidan su Hauwa ba tareda yau ma ya iya tsayawa a kofar dakinta
yadda ya saba ya yiwa Hauwa sallama ba, kasa shiga Sorondinki yayi yau, saboda halin da ya
samu zuciyar sa a ciki a kan maganganun da suka yi yau shi da Inna heart-to-heart, ta gama
fede masa zahirin abinda ke karkashin zuciyar ta akan miskiniyar diyar ta, HAUWA-KULU,
wanda dan cikin ta kadai zata iya gayamawa, amma shi yau ta zaunar dashi ta gaya masa duk
wani abu dake karkashin zuciyarta a kan future dinta bisa radadin da take ji na nakasar diyarta.
Kai tsaye ta bayan gidan ya wuce ya lallaba ya shige dakinsa, ba tareda kowa ya san da
dawowar sa ba.
Sarham ya kulle kansa don kada Sumayyah ta zo ta dame shi da dumi, dama kuma Inna ta
ciko masa cikinsa taf da abincin ta, don haka baya bukatar karin cin abincin Mama yau.
Ya kwanta a ranar a tsakiyar gadon sa yana tunanin maganganun Inna, ya kuma debo na
kanwarsa Sumayyah na rannan ya kara akan su, wato yayi addition, yana tarawa yana debewa,
tsakanin maganganun Inna da maganganun Sumayyah….
Sumayyah ta ce “Hauwa mutum ce kamar kowanne dan adam, tana da right din yin aure da
bukatar yin sa kamar kowa ‘in spite of her disability’, Uwarta kuma ta ce ko zata tsufa a gida
bazata bata wannna damar ba.
Ba don komai ba sai don tana guje mata wulakanci da tozarci a dalilin nakasar da shi Sarham
yayi mata lasisin ta.
Bayan kuma addini da al’ada da ‘yancin dan adamtaka duka sun bata damar yin aure. Shin
tsakanain Inna da Sumayyah, waye mai gaskiya akan future din HAUWA-KULU???
A take kaso mafi rinjaye na zuciyar Sarham ya ce “Sumayyah ce mai gaskiya!!!
Ita Inna ba wai bata so Hauwa tayi aure bane a’ah, gudun kada a wulakanta mata ita ne da
sunan aure, da guje mata tozarci da dawainiyar aure da take da tabbacin bazata iya ba sabida
rashin ido, yasa ta gwammace tayi ta ajiyar ta a daki. Wato abinda ka san bazaka samu ba
hada shi da bana so! Amma ita Hauwa din tunda har take kula Jamilu, to ya tabbata tana son
tayi auren kenan ko bata furta ba. Don Inna ta gaya masa yadda Hauwa ke sakewa da Jamilu
ita kanta abin yana bata mamaki matuka. Sai ya samu kansa da tambayar kan sa to KO DAI
HAUWA SON AUREN JAMILU TAKE YI?
Sarham sai yaji ran sa yayi wani iri mummunan baci, a take wani tunani ya bijiro masa, me
zai hana shi Sarham din ya aure Hauwa kowa ya huta (ko da baya son ta so irin na soyayyah
irin wanda yake yi wa matarsa Madinah, don shi kadai ne solution ga rayuwar ta (shi Sarham
din), da zamowa maslaha ga mahaifiyar ta, hakan zai fi alkhairi fiye da auren Jamilu ko wanin
sa ga Hauwa. Tunda maganar Hauwa ta dauwama ba aure ba dabara bace so-karbau, a
matsayin ta na ‘yar adam mai cikar lafiya da ‘sexual hormones’ kamar kowa dole tana bukatar
yin aure.
A take Sarham ya shiga gayawa kansa; zai auri HAUWA-KULU domin wasu dalilai masu tarin
yawa da ya dade yana dambarwa da zuciyar sa a kansu, amma ba don kalmar SO ta gitta ko
zata gitta nan gaba a tsakaninsu ba. SO guda daya ne a zuciyar sa; kuma na matar sa
MADINAH uwar Hauwa-Waheedah ne.
Zai auri HAUWA ne a dalilin ya san ta kullace shi, akan-karan kan sa kuma yana son kankare
wannan kullacin nasa dake kasan zuciyarta, har gobe ya kasa yafewa kansa zama sanadin
makantar ta. Babu kuma ta hanyar da zai iya kankare wannan tabon nasa daga ran Hauwa in
ba ta sanadin aure da hayayyafa ba. Zai kuma yi amfani da kwarewar sa ta yanzu, wajen ganin ganin ta ya dawo, koda ba duka
ba, da iznin Ubangiji.
