Showing 15001 words to 18000 words out of 46557 words

Chapter 6 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf

su yi
murnar ganin ka bagatatan yau ba?”.
Sarham ya mike ya isa gareta ya kama hannayen Mama ya rike cikin tafukan sa, yana
murmushin farin ciki ya kai su ga fuskar sa kan sajen sa, wanda a baya kafin ya tafi bashi da shi
yace “My Mommah, I missed you badly kin sani. Amma autar ki bata san ta girma ba, kullum
tana nan jiya I yau shiyasa bazan daina fada ba”. Kafin kace meye wannan gida ya kacame da murnar dawowar Dr. Sarham. Da Abba Prof. ya
dawo murnar tafi armashi, a ranar har dare suka raba a falo suna hirar yaushe gamo, amma an
nemi Surayyah an rasa a falon, tunda ta zo ta yi masa sannu da zuwa ta gudu gidan Kakar su
Haj. Kulu a gadon kaya, don tayi-tayi Sumayyah ta karbi ‘yan kudin da ke hannun ta ta kai Kofar
Na’isa, ta roke ta kan ta rufa mata asiri tayi maza ta kai musu tun kafin Yaya Doctor ya huta ya
waiwayi zancen, wadanda ko kwatan abinda ta kashe daga abinda yake aikowa din basu kai
ba.
Sumayyah ta ki amsa, ta kuma ce in ta takura mata ta cigaba da saka sunanta cikin laifi nan
wallahi zata tona ta, “kawai ki yi harkar ki Yaya Surayyah ki rabu da ni, ni ba maciyiya amana
bace kuma ba’a shirya rashin gaskiya da ni”.

Duk da ta san Sumayyah ta gaya mata bakar magana sosai amma ta kasa cewa komai
wannan karon, girma da mutunci ai madara ne, kuma mutum shi yake rike kayan sa, ta yarda
ita ta zubar da girman ta har Sumayyah kanwar bayan ta yau ta nemi zagin ta (in disguise). Don
haka Surayyah ta ga gara ta gudu gidan Hajiya, inda ba abinda Sarham ya isa yayi mata in dai
a gaban Hajiya ne koda ta bare da ita.
Washegari walima sosai Mama ta hada musu a babban falon ta, ta murnar dawowar Sarham
da kammala zurfafa karatunsa, wato kwas din da ya je yi na tsayin shekaru uku a (KAU,
Jeddah) ta kasar Saudi Arabia, don haka aka tura direban zuwa Abba Gadon kaya don ya
dauko Hajiyar Gadonkaya. Jin maganar zuwan direba daukan su daga bakin Maigadi yasa Surayyah duk ta damu,
lokacin da da aka ce su fito a tafi gidan Abba, Hajiya tace ta shirya su tafi gidan nasu tare, ta
yaya ana can ana murnar zuwan dan uwanta da taya shi murnar zama babban likita zata taho
ta zauna ita kadai anan kamar mujiya a cikin ‘yan uwanta? Tace lallai ta shirya su wuce, bazata bar ta ita kadai a gidanta ba.
Da Surayyah ta ga ba sarki sai Allah sai ta fadawa Haj. Gaskiya cikin damuwa, cewa laifi tayi
masa fa, bata so ya kure ta, don zai iya dukan ta, Hajiya kuwa ta saka ta a gaba tace sai sun
tafi taren, mai dukan mata ita sai ruwan sama.
Mama da hannun ta tayi girke-girken walimar nan, don haka sun kwashi gara mai dadi sosai.
Sarham yayi wa girkin Maman sa cin yaushe rabo! Da sweet cook din Mama!? Ba abinda bai ci
ya hantse a wajen ba. Da yake magananne ne har gobe tunda ya fara cin abincin nan bai yi
shiru ba, yana yi ne yana zuba santi, saida Hajiya Kulu ta saka masa filon kujera a kuturin sa,
tace, “gara a saka maka waigi haka likita Sarhamu, Allah yasa dai matar duk da zaka aura mai
iya girki ce.
Shin ma ina aka kwana kan maganar aure? Wannan karon kam zan bada cigiyar mata har a
masallatai idan bakin jini ne ya hana ka samun mata”. Daga Abba har Mama duk suka bi shi da
ido kamar Hajiya ta ci musu albasa ne ta fadi abinda ke ci musu rai, suka dakata da cin abincin
suma suna jiran amsar sa da zai fada, da alama dukkannin su suna da wannnan damuwar
tuntuni kawai Hajiya ta riga su furtawa ne.
Ai yau Sarham da karfin guiwar sa ya ce “ki kwantar da hankalin ki Hajiya, ba sai kin kai
tallata a masallaci ba, an riga an bani mata cikin daraja da kima kuma wadda nake so tuntuni,
ku ake jira ku je tambaya da sanya lokaci”.
Mama da Abba har suna hada baki wajen tambayar sa.
“Daga ina ka samo matar kuma ‘yar waye a Kano a ina suke? Tun yaushe kuke tare bamu
da labari?”
Yace “Mama zaki iya tuna yarinyar dana ke tare da ita tun zuwana karatu MBBS na farko?
Ina nufin MADINAH. Ke ai kin jima da sanin labarin ta, wadda a baya mahaifin ta yace bazai
bani ba, to ita din ce dai muka sake haduwa a wannan karon muka sulhunta, mahaifin ta kuma
ya bani auren ta already ku kadai yake jira, ‘yar gidan Attahiru Habibu SoronDinki ce”. Mama da yake ta san zancen Madinah tuntuni nan da nan ta ci magani, fuska a gintse tace
“shima ai ya sani” (tana nufin Abba Prof.) ta kara da cewa “ko ba yarinyar da ka kusa kashe
kanka a kanta ba, saboda uban ta ya wulakanta ka? Yarinyar da ka zauna shekara bakwai cikin
tuzuranci babu aure saboda an hana ka ita, sakamakon cewa sun raina arzikin mu da
mutuncinmu? Itace ko ba ita bace?”

