Showing 18001 words to 21000 words out of 46557 words
Chapter 7 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf
Sumayyah kanwarta wadda ta soma hawayen ganin yadda ransa ke hauhawa wajen baci
tun ma kafin yaji laifin da Surayyah tayi masa, taga basu da mafita banda ta gaya masa
gaskiya, sai tace.
“Bhaiya, maganar gaskiya ko sau daya bata taba bani komai tace in kai musu ba, sai ranar
da ka zo take gayamin ai kayan kwalliya take saye da kudin, ni ma kuma ban taba zuwa duba
su ba, wallahi na manta hanyar gidan sam, lokunan (are complicated), don haka dukkan mu
mun yi laifi Bhaiya, muna rokon ka in ka tashi hukuntamu, to kayi mana sassauci a hukuncin ba
don halin mu ba, ka yi mana uzuri da ajizanci irin na kowanne dan adam”.
Sarham ya kasa magana don takaici sai raba ido yake a kan su su biyu, amma kalaman ta na
karshe sun yi tasiri sosai a cikin ran sa dake tafasa, ya ciza fatar bakin sa kadan, yana kallon su
da lumsassun idanu duk sun zama unease, kada Surayyah ta ji labari, wadda ta kasa zama
tana daga tsaye har lokacin amma kafafun ta rawa suke. Da kyar Sarham ya hadiyi miyau, yace
cikin sanyin murya.
“My only two and beloved Sisters ne suka ci amana ta haka?!”
Sumayyah ta cigaba da hawaye tace “wallahi Bhaiya babu ruwa na, bata ma taba gaya min
ba ni sai ranar da ka dawo.
Ni nawa laifin na rashin zuwan maka ne kawai, da kuma rashin taya ka kula da abinda kake
so a bayan idanun ka, wanda ko kadan baka cancanci hakan daga gare ni ba. Kamata yayi ace
ko kare ka ajiye don kana son shi ya kamata in kula maka dashi in your absence balle mutane
‘yan adam. Na yi kuskure Bhaiya, amma na tuba, ka karbi hanzari da uzuri na, ajizanci ne na dan adam
da mantuwa, na tuba Bhaiya bazan sake ba”.
Sumayah ta durkusa a gabansa ta daga hannu cikin roko, hawaye na bilbila, Surayyah ta
kasa kare kanta amma hakika yau ta ji kunya, ta kuma yi nadama a lokacin da bata da amfani,
wato lokacin da ko ta bada sakon ba zai yi masa amfanin komai ba tuda ya riga da ya dawo,
gashi ta san ta sirewa dan uwan nata yanzu, saboda rashin amana, koda bai fada ba bai kuma
bai doketa ba.
Mama ta shigo da sauri jin kukan Sumayyah, tana tambayar su “me ke faruwa ne haka a
falon nan ake kuka har da kururuwa?”
Sarham ya ce cikin kololuwar feeling of disappointment “Mama kin gan su, su duka sun ci
amana ta!” Mama ta ce “kada Allah ya nuna mini ranar da zan haifi Da maci amanar dan uwan
sa, sun dai yi kuskure wanda ba wanda yake sama da aikata shi, ka yi hakuri Sarham ka yafe
musu kaji! Duk da ban san girman laifin ba”. Sarham ya dubi Surayyah (feeling disappointed) ya ce “Surayyah idan abinda kika yi
kyautatawa ne ga zumunci na da ke, na gode. Allah ya saka da alkhairi.
Ke kuma Sumayyah baki yi min laifin komai ba, amma daga yau na san matsayina a wajen
ki, na kuma ga ajin da kika ajiye ni, tunda bazaki zame min ‘yar uwar da a bayan raina zata kula
da haula ta ko abinda na bari ba”.
Sai ya sa kai ya fita, makwallaton sa har motsi yake don tsananin bacin rai, ba tare da ya
tsaya yi wa Mama bayanin laifin da suka yi masa ba.
