Showing 39001 words to 42000 words out of 46557 words

Chapter 14 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf

tace “innalillahi wa’inna ilaihi rajioun, ni Safiya me nake ji haka? Da auren nawa na
likewa Malam Isa? Ni Safiyar ko dai wata ce kike nufi kika dauka ni ce?” Maikosai tayi tsaki
tace.
“Ahap! Da bakin sa ya gayamin kin dawo zakuyi Gaiba ya aure ki, ko kin dauka akwai abinda
yake boye min?”
Inna ta mike tsaye tana fadin “Maikosai baki da lafiya, ina rokon Allah ya baki lafiya”, daga
haka ta fice ta barta tana ta sakin maganganu marassa kai bare kafa.
A zaure ta ci karo da Malam Isa zai shigo, cikin far’a Malam Isa yace “a’ah, Innar Hauwa da
kan ta yau a gidan mu? Maraba lale”, wani kallo da Innar Hauwa ta yi masa yasa nan da nan ya
sha jinin jikin sa, yayi tsuru-tsuru kamar bafaden da yayiwa sarki karya, tasa kai ta wuce abinta
ba tareda ta ce masa kanzil ba. Malam Isa ya fada gidan sa kamar an jefo shi, yana kwalawa Maikosai kira, a zaune ya
sameta tana ta kunkuni ita kadai yace “uban me kika cewa Safiya?” Tayi tsaki tace “munafurcin
da kuke kullawa na gaya mata na san komai” Malam Isa ya yi salati yace “amma Maikosai anyi
dabba a cikin garke, kin jika min aiki, tsakanina da ke Allah ya isa”. Maikosai ta tafa hannu tace “kace haka mana, saboda kafi so ku cigaba da ninke ni a baibai,
saidai inji sallamar kishiya a kaina, duk abinda kuke ciki na sani, da zaryar da kake tayi a gidan
su, har kuka yi kulla-kullar da kuka nemo ta kuka dawo da ita unguwar nan duk don kana
kulafucin ta”. Malam Isa bai iya tsayawa ya cigaba da sauraron ta ba ya juya da sauri ya bi bayan Innar
Hauwa.
Tana isa gidan shima ya iso sabida saurin da yake yi saura kadan babbar rigar sa ta tadiye
shi.
Tana shiga gidan ya doka sallama sai Inna ta dauko mayafinta data rataye a jikin kofa ta fito.
Sabanin da da zata yi masa iznin shigowa yanzu sai ta fita ta tadda shi a zauren.
Suka gaisa Malam Isa yanata rawar jiki yana bata hakuri wai bai san me Maikosai ta gaya
mata ba. Inna ta dube shi da manyan idanun ta irin na Hauwa masu neman fadowa kasa sabida
girma ta ce.
“Malam Isa, mutunci da makwabtaka ne tsakanin mu, ina ganin girman ka da mutuncin dake