Sarham yayi shiru, gaban sa da zuciyar sa na wani irin faduwa, tsoron sa Allah tsoron sa
kada Mama tayi (opposing) maganar Madinah, shi kam da ya shiga uku, don in har ba Madinah
ya aura ba, babu shi babu aure a duniya (ya fada a zuciyarsa).
Abba ya ce “Lelen Abba rabu da Mama, yi min cikakken banyani, diyar Attahiru Sorondinki
wanda na sani ce da gaske? Ina nufin na ISDB? In haka ne kenan jikar Alkalin Alkalai Habibu
SoronDinki kake nema kenan fa?”
Sarham ya dan samu kwarin guiwa da hope, domin a muryar Abba kawai ya ji ‘excitement’ na
sanin iyayen Madinah da yayi, kamar zai yi na’am da maganar shi kam. Yace,
“sune Abba, his last daughter Dr, Madinah Attahiru”. Da rashin karsashi a muryar sa ya
baiwa Abba tarihin su Madinah da iyayaenta kamar yadda ya ji daga bakinta, da kuma na
rayuwar su a Jeddah itada mahaifanta da ‘yan uwanta maza, inda a can aka haife su itada
wasu daga cikin yayyen nata, da yadda mahaifin ta ya raba su a baya, yanzu kuma su da kan
su suka neme shi ba shi ya nemi Madinah ba ta dawo masa ba, har pretending din da yayi tayi
mata don kada ya koma mata ya gaya musu, da kiran sa gidan su da Daddyn nata yayi, domin
ya bashi hakuri da uzurin sa na hana shi auren Madinah.
Amma abin mamaki duk da wannan labarin da Sarham ya bayar Mama taki saukowa ta
amshi zancen Madinah da hannu bibbiyu, musamman da taji wai har aure an daurawa Madinah
bata tare ba mijin ya rasu, sai ta kara ninka ‘opposition’ din ta da zancen, inda tace cikin
mamaki, “Sarham! Kai kuma inda Allah yayi da kai kenan saboda soyayyah? Bazawara/widow zaka
dauka kana saurayi wanda bai taba aure ba? Bazawara fa kaikuma saurayi? Ni ban yarda wai
bata je gidan mijin ba, sun dai rufa ka ne don su sayo mata matsayin budurwa, shiyasa ko lefe
aka ce ka bari, kai kuwa saboda Allah me Madinar nan ke da shi da sauran mata da kake gudu
suna rububin ka basu dashi?”
Abba yace “Maimuna har gobe baki san SO ba na ga alama, kyale rai da abunda ya afu ga
so, aure kuma ai ba kaskanci bane daraja ne, haka mutuwar miji baya nufin darajarta ta ragu, ni
ban ga laifi anan ba don yarinya ta taba aure, shin Manzon mu ba da bazawarar ya fara ba?
Yarinyar nan ‘yar manyan mutane ce kuma ‘yar babban mutum, sama da abunda yafi haka
zasu iya cewa kafin su bada auren ‘yar su, aka ce tuwon girma… miyar sa nama Maimuna, ko
yanzun ba don ta rasa miji bane yasa suka bashi, a’ah, ya ci darajar soyayyah ne kawai Allah
kuma ya tsaga cewa ita din rabon sa ce”. Mama tayi shiru amma ta ki gamsuwa, ta ce “ni kawai ko ‘yar shugaban kasa ce bai dame ni
ba, tunda suka raina arzikin mu tun farko nima na raina mutuncin su, saboda basu yi amfani da
ilmin su ba anan don wallahi ba yabon kai ba, Sarham dina ya wuce raini, tunda Allah ya bashi
addini, nasaba, ilmi da basira to ya gama bashi duk wani arziki na duniya koda kuwa a kan jaki
yake yawo”.
Duk aka yi wa Mama dariya Abba yace “Maimunatu Dan farin? Kike wannan zakewar a kan
sa babu fulatanci? Ina fulatancinki ya tafi ne?” Ta yi fuska sosai ta ci laya tace “ko rabin farko ne
shi ba Dan fari ba, ina son abuna yadda suke so ‘yar su koma fiye, sun dauko sudin kwano sun
bashi, ina dalili da gatan sa shima da komai?” Abba yana danne dariyarsa yace. “Barr. Maimunatu to yaya zaki yi? Tunda shi ya ji ya gani yana son leftover din nasa a haka?”
Sarham dai bai ce komai ba kansa na kasa, kamar yace da kasar ta tsage ya shige, amma
ya ji ciwon kalmar nan ta an bar masa sudin kwano, ta kara rura wutar kishin sa akan auren

