Showing 42001 words to 45000 words out of 46557 words
Chapter 15 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf
yake shi din shine Sarhamu, sai ya bagarar, yashare, ya
hadiyefirgicewarsa yayi kamar bai ji kalaman Jamilu ba, yayi musu sallama da dusassar
muryarsa ya kuma baiwa Jamilu hannu suka yi musabiha, ya dan kalli Hauwa yana mamaki
yana karawa, sannan ya shige cikin gidan.
Inna ta rako Babar Jamilu zata tafi suka yi kacibusa da shi yana shigowa tsakar gidan, kafin
Jamilu ya samu zarafin tambayar Hauwa ko wanene shi ya isa dakin Inna, shigowarsa tasa
hankalin Inna ya koma kansa, a gurguje suka yi sallama da Haj. Rumanatu ta wuce, bayan ta
tabbatar mata cewa kwarai ta fahimce ta, zata yi iya yinta wajen lallashin Jamilu ya hakura, ko
don kwanciyar hankalin Inna da zaman lafiyar su da Babansa dan jidali (Zakari).
Sarham ya zauna a falon Inna yana jiran ta har ta shigo ta zauna akujerar dake fuskantar sa,
suka gaisa, sai ya koma cikin kujera ya kishingida yayi shiru, har da dan juyawa ya kalli taga
yaga ko Hauwa taji kunyar idonsa na abinda ya tarar tana yi (soyayya) tayi maza ta baro
saurayin ta shigo gida ko a’ah? Amma ina! Ko keyarta bai gani ba, tana can suna sallama da
Jamilu kamar bazasu rabu ba, Sarham ya mike dogayen kafafunsa a kasa. Bai iya kara cewa
komai ba don al’ajabi da mamakin Hauwa.
Can jimawa sai ga Hauwa ta shigo, tana tafe abunta kanta tsaye, babu ko lalube irin na
makafi, tsabar ta gane hanyar dakinta, tasa kai zata wuce dakinta taci uban tuntube da kafafun
Sarham, saura kadan ta kifa ta ci da baka. Ko sannu bai mata ba balle yayi ‘apologizing’. Cikin
fushi tace.
“Inna wa ya saka min kafa zai kayar da ni haka?” Inna ta yi mata shiru, kafin tace “daga ina
kike?” tace “Yaya Jamilu ne ya kira ni soro”.
Haba! Sai Inna ta balle da fada kamar ta rufe ta da duka, cewa take “da iznina kika fita zance
gun Jamilu? Kece da zuwa zance Hauwa da wane idon zaki ga saurayin?” Saida Dr. Sarham
yace “ya isa Inna, kinsan kinada matsalar zuciya, kada ki dinga bata ranki irin haka kan
kananan abubuwa har ya tabo zuciyar ki”. Hauwa ta wuce dakin ta a sanyaye, bayan ta gaishe
shi. Dr. Sarham yaki ko amsawa balle ya nuna ya san tana gaishe shi, har ta wuce tana
mamakin me ta yi wa Dr. Sarham yau?
Gashi dai yau bai kira sunanta da yake mararin kira na MAIJIDDAH cikin farin-ciki, yalwar
fuska da far’ar nan tasa ba, bai kuma amsa gaisuwar ta da kulawa da (attention) kamar yadda
ya saba ba. to me ta yiwa Likitan Inna?
Ji yayi gabadaya yau ya kasa zama ya dade a gidan yadda ya saba, ya kuma kasa hira da
Inna yadda suka saba, ita kadai take ta babatunta, daga karshe da Inna taga shirunsa yayi
yawa sai ta dago ta dubeshi tace,
“ko lafiya kake kuwa likita? Na ganka ba’a yadda na saba ganinka ba”.
Sai kawai ya mike yana cewa “bari in karasa gida Inna, kaina ke min ciwo, yanata sarawa,
idan na ji sauki zuwa gobe ko jibi in sha Allah zan shigo”.
Inna tace “ni ai ban sani ba, gashi har nayi maka tuwon Acca kuwa, da miyar da kake so ta
zogale” Sarham ya juya a lokacin yana saka takalman sa a bakin kofar falon, yace “ba komai
Inna, some other time, zan ci”.
Suka yi sallama dukkansu jiki babu kwari ya juya ya tafi. Ko sallama bai yiwa Hauwa ba.
Yana tuki yana hada gumi kashirban, duk da sanyin AC din motar sa. Abun ya daure masa
kai matuka. Ya kuma sakashi a damuwar da ya kasa sanin ma’anarta. Yana isa gida yaji ana
murnar zuwan Sumayyah, wadda ta zo hutun karshen shekara da barkar haihuwar Waheedah.
Kamar bai ga Sumayyah ba, bayan kuma har ido sun hada a falon, ya dauke kai yasa kai ya
wuce zuwa dakin sa bayan yace musu cikin jam’u “sannun ku da gida”.