tasakanin ka da maigidana, da hakkin makwabta da kake saukewa dare da rana, bai kamata
kuma ka yi min kazafi ba ban ji ba ban gani ba, yaushe nace zan yi GAIBA? Balle har na aure
ka?”
Malam Isa ya hau gumi yana bata hakuri yace wallahi shi da bakin sa bai yi zancen nan da
Maikosai ba, ya dai yi zancen cikin hira da Dan ta Sunusi, inda yace masa “da ace zata yi
Gaiba….”.
Bayan wannan bai kara komai ba, watakila Sunusin ne ya gaya mata, ita kuma ta canza
maganar yadda taga dama, amma ta yi hakuri. Inna tace “baka yi min laifin komai ba sai alkhairi
Malam Isa, amma ka sani ko Malam Bilyaminu bai dawo ba bazan yi wani aure ba, daga nan
har gaban abada! Burina kadai a duniya “Hauwa ce”. In rayu tare da ita, in kula da ita, in tsare mata mutuncin
ta. Amma bayan wannan bani da wani sauran abu da ya rage min a rayuwa ta sai fatan cikawa
da Imani”.
Malam Isa dai hakuri yake bayarwa, ya kuma roketa kan kada hakan yayi sanadin bacin
zumunci da makwabtakar su, ya bar zancen har abada ba zai sake tada shi ba, don Sarham ma
ya hanashi. Maikosai kuma zai ja mata kunne itama. Inna tace babu komai. Ya wuce.
Daga nan ya gaya mata maganar dabbobin ta daya kiwata mata, suna nan garke guda a
cikin kangon gidan sa. Inna ta rasa da me zata godewa wannan karimin makwabci, ta yi masa
godiya mai tarin yawa don tana matukar son dabbobin ta. Tace ya bar su anan su cigaba da
zama tare da nasa, zata cigaba da bada abincin su. Wanda yayi a baya Allah ya biya shi da
aljannah. Nan yake gaya mata ai SARHAMU yafi shekara yana sayen dussar su da harawar su.
Mamakin Inna da Sarham ya kara ninkuwa, ta ji yaron ya kara kwanta mata a rai, wato ba ita
kadai ba, ba ‘yar ta kadai ba, hatta dabbobin ta ababen kulawa da darajjawa ne a gare shi. Ya
Allah! Da me zata biya wannan bawan nasa banda addu’ar alkhairi mara yankewa gareshi, da
iyayen da suka kawo shi duniya da zuri’ar sa??? Sukayi sallama ya tafi, ta koma gida tana labartawa Hauwa abinda ya faru a gidan Malam Isa
da zauren su. Hauwa tafi Inna fusata, tace zata je ta tadda Talatu Maikosai ta gaya mata ba
abinda zai kawo su gidan ta koda zasu koma kwana a kan kwalbati in sha Allahu.
Inna ta hana ta tace “tura mata aniyarta mutuncin Malam Isan zaki duba, na gaya miki ashe
dabbobina duka suna garken sa yana kiwata mini har yau”. Wannan ne ya dan sanyaya ran
Hauwa ta daina jin haushin Malam Isa amma sosai ta shaka da Maikosai.
**** ***** *****
RACE COURSE, KANO
A
wajen kallon Polo na Dawakai wato a filin sukuwa (Race Course) dake unguwar Nassarawa,
Salele ya ga Jamil Zakari a matsayin wanda ya lashe kofin gasar dawakai (sukuwa) wanda
akayi a ranar, dama dai Jamilu kwararren dan Polo ne, sun dade suna haduwa da Salele a
wurare mabanbanta na tseren Dawakai, suna gaisawa, don ya san shi tun a jinyar da Hauwa
tayi, sanda ya kadeta da mota.
Yau da Jamil Zakari ya lashe kofi Salele ya shiga sahun samari masu kutsawa suna gaisawa
da Jamil Zakari Dan Agundi, Salele yana cikin samari ‘yan kallo masu cike da fata da burin
watarana su zama manyan ‘yan Polo kamar Jamil Zakari Dan Agundi.
An fara watsewa kenan Jamilu ya shiga farar motar sa kirar (kia picanto) zai tafi sai ya

hango Salele yana ‘waiving’ dinsa daga nesa wato yana ta dago masa hannu, har ya kunna
motar ya dakata har Salele ya iso da gudu yana haki yana dariya. Jamilu ya fiddo gudar naira
dari ya baiwa Salele, wadda a yanzu zata yi kimar kamar ace naira dubu daya. Salele don
murna bai san lokacin da ya hau barin zance ba. “Yaushe zaka zo gidan su Innar Hauwa ne? Sun dawo bada jimawa ba, sun gine gidan su ya
koma sabo dal, sun tare tuntuni, jiya ma Innar Hauwa ta shiga gun Innata sun gaisa har Innata
ta zo gidan ta yiwa Hauwa kitso”.
Jamilu yayi sakare! Yana sauraron Salele, kafin ya ji zuciyar sa ta harba, tsohon mikin son
Hauwa-Kulu da yake kwana yake tashi da shi ya motsa kansa a kasan ransa, bai san sanda
yace da Salele ya shigo gaban motarsa su je ba.
Salele ya kame a gaban mota suka dauki hanyar Kofar Na’isa.