Madina da AVM Alkali. Duk ya daina dokin auren ma, Madinar ta kara bashi haushi, amma baya
jin ruwa da iska zai fasa karbar auren Madinah ko da ta haihu goma da AVM wanda ke nufin so
na hakika yake yiwa Madinah.
Abba da Hajiya Kulu, suka yanke shawarar wadanda za’a tura Sorondinki daga waliyyan
Sarham don gabatar da zancen aure don itama Haj. Kulu tayi na’am da zancen dari bisa dari
don kuwa ta san Kakan Madinah farin sani marigayi Alkalin Alkalai wanda tace zuri’arsa ne kaf
suka samar da Sorondinki. A daren Abba Prof. kwana yayi yana lallashin Mama cikin dabara da soyayya irin ta manya
akan maganar auren Sarham, yace mata abu daya zata duba kawai; son da Sarham yake wa
Madinah, in ta duba wannan to sai ta sakawa ranta salama.
Domin shi ya lura son da Sarham yakewa Madinah mai yawa ne, tunda har ya iya kwashe
shekarun nan babu aure saboda rashin ta, kuma jin ta auri wani kafun shi, bai say a ce ya fasa
ba.
Ita kuma Mama irin iyayen nan ne masu kishin ‘yayan su, wannan son da ake fadi yana wa
Madina shi yafi komai bata mata rai, don a tsarin ta sam bata son Sarham ya auri macen da son
da yake mata ya zarta wanda take masa, ko wadda zata zo ta canza masa behaviours da
alaqarsa dasu. A ganin ta son da yakewa Madinah yayi yawa har ya zarta nata son, ba don
haka ba ai da bata yarda ta auri wani kafin shi ba, tana tsoron kada Madinah tayi amfani da
hakan ta bautar mata da shi, ko ta wahalar mata da shi tunda ta zame masa rayuwa
dungurungum. Duk da ta san Sarham jarumi ne akan komai nasa ko a cikin maza, kuma
tsayayyen namiji ne tun yana yaro akan ra’ayinsa, amma tana tsoron wannnan matsiyacin son
da yake yi wa Madinah Attahiru.
​ Haka Abba Prof. ya samu ya lallaba ‘yan kayan sa, don shikadai yasan abinda yake
zuciyar Mama, ya nuna mata in bata cire kishin matar Sarham daga ranta ba zata zubar da
girmanta, kuma zata sha wahala don matsayin kowaccen su daban a wajensa, ya roketa kada
ta zama fitinannun iyayen mijin zamani masu tsanar surukansu babu gaira babu dalili kawai don
yaransu na son su, tunda itama ba haka Hajiyar Gadonkaya tayi treating dinta ba duk da ta san
son da Abban yayi matukar yi mata, da haka ya samu ya lallabata har dai ya samu lagonta ta
amince aje akai kudin auren, ta kuma sakawa al’amarin albarka.
​ Washegari waliyyan Sarham suka tafi SoronDinki. Suka dawo da albishir mai dadi na
cewa Baffanta yace Juma’ar nan za’a je a daura auren a babban masallacin juma’ah na Kano,
su sun shirya tuntuni, su suke jira dama. Suka kuma fadi irin karbar mutunci da saukar girma da
aka yi musu, wannan ya kara sauko da zuciyar Mama. ​ Iyayen Sarham sun gabatar da komai na auren har sadaki ga kanin Baban Madinah tun
kafin juma’ar ta zo, kuma Baban Madina yana ta kara jaddadawa kanin shi ta waya ya gaya
musu shi baya karbar lefe, sadaki da kudin aure kawai yake amsa. Wannan ma ya kara
sanyayawa Mama. Juma’ah na zagayowa aka daura auren. ​ **** **** ****
Tun dawowar sa Najeriya Sarham bai samu nutsuwa ba ko ta kwabo, sai yau da aka daura
auren sa da Dr. Madinah Attahiru bayan saukowa daga juma’ah, mahaifin ta da duka ‘yan
uwanta maza hudu sun samu sun halarci dauren auren, Madinah ‘yar dangi ce gaba da baya
kasancewar auren zumunci ne a tsakanin iyayen ta, sun kuwa nunawa Hajjah Ramlah
zumuncin da karah, don kwansu da kwarkwatarsu zuri’ar Sorondinki sun yi dafifi a ‘main house’