Mama duk suka saka ta a duhu, ta rasa gane komai, sai da Sumayya ta share hawayenta ta
gaya mata komai cikin muryar kuka.
Mama ta kasa tuno mutanen da ake matsalar a kan su, ta san dai ire-iren jama’ar sa ne
da baya rabo da kyautatawa, da irin jajibe-jajibensa, amma hakika ta harzuka da abinda
Surayyah ta yiwa Yayanta, bata san ko su waye wadanda yake turowa kudin ba duk wata tun
daga Jeddah ba, ba kuma tareda ta damu da ta sani ba, amma tunda har ya dauki tsahon
shekaru uku yana turo musu kudi duk wata bait aba mantawa ba to masu muhimmanci ne a
wajensa, kasancewar ta san halin sa akan son tamakawa mutane da son kyautatawa na kasa
da shi da marassa lafiyansa, sai hakan bai zame mata wani sabon abu cikin halayen dan nata
Sarham ba, Mama tace. “Da gaske wannan cin amana ne, kuma zai fi bakanta masa rai ne kasancewar mutane
mafiya kusanci da shi ne suka yi masa”, ta dube su cikin fushi ta sake cewa “a duniyar nan in
dan uwanka ciki daya bai rike maka amana ya rufa maka asiri ba, in bazaku kashe ku rufe kai
da shi ba, ba tareda ko iyayen ku sun ji ba, waye zai yi maka? Sannnan da wa zaka yarda a duniya, kuma da wa zaka aminta?
Kin yi kuskure Surayyah, ba dan uwa irin naku ake badawa kasa a idanu ba, saboda shi din
dan uwa ne har dan uwa guda har da rabi, ko in ce Yayan da babu irin sa, ko don son da yake
muku da kulawar sa da kyautayinsa gare ku”.
Surayyah ta gama dukkan nadamar da mutum zai iya, a lokacin da yasan bai kyauta ba aka
kuma ankarar dashi. Cikin kuka ta ce.
“Mama don Allah ki bashi hakuri, na tuba na bi Allah na bi shi, zan biya shi duka kudin sa da
zarar na fara aiki, dama ban kashe da niyyar bazan biya ba, kawai ya zo ba ‘notice’ dina ne,
nayi niyyar in bata ta kai musu kafin lokacin zuwan sa, wallahi zan biya shi”, Mama ta wani
harareta ta ce “ta baya ta raggo. Duk abinda zaki biya shi yanzu bazai karba ba, kuma bazai masa amfanin komai ba.
Surayyah an yi bokon banza tunda shi ya koya miki son abin duniya, kayan kwalliyarbanza
kayan kwalliyar hofi, saboda Allah da me iyayen ki suka rage ki banda son kyale-kyalen ki na
banza da wofi da kika dorawa kan ki tun shigar ki jami’a, da son lallai sai kin hada kafada kin
goga da kawaye da suka dauki karyar rayuwa suka dorawa kan su?
Kullum ina nuna miki ‘reality’ akan barin sayen abubuwan nan masu tsada da suka fi karfin
aljihun ki ko na iyayen ki, kina ganin kamar ni kaina ban waye ba, tunda bana sayen turare su
‘designer’ sai Humrah sai Oud, har ni zaki nunawa sanin ya kamata akan rayuwar duniya
Surayyah? Yaushe aka haifeki har kikayi wayewar??” Mama tayi ta fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, daman tana cike da halin
Surayyah din kan irin tsarin rayuwar ta mai tsada, fadan da Sarham bai tsaya ya yi musu ba don
bacin rai shi Mama tayi ta yi musu ta wanke Surayyah tas. Wankin babban bargo. Surayya dai
sai hakuri take baiwa Mama ganin har tafi Sarham daukar zafi da al’amarin. Aka ce dan uwa rabin jiki, ganin yadda duk ta muzanta sai ta koma baiwa kanwar ta
Sumayyah tausayi, Summy ta ji kamar a maida laifin ya koma kanta, ita a cigaba da yi mata
fadan ita kadai, ta koma taya ta suka yi ta baiwa Mama hakuri da rokonta kan ta bashi hakuri in
ya dawo, sunyi alkawarin bazasu sake yin kuskure makamancin wannan ba, Sumayyah dai ta
ari laifin suka yafa shi tare da ‘yar uwar ta.