Inna da Hauwa a tsakar gida, Inna na tankaden garin tuwo Hauwa na sallar la’asar akan
dardumar sallah anan tsakar gidan su mai yalwa da sanyin sabon siminti, saidai yanzu babu
shukokin su na Umbrella da bishiyar dalbejiya, don haka basu fiya zama a tsakar gidan da rana
ba sai da yamma irin haka ko da daddare. Sai sallamar Salele suka ji, yace Inna kuna da bako” Inna da yake ta san Sarham zai zo sai
tace “gidan bakon sa ne da zai tsaya a waje ya turo ka? Ko ba sallama yake da kansa ya shigo
ba? Yau nake ganin sabon salo banbarakwai wai namiji da suna Hajara, kace ya shigo, kuma
daga yau kada ya kara aikomin yaro idan yazo, shi da gidan su?” Salele ya koma yace da Jamilu Inna tace ya shiga.
Inna da Hauwa sai ganin Jamilu Zakari suka yi a kan su, yayi sallama kamar an jefo shi. Ya
shigo tsakar gidan su cikin kyakkyawar shiga ta hawan Polo.
Idanun sa akan Hauwa ya hau sakin Hamdalah a fili kafin ya zube gaban Inna kamar mai
neman gafara. Zai fara gaisheta Inna ta ce “tsaya-tsaya, wa nake gani kamar Jamilu? Wai dama
kai ne ka aiko Salele?” yace “ni ne Inna” tace “to sawunka a likkafa Jamilu ka juya ka koma inda
ka fito, kafin ka janyo min tijara, yau ko gaisuwa babu tsakanin mu wallahi ka ji na rantse ka
tashi ka fice mana daga gida, kada ka kara zuwa balle ka janyo min bacin rai Ina fama da ciwon
zuciya, zuciyata tayi rauni kuma bata da lafiya bazata iya daukar bakin cikin ubanka ba”.
Inna ta soma hawaye, tana rokon Jamilu ya tafi. Tun ba'a kaiwa Zakari labarin an ganshi a
gidansu ba. Jamilu ya mike ba shiru, yana kallon Hauwa da wani sabon so a cikin idanunsa,
musamman da yaga ta kara girma tayi wani irin kyau ta yi bulbul da ita, datar ta tayi sumul.
Likita Sarham ya tsaya mata da shan (freshmilk) wato danyar madara tana Nan fal firinjinta tun
dawowarsu ita take daddaka don bata iya cin abinci sosai.
Jikin sa yana rawa ya soma ja da baya. Tace “ko a lahira wani kan ci albarkacin wani,
albarkacin ka Zakari ya ci ban yi karar sa hukuma ta kwatar min hakkina da tozarcin da yayi min
a kan ka ba.
Don haka tun muna shaida juna muna kuma ganin sauran mutuncin juna to ka fita daga inda
muke”.
Jamilu ya juya a hankali ya fice, saida ya tsaya a zaure ya share zufa da hawaye, shi ya san
da gaske yake son Hauwa, son da yake mata ba shi ya dorawa kansa ba Allah ne. Saboda ita
har yau ya kasa yin aure, alhalin ba abinda bai mallaka ba na rufin asiri a rayuwar sa.
Daga nan gidan su Inna gidan Hajiyar sa ya wuce, ya kafa mata kahon zuka kan taje ta

baiwa Inna hakuri, kada ta hukunta shi da laifin da ba nashi ba. Hajiya Rumanatu na jin an ga
su Inna ta dauki mayafin ta tace su je ya kaita. Don dama zaman Jamilu har yau ba aure ya
dameta.
A mota Jamilu ya zauna, bayan Hajiyarsa ta shiga gidan, ya kifa kai a kan sitiyari ya rasa
inda zai sa kansa da damuwa. Bai san yana son Hauwa bama sai yanzu, data kara girma ta
zama cikakkiyar budurwa komai ya kai ya kawo. Hajiyarsa ta shige gidan da sallama.
Inna sai ganin Haj. Rumanatu tayi tayi sallama, Inna ta amsa fuska ba yabo ba Kuma fallasa
don ta gaji da nacin Jamilu da uwarsa.
Inna ta yiwa kawarta tun ta kuruciya wato Rumanatu tarba ta mutunci, irin ta tsofaffin kawaye,
bayan sun gaisa kafin Hajiya Ruma tace komai Inna ta hau rokon ta kan ta raba Jamilu da zuwa
inda suke, ya rabu da Hauwa. Tace, “ku yi hakuri, ni babu wani aure da zan yi wa Hauwa-Kulu
fau-fau, balle na dauketa da hannuna na kaita cikin zuri’ar Zakari a hallakamin ita da niyya
sabida ‘yan ubanci irin nasa, muddin Zakari yaji labarin Jamilu na zuwa wallahi zai juyo da
rashin mutuncin sa kan mu”.
Iyayen suna can dakin Inna suna zantawa suna kuma fahimtar juna, Haj. Rumanatu na mai
gamsuwa da hujjojin Inna akan bazata iya aurar da Hauwa ba, ba ga Jamilu kadai ba har ga
kowanne namiji ma. A lokacin Salele yazo zai wuce, sai Jamilu ya roke shi ya sadada a hankali
don Allah ya kira masa Hauwa su gaisa. Nan da nan Salele yabi umarnin ubangidan sa ya je yace da Hauwa tazo ana kiranta za’a
bata sako, tace a baiwa Inna mana! Yace tana da bakuwa ne sun kule suna sirri. Haka ya
kalallameta ta taso ta tako da hijab mai hannu har kasa a jikin ta zuwa soron su.
Sai ta ji muryar Yayan ta Jamilu ya ce “Hauwa!” Ya saki ajiyar zuciya ya sake cewa, “Hauwa
nine Jamilu, ni nace Salele ya kira ki, Hauwa ina kuka tafi duk tsayin shekarun nan kusan uku
sai dawowa nayi daga Delta na nemeku na rasa? Ko kinsan har yau ban yi aure ba ina
tsumayin dawowar ki Hauwa?” Hauwa ta dan waiga kamar me tsoron ko Inna na wajen, tace “Yaya Jamilu ne da gaske?”
“Nine Hauwa’u, I missed you so much, and I truly love you kin sani Hauwa”. Hauwa ta ji duk ta
rikice, ta kasa cewa komai domin maganar sa ta yau ta mata gingiringin, ta mata nauyi, rana ta
farko da wani da namiji ya furta mata kalmar so da bakinsa da nata, taji kunya har kasan ranta,
Jamilu yace.
“Ki bani dama don Allah Hauwa, in turo magabatana gun Inna, in sha Allahu zamu yi aure ko
a boye ne in ya so mu bar Kano gabadaya ba tareda Babana ya sani ba, ina mai baki hakuri
kan abinda ya faru, na ji komai bayan dawowata kuma ba inda ban neme ku ba cikin Kano da
wajen ta ban samu ko wanda yace ya san inda kuke ba. A kan ki Hauwa Babana ya kusa tsine mini, Inna kua ta kasa gane karfin son da nake miki
ba irin wand azan iya hakura bane, don Allah Hauwa ki manta da komai, ki duba ‘yan uwantakar
dake tsakanin mu, mu yi auren mu cikin alfarmar zumunci da kaunar juna, dama Bankinmu
zasu yimin transfer kwanannan zuwa Ikeja, in yaso sai mu koma can”. Hauwa ta rasa abinda zata ce, domin Jamilu ya matukar bata tausayi, ya tafi da imaninta, ya
kuma gama saye zuciyarta da wannan kauna da ya nuna mata, tayi shiru kawai tana sauraron
Jamilun da zuciyarta da kunnuwanta, tana mai yarda da kowacce kalma da kowanne harafi
dake fita daga bakinsa, zuwa can ta ce. “Ni fa Yaya Jamilu banida matsala, amma babu ruwa na a kan maganar aure. Allah ya sani