din su, don halartar yinin bikin Madina a ranar da aka daura aure.
Iyayen Madinah su ya kamata a kira masu Kano, ba kuma wai sarauta ce dasu ba domin
iyayen ta da dangin ta na uwa dana uba wadanda duk abu guda suke, sun kame duk wasu
madafun iko na Kano.
​ Sai bayan daurin aure ne, da ya samu ya huta ya samu nutsuwa bayan mutane sun
watse, a daren daurin auren ya samu ya zauna da Sumayyah yana tambayar ta yaya labarin su
Hauwa da Inna?
In ce ko tana zuwa tana gano masa su da baya nan kamar yadda ya bar mata sallahu? Kuma
in ce ko duk wata tana kai musu sakon da yake aikowa ta hannun Surayyah?”
Ya tsare ta da kaifafan idanun shi ganin yanda tun bai gama magana ba Sumayya ta shiga
cikin rudani da damuwa, na farko dai itama ta mance da su Hauwa, bata kara tunanin zuwa
kofar Na’isa ba tun bayan tafiyar sa, na biyu ga abunda Surayyah tayi, wanda ke nufin dukkan
su sun zama masu laifi ga Bhaiya, sai dai a ce laifin Surry ya take nata wato, sawun giwa ne ya
take na rakumi.
To amma ta kwana da sanin halin Bhaiya baya son yayi maka tambaya wadda a wurinsa mai
muhimmanci ce ka zuba masa na mujiya nan da nan zai harzuka, sai duk ta daburce, ta hau
inda-inda da in-ina, tana son cewa ba ita bace Surayyah ce, tana kuma son kare Surayyar.
Kawai sai jikin sa ya bashi babu gaskiya acikin al’amarin ta, ko wani abu mummuna ya faru
dasu Inna a bayan tafiyar sa, gabansa yayi mummunan faduwa ya fiddo wayar sa ta tafi da
gidan ka daga aljihun gaban farar shaddar shi Wagambari wadda ta sha maikon sabunta, Ango
sosai, sai walainiya yake yi a cikin farar Excelcior din, yasa dan yatsan sa daya yana dannawa
Surayyah kira, tana amsawa yace ta same shi a karamin falon Mama.
Tun daga jin kiran sa itama Surayyah ta hau numfarfashi ta san ta gama barewa, a lokacin
suna tare da wanda zata aura a harabar gidan su wato Engnr. Aliyu Barde, wanda dan abokin
Baban su ne, iyayen su suka hada su, Aliyu ya fahimci hankalin ta ya rabu gida biyu tun bayan
amsa wayar ta, yace “me ya faru ne a wayar?” Surayyah ta dauki excuse daga wajen Aliyu kan
Yaya Doctor dinsu yana kiran ta a cikin gida, ko zai bata minti goma?
Egnr. Yace ai tafiya ma zai yi don akwai inda zashi, don haka suyi sallama kawai, sai wajen
jibi zai dawo. Don lokacin an saka musu lokacin aure.
Bayan sun yi sallama ya tafi, Surayyah ta taka zuwa cikin gida tana tafe salalau-salalau
kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
​ Sarham har ya gaji da jiran shigowar ta ya mike zai biyo bayan ta yana huci sai gata
tana shigowa. Tun kafin ta zauna ya jefo mata tata tambayar kamar yadda yayiwa Sumayyah
game da sakon su Inna da yake turowa ta account din ta duk wata, yau shekara uku bai taba
fashin turowa ba, wanda yace a dinga kaiwa mutanensa na kofar Na’isa. Surayyah tayi zuru-zuru ta yi wiki-wiki da ido tayi masa shiru, kiris ya rage ya mare ta, don
baya son halin ko’in kula in yana maka maganar da a wurin sa mai muhimmanci ce, kayi shiru
ka zuba masa ido kamar tsohon maye kana kallon sa.
Da kyar Surayyah ta motsa baki ta ce cikin rawar murya “I’m sorry Yaya Doctor!” Ta kara
cewa “I’m so sorry” “Sorry for what?!” Ya tambaya (in exclamation).

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login