**** **** ****
SARHAM
D
a ya fita cikin zafin rai, wata motar Abbansa (Peogeot 504) ya dauka wadda tun saukarsa da ita
yake amfani, kasancewar bai kai ga sayen motar kansa ba tun dawowar sa, ya fizgeta a guje ba
tareda ya san wajen zuwa ba, yana dai so yayi nesa da gida don shi kansa ya san bai iya fushi
ba, baya son ‘yan kannen sa su ga launin fushin sa mara kyau, ana he’s jovial amma in yayi
fushi kamar zawayi yake komawa don rashin hakuri, musamman akan Surayyah da baya son
wasu halayenta.
Sai ya samu sitiyarin nasa na sarrafa shi, ya dauke shi yayi hanyar titin da zai sada shi da
kofar Na’isa. Yana tafe yana gayawa kan sa ya yafewa Surayyah duniya da lahira, ya yafe
mata, amma hakika ta ragewa kanta matsayi a idon sa. kuma ‘outing’ din da yayi niyyar fita
dasu zuwa Dam, don tayata murnar kammala degree ya gayawa kansa ya fasa. Duk da Mama ta ce zata bashi hakuri inya dawo, amma hankalin su su duka bai kwanta da
fitar sa cikin fushi ba da kuma ganin tsayin lokacin da ya dauka bai dawo gidan ba.
Ya isa kofar Na’isa da yamma lis, ya karya kan motar sa zuwa titin da zai kai shi lokon
su Hauwa, yana tafe yana tunane-tunane akan su, ko a wane hali zai same su? Ko Hauwa ta
gama makaranatar sakandire yanzu? Ko yaya suke rayuwar haka babu tallafin kowanne namiji?
Ko Baban su Malam Bilyaminu ya dawo? Ko yaya idanun Hauwa? Allah Masani! Bai san
meyasa zuciyar sa ta damu da al’amarin su ba, take kuma daraja su, yana saka damuwar su a
ran sa in ya tuna a hannun sa Hauwa ta karbi shaidar makanta da lasisinta, daga zuwa neman
magani. Shi ya san da ace ba shi yayi mata aikin nan ba, da bazai damu ba don an samu
mishkila.
Har gobe kuma ya kuma kasa yafewa kan sa a kan makancewar Hauwa, ya ki cire abun a
ran sa, duk da ya san kaddararta ce, shima kuma ba yin kansa bane amma har gobe Sarham
yana ganin negligence dinsa ne wato (sakacinsa da rashin iya aikin sa), su suka janyo har
Hauwa ta kai ga rasa idonta completely. Haka tunda ya tafi Jiddah yau shekara uku bai taba kasa tuno su ba kullum, har
Allah-Allah yake a yi albashi don kawai ya tura musu, ranar Allah dai-dai ce da baya tuna su,
tare da yi musu addu’a da fatan alkhairi. Ya san kuma kudin da yake aiko musu daga albashin
sa zai ishe su kananan bukatocinsu na yau da kullum da makarantar Hauwa. Bayan motar Abban sa da ya tuko, shake yake dankam da tsarabar su Inna rankatakaf!
Wadanda tun daren jiya ya saka su a mota yana jiran ya samu nutsuwa ya je kofar Na’isa, yayi
ido hudu da Innar sa Safiyya, don ba Hauwa yake kewa ba Inna yake kewa. Eh mana, Hauwa
da bata son sa kuma take kullace da shi. Hauwa danger Hauwa hukuma. Har sabuwar waya nokia karama ya sayowa Inna, da alkawarin yanzu in ya koma Jiddah
kai tsaye zai ke kiran su. Idan har Hauwa ta kammala sakandire da kyakkyawan sakamako ya
fara tunanin bincike akan yiwuwar cigaba da karatun ta a jami’a, idan hakan mai yuwuwa ne.