Mama ta bi shi da kallo, Sumayyah kuma ta ce. “Bhaiya lafiya kalau yake? Kaamr bai ganni
ba Mama?” Mama ta ce “oho muku, kun fi kusa”. Surayyah ta ce “nafi tunanin wani ne ya bato
masa rai daga waje, baki ga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ba?” Sumayyah
sai ta mike ta bi bayan sa zuwa dakin nasa. Sallama tayi daga bakin kofa, sai da ya bata iznin shiga ta shiga dakin ta same shi zaune
akan ‘study chair’ ya rafka uban tagumi, ta ce.
“Bhaiya baka ganni bane ka wuce bamu ko gaisa ba?”
Ya dago ya dubeta da jan ido, a lokacin taga idanuwansa sun kada, yace “a’ah Summy ce
yau a gari? Saukar yaushe?” Tace tun dazu na sauka, ta gabana fa ka wuce, har ido mun hada,
ka san mun yi hutu shine fa nace bari kawai in taho ganin Hauwa’u”.
Ta zauna a kujerar ‘sofa’ kwaya daya dake dakin, ta ce “Bhaiya duk ka birkice, you are upset,
anya lafiya kake kuwa? Na ganka ‘moody’ tunda ka shigo”. Yace “Sumayyah, bansan yadda
zaki fassara abinda ya sani a damuwar ba idan na fada miki, ba wani abu bane serious I don’t
know why I made it serious, abun ne ya bani mamaki, ya kuma bata min rai, wai Hauwar nan da
kika sani ko ido bata da shi, amma ta iya tsayawa zance da saurayi a soro???
Ni ban taba ganin abinda ya bani mamaki ya rikitani irin wannan ganin dana yi ba”.
Sumayyah tana sane tace “Hauwa wacce? Baby Hauwan mu?” Ya harareta, “ke bana son
sakarcin banza. Hauwa ‘yar Inna mana, kanwata ta kofar Na’isa” Sumayyah ta wani ce “au ho!
Ka ce min kawai Hauwar Inna, HAUWA-KULU ‘yar cikin BADALA!”. Sai ta hau tuntsira dariya
tace “Bhaiya, yanzu ganin Hauwa da saurayi shine abinda ya birkita ka haka?” Sarham ya harareta yace “Sumayyah yaya ina miki magana ‘serious’ za kina dariyar rainin
wayo, Hauwa fa, wadda ko ido bata da shi, ina zata kai wani namiji da sunan soyayya?
Ganin ta nayi da wani cousin dinta suna zance fa, zance na saurayi da budurwa! Wai sunan
sa Jamilu, dan kanin Babanta ne”.
Ai kuwa Sumayyah ta kara tuntsirewa da dariya sai da tayi mai isarta, shi kuma ya shaka
sosai, saida dariyar ta lafa mata ta ce.
“Bhaiya makaho ba mutum bane? Ko kuwa makaho bai san SO da mai son sa ba?
Don tana makauniya shikenan sai akace bazata yi aure ko soyayya ta ji dadin rayuwar ta
kamar kowanne dan adam ba? Ko in bata saurari masu son ta ba kai din auren ta zaka yi?
Yau nake ganin ikon Allah, yau ina ganin abinda ya gagari Kakata Kulu, kai ka dafe dahir har
da ‘yar ka tubarkallah, shine ita zaka yi mata fatan ta tsufa a dakin uwar ta, alhalin kai ba son ta
kake yi ba, wannan fa shi ake kira karfin hali barawo da sallama ko in ce, Bhaiya na, da tsabar
son kai tsagwaro. Wani hali da ban san shi da shi ba. Ni wallahi gani nake ma babu wanda ya dace da ya aureta kamar dan uwan nata, tunda jinin
su daya, ya san darajar ta, zai yi hakuri da nakasar ta, ya riketa da daraja a gidan aure, don kai
kam Bhaiya, baka da alqiblah.
Ayi magana cibi ya zama kari!”.
Ta sake tuntsirewa da dariya ta ce “sai amara kirazan biki, mu ne manyan kawayen amarya
Hauwa’u, a bikin ta da Yayanmu Jamilu”. Sumayyah har da dan gudu-gudunta ta bar dakin,
tana cigaba da tillika dariyar shegantaka. Don ta san ta gama kunna shi in ta kara minti uku a
gabansa zai iya losing control kai mata duka. Don tana ganin yadda yake girma idanunsa tunda
ta soma shegantakarta.
Maganganun ta dinnan, suka taru suka zamewa Dr. Sarham “a warm food for thought!” A
tsayin wannan daren bakidayansa kona rabin away a kasa runtsawa.