ban rike ka da komai a raina ba, sannan kuma bana kin ka, ina ganin abinda yafi, ka nemi
amicewar Inna ba tawa ba, ni din da komai nawa ababen ikonta ne kuma ni mai son yin biyayya
ce a gareta, don haka duk wani hukunci da Inna tayi akaina, inaso ko bana so, bani da ja a
kansa”. Jamilu ya gyada kai cikin gamsuwa da kalamanta, at least ya fahimci Hauwa bata kin auren
sa koda bata furta tana son shi ba, tofa babu kiyayyarsa ko kadan a tare da ita, ya rausayar da
kai yace,
“ni kuma na yi alkawarin zan lallashi Inna, idan ta bani ke zan kuma kula mata da ke kamar
yadda zan kula da kaina. I can understand her fear, kuma kwarai nake la’akari da abida take
hangowa (taking the marital responsibility of a blind person will never be easy) amma abinda ta
manta ni dan uwanki ne, jinin ki ne, I can possibly endure it fiyeda bare, aure sunnar Manzon
Allah ne SAW bai yuwuwa ace saboda lalura ta makanta baza’a yi shi kwata-kwata ba tunda ke
din ‘yar adam ce kamar kowa mai lafiyar yin aure, ni Jamilu na yi alkawarin zan zame miki miji
abin alfahari kuma dan uwa wanda zamu raba rashin idanun ki tare, sannan wanda zai tsaya
wajen ganin kin zamewa ‘ya’yan ki uwa tagari a yadda Allah ke son ganin ki, tsan tsaya tsayin
daka wajen ganin cewa lalurar rashin gani bai sa kin kasa basu kulawa ba.
Ni da kaina zan taya ki rainon ‘ya’yan mu Hauwa’u”. sai Hauwa ta kai tafuka ta rufe fuska
cikin jin kunya tana murmushi kamar tace kasar ta tsage ta shige cikinta.
Maganar Jamilu ta karshe kai tsaye ta sauka a kunnuwan Dr. Sarham Abbas ne, a lokacin da
ya kashe motar sa “opel astra’, ya tako zuwa gidan ya sawo kai soron, cikin takunshin nan mai
sauti gab-gab-gab na bakin cover shoes ma matukar daraja, ya shigo zauren su Hauwa, yayi
harr da idanunsa a fuskokin su. Yana sanye da shirt fara kal, wadda aka yi rubutun ‘Dolce&Gabbana’ a jikin ta, da bakin
Trouser ne na ‘Tokyo Jeans’. Kansa babu hula, sumar nan tasa baka wuluk ta fulanin Shanono
ta cika kan sa har ta nannade (curl), a kafafun shi bain takalmi ne sau ciki na bakar fata kirar
Italy. Da farko he was shocked, da ganin Hauwa tsaye da namiji a zaure, da abinda
kunnuwansa suka jiye masa Jamilu na fade, da kuma yanayin da yaga Hauwa wanda kiri-kiri
yana nuna tadin soyayya. Amma da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login