A karshe ya gayawa kansa zai auri HAUWA domin yana tausayin Inna, kuma yana kaunar ta,
don haka zai karbi amanar nan data bashi ne ta hanyar AURE wanda ta hanyar sa ne kadai zai
iya cika mata burin ta, na kular mata da ilmin Hauwa da rayuwarta gabadaya, zai yi kokari
wajen cikawa Inna burikan ta a kan HAUWA-KULU ne kadai idan ya samu damar auren ta
tunda shi ba mazaunin Kano bane. Auren Hauwa gareshi ta kowanne bangare JIHADI ne
maigirma kuma solution ga rayuwa da zukatan bayin Allah masu yawa. Ba sai don SO kadai
ake aure ba.
Ya san dole ce ta sata yanke hukuncin kin yi wa Hauwa aure, amma ba don bata so ba,
tunda burin kowacce uwa shine ta kai ‘yar ta gidan miji, idan ta isa munzali.
Ta amma ta wacce hanya zai fara? Wadanne matakai zai bi wajen ganin tabbatuwar
hakan? Ya san dai wannan hukuncin da ya yanke daidai yake da a ce ya daukowa kansa Dala
babu gammo. To amma ya shirya kinkimar wannan Dalar, ya dora a kansa, koda kuwa babu
gammon babu gudu babu ja da baya, in sha Allahu ruwa ko iska babu mai hanashi aiwatar da
shawarar da ya yanke shi da zuciyarsa ta sanya HAUWA’U CIKIN IYALIN SA.
Sai dai kuma ta ina zai fara? Abin nufi ta wane bangaren???
Ta matar sa abar kaunar sa masoyiyar sa GIWAR SA MADINAH? Ko kuwa ta rigimammiyar
uwar Hauwa wato INNA SAFIYYA? Wadda ta ci layar ko dan shugaban kasa bazata bawa
auren miskiniyar ‘yar ta ba don kada a tozarta mata ita sabida nakasarta?
Ko kuwa ta bangaren mahaifin sa ABBA PROF.? Wanda tun asali alamu sun nuna ko
zancen su baya so? Koko ta bangaren MAMANSA Mai Shari’ah Haj. Maimunatu???
Kowanne daya daga cikin wandannan bangarorin ya dosa da hukuncin da ya yanke, ya san
babu sauki wai ciwon arne.
Dr. Sarham ya aje numfashi, ya muskuta ya gyara kwanciyar sa ya koma rigingine, daga
kwancen da yake yana hararo jan aikin dake gabansa. Ya san da gaske ya daukowa kansa
DUTSEN DALA da na GWAURON DUTSE kai har ma da duka KOFOFIN KANO da
BADALOLINTA bakidaya ya kinkima ya dora a kan sa. Shin ko wa zai taya Dr. Sarham saukewa kansa nauyin wannan kuduri da ya dauka? Ni dai
na san mutum mai kyakkyawar zuciya da kyakkyawar manufa a kullum mai nasara ne akan duk
abinda yasa gaba. Kuma kamar yadda Hauwa tace ne shi din mutum ne mai ‘abstract
reasoning’ komai cudewar lamari baya kasa warware abinsa. Don haka ina yiwa Dr. sarham
fatan nasara da fatan alkhairi da taya shi fafutukar kaiwa ga cikar kudirinsa na alkhairi.
MURFIN LITTAFI NA BIYU
Mu biyo “HAUWA KULU-AKA- (‘YAR CIKIN BADALA)” a littafi na uku, Ubangiji dai yayi
alkawarin cewa “cikin dukkan tsanani akwai sauki”. Sannan a cikin biyayyar iyaye akwai babbar
NASARA. Hauwa kuma tuntuni tayi aniyar yiwa Inna biyayya ta danne kwadayinta na dukkan
dan adam, wato ta hakura da rayuwar ‘marital life’ da ‘motherhood’ daga yau har karshen
rayuwarta domin yin biyayya ga Inna.
Shin kwadayin Hauwa na can karkashin zuciya zai tabbata? (Hauwa za ta samu damar yin
marital life da motherhood kamar kowacce diya macen data kai munzali duk da lalurar
makantarta? Ko kuwa zata dauwama ne a gaban Innarta tana kaf-kaf da abarta yadda Innar ta
zabar mata tayi rayuwa??? Shin HAUWA-KULU zata yi rayuwar aure da tara iyali a yadda Ubangiji ke son ganin ta ko
kuwa zata dauwama bisa tsarin Innarta?
Ina labarin Malam Bilyaminu har yanzu ne? A mace yake ko a raye?
Amsoshin duka wadannan tambayoyin in sha Allahu suna cikin littafin HAUWA-KULU
kashi na uku.
Taku har abada;
Sumayyah Abdulkadir (Takori).
2/09/2023
07030137870
(WHTSAPP ONLY)