Sarham sai faman juyi yake a kan gadonsa, daga wannan gefen zuwa wancan, yana tauna
maganganun Sumayyah a kwakwalwarsa, yana kuma fassarasu a zuciyarsa cikinma’auni na
hankali da tunaninsa. Daren da yazo masa da tarin ‘alterations’ koko ‘revolutions’ wadanda a
can baya bai taba hango yiwuwar makamantansu ba. Ko na minti daya ya kasa rintsawa. Idan ya tuna maganganun Sumayyah. A ganin sa
Sumayyah maganganu ta gasa masa masu zafi ta cikin ruwan sanyi, koko yace jirwaye tayi
masa mai kama da wanka, don dama tana kullace da shi akan abinda yayi mata, don kawai ta
tambaye shi ko son Hauwa yake yi shekarun baya, bazata manta ba yayi mata wulakancin da
bata zata ba, kiris ya rage ya doketa. A nata bangaren Sumayyah, ta dade tana kiwon
mu’amalar sa da su Hauwa ta rasa alkiblarsa, musamman in ta tuna abinda yayi mata daga ta
tambaye shi ko son Hauwa yake? Ta tuna a ranar dukanta ne kawai bai yi ba, shine abinda take
nufi da “ayi magana cibi ya zama kari”.
Da gasken gaske ya kasa barci a daren, sai faman tauna maganganun Sumayyah wadanda
ya kira jirwaye mai kama da wanka.
Washegari ya samu kansa da kasa zuwa gidan Inna, saboda har zuwa lokacin ransa a bace
yake, haka a sauran kwanaki ukun da suka biyo baya ko hanyar kofar Na’isa bai kalla ba, yana
like wajen su Waheedah, kamar ya maidasu ciki, don a can yake samun sanyin ran sa, daga
zafafan maganganun Sumayyah da haushin Hauwa (a ganin sa bakaken maganganu ne
Summy ta gasa masa son ran ta), da suka dade suna dafa shi kamar dafaffiyar masara, kuma
ya kasa cewa Sumayyah komai a kai again bayan kuma ita kadai ce zai iya zancennan da ita.
Madinah ta samu lokacin sa sosai a wannan satin, don yanzu kullum yana wuni tare da su baya
zirga-zirgar gidansu Inna.
Inna na talgen tuwo a yammacin yau da Sarham ya kwashe kwanaki bakwai bai zo gidan su
ba, sai ya fado mata a rai, ta dubi Hauwa dake wankin sittirun ta a bakin famfo tace.
“Kuluwa!”
Hauwa ta tsuke baki ta kuma tsuke fuska bata amsa ba, ai ta san in ta ce mata Kuluwa
bazata amsa ba, sai ta ce “ni kuwa kin lura da abinda na lura da shi?” Hauwa tace “me?” “Likita
Sarhamu, yau kwana bakwai bai zo gidannan ba, tun ranar da ya zo yace min kansa na ciwo,
yanzu haka jikin ne ya matsa masa tunda har kika ga yayi wannan dadewar bai zo ba”. Hauwa ta yi shiru bata ce komai ba, ta cigaba da wankin ta, ashe ba ita kadai ta lura da
rashin zuwan nasa ba. Inna ta sake cewa.
“kin ga da ace na san gidan su sai in je in duba shi”.
A nan ne Hauwa ta bata amsa,
“kai su Inna akwai wuce gona da iri”.
“Ba wuce gona da iri bane Hauwa-Kulu, baki ji fadar bahaushe ba? Yace KA GAIDA MAI
GAISHEKA KO DA BAZAI AMSA BA!”
Wannnan magana ta karshe da Inna ta yi, ta yi ta ne a kunnen dan halak din wato (Sarham),
don a lokacin ya iso tsakar gidan da kasaitattar sallama a bakin sa.
Nan da nan Inna ta bar abinda take yi a madafin ta fito, ta washe baki tana amsawa,
“maraba da Da na Sarhamu, likita Sarhamu na ne tafe? Dan halak yanzu nake zancen ka, sai
gaka”.
Sarham ya tsugunna a kofar kitchen din yana gaida Inna, Inna ta koma ta kashe wutar tuwon,
ta taso suka shiga falon ta tare, suka kara gaisawa, Inna sai taga duk ya rame mata, tace “Likita
jikin ne ya boye ka ne?” Ya ce “a’ah Inna lafiya ta kalau, kwana biyunnan dai ban cika fitowa ba,
ina can wajen su Hauwa’u karama kullum”. Hauwa ta shigo da sallama tana dan dafa bango, ta isa kofar dakin ta sannan ta juyo saitin
da ta ke jin tashin tattausar muryar Sarham, ta ce cikin girmamawa “Dr. barka da zuwa, ina
wuni?”
Ya dago kai ya kalle ta kadan, kayan jikin ta sun dan jike sun manne a fatar jikin ta, Hauwa
yar shekara sha takwas ta gama samun duk wani dirin jikin da jikinta zai bayar, da kyakkyawar
suffa na abinda ake nema a tare da budurwa ‘teenager’, nata har ya zarta yawan shekarun ta,
don tsammani zakayi ta kai shekaru ashirin da daya. Tun asalinta Hauwa bata da rama haka take ‘yar duma-duma, lubu-lubu (luscious). Dr.
Sarham ya yi wata ‘yar ajiyar zuciya ba tareda ya san ya yi ba, yana tuno kwailancin ta na
shekaru biyar a baya, wai itace haka yau a gabansa, yace a hankali “lafiya kalau, ina Saurayin
ki dan polo dan gayu?” ‘yar dariya Hauwa ta yi, ta shige dakin ta bata ce masa komai ba.
Sai Inna ce tayi kwafa ta ce, “ai ka bar ni da Hauwa da Jamilu kawai, nice maganin su da
rashin kangadonsu, da ni suke zancen wallahi, na sa uwarsa Rumanatu tayi musu iyaka, idan
yaji toh, in bai ji ba na rantse zan iya kai shi kotu don alkali yayi musu iyaka.
Na fada na kara ni fa bazan taba yi wa Hauwa wani aure ba, balle in bawa dan Zakari.
Allah na tuba ko dan shugaban kasa ne ya zo neman auren Hauwa, wallahi bazani bayar ba,
balle dan Zakari tsatson zalunci.
A cikin burika na masu kyau a kan Hauwa, babu batun yi mata aure a ciki, babban burina
shine ta yi karatunnan na zamani mai zurfi in dai makafi na iyawa kamar yadda ta fara, ta samu
abunda ko bayan raina zata dogara da kan ta, kuma in karfina ya kare kada nata raunin ya
bayyana dalilin rashin karfi na, ko in ta Allah ta kasance min hakan ya kassarata. Ni din nan nice karfin Hauwa, ni ce kuma idanun ta, bazan taba bari a wulakanta min ita da
sunan aure ba, ko a ci mutuncin lalurar ta a dalilin aure, shi yasa na gwammace in adanata a
gabana, in kula da ita, tayi ta karatu, duk da ni ma ba karatun nayi ba, amma alhamdulillahi ni
lafiya ta kalau, zan rayu ko ba ilmin zamani ba tare da na zamewa kowa labiliti ba. Amma Hauwa fa? Ai duk wanda na bawa auren ta na kware shi, domin na hada shi da aiki da
jidali. Itama kuma na sayo mata rashin kwanciyar hankali. Don haka maganin kada a ji, kada a
soma.
Gashi bani da matallafi namiji wanda zai tsayawa Hauwa ta samu ta yi karatun nan tunda ni
bansan kansa ba, da wannan yau nake baka amanar Hauwa-Kulu Sarhamu, ina mai baka
amanar ta don na amince maka, na kuma amince bat un yau kaunar ka damu ta saboda Allah
ce. Don Allah likita ka taimaka min, wajen cikar burika na a kanta, na tayi karatu mai zurfi wanda
zai amfani al’umma ya kuma amfane ta duk da nakasar ta. Bana so nakasar nan tata ta zame
mata rauni, so nake nakasarta ta zama ado a gareta.
Inna ta soma sharar hawaye ta ce “gashi Bilyaminu ban san inda yake ba, bansan a halin da
yake ciki ba, yana mace ne ko yana raye Allah masani, na tabbata da ace yana tare da mu,
shima burin sa zai zama irin nawa ne akan Hauwa, don a komai muna kasancewa da ra’ayi
daya ni da shi. Allah ya gani bazan iya baiwa Jamilu auren ta ba duk da na san a shirye yake da ya tsayawa
Hauwa, ba don komai ba sai don ubansa, amma ba don yayi min wani abu ba, ko bai cancanta
a bashi aure ba.
Ko Hauwa-Kulu zata tsufa ba aure, tana nan a kwibi na, (a kusa da ni) ba inda zata da sunan
aure”.
Hauwa daga dakin ta duk tana jiyo abunda Inna ke fadi akan ta, sai ta samu kanta da
dimaucewa, don fisabililahi ko ba’a fada ba ta san zuciyarta ta amince da Yaya Jamilu dari bisa
dari, yau ga Inna na cewa a dakin ta zata tsufa. Ya Allah! Itafa mantawa take da makantar nan
tata, idan har ba bude littafi da zummar yin karatu taga duhu didim tayi ba, mantawa take bata
da ido, saboda rayuwar ta cike take da baiwarwaki da kuma alfarmomin Ubangiji masu yawa da
wadatar zuci.
Ji take babu wani abu da mai lafiya yake yi a rayuwar duniya wanda bazata iya ba,
musamman aure da hayayyafa.
Inna da