Zai nemi dai wanda zaiyi ‘coaching’ din sa akan ilmin ‘visual impaired’, ba zai koma Jeddah
ba sai ya tabbatar rayuwar su bata da matsala ta zama ‘stable’ kuma Hauwa na kan turba ta
tafiya zuzzurfan ilmi.
Wanda shine kadai zai zame mata gata a dukkan rayuwar ta, a matsayin ta na mai nakasar
da ake kira mutuwar tsaye.
To amma me? Sai zuwa yake yana dawowa a inda ya san lokon gidan su Inna yake
situating, amma baya ganin gidajen da ya sani a wurin sai fili fetal. Da aka zagaye da
langa-langa. Ya ilahi! Ko dai yayi batan kai ne? Ko makuwa yayi? ko kuma ya manta hanya ne?
To amma da mamaki ai ace ya mance hanyar gidan su Hauwa, ko shekaru goma yayi
baya nan ba uku ba, in dai ba juyewar kwakwalwa ya samu ba ko shafewar tunani wato
‘amnesia’. Kuma dai ga Kofar Na’isan nan dai tana nan bata je koina ba.
Da ya gaji da zuwa da dawowa wato ya gaji da safah da Marwah a cikin mota sai ya fito yayi
ta zagaye wajen da kafafun sa, amma ya kasa ganin gidan Malam Bilyaminu, ya kuma tabbatar
anan gidan yake, sai ma yaga ‘pure water’ na leda ake bugawa a filin wajen. Kamar an maida
wajen kamfanin ruwa leda. Ya tambayi wani saurayi cikin masu buga ruwan ledan don Allah ko inane gidan
Malam Bilyaminu dan Kofar Na’isa? Ya ce da saurayin “kamar na maku, don na jima bana nan”.
Saurayin yace shima bako ne a unguwar, amma bari ya hada shi da Malam Isa mai faskare shi
da ya dade a unguwar. Gidan malam Isa ne kawai ba’a rushe ba cikin gidajen wurin don gidan yayi gefe sosai,
saurayin ya raka Sarham suka samu Malam Isa a zauren gidan sa yana aikin itacen sayarwar
sa, ya yiwa Malam Isa bayanin wanda Sarham ake nema ko ya san shi? Wai gidan Malam
Bilyaminu. Malam Isa ya bar abinda yake yi ya juyo ga Sarham sukayi musabiha, sai ya bashi
wajen zama kan buzun sallahr sa yace ya zauna, da ya tambaye shi ko wa yake nema a gidan
Malam Bilyaminu? Sarham yace.
“Innar Hauwa”.
Sai Malam Isa ya tambayi Sarham “kana da alaqa da Innar Hauwa ne?” Sarham yayi
dan jim! Kafin yace “eh, amma na dade bana kasar, ina fatan ba wani abu ne ya faru da su ba?”
Malam Isa ya nisa yace, “eh toh, samari, ai Innar Hauwa ta gamu da sharrin wani azzalumin
kanin miji, ya sayar da gidansu, rana daya muka ga an zo ana rushe gidan, aka maida wurin
wajen hayar neman kudi kala-kala, na so ta zauna mu je kotu a kwato musu hakkin su ni da
sauran makwabtan su, kasancewar a gaban mu Zakari ya sayarwa da dan uwan sa gidannan
aka raba rigima tun a lokacin a gaban marigayi mai unguwa, amma matar nan ta ki tsayawa, ta
gudu daga gidannan bamu sani ba, yau kusan shekara uku zancen nan da nake maka, bamu
kara jin duriyar su ba ita da ‘yar ta Hauwa-Kulu”.
Sarham ya ji idon sa har rawa yake banda fatar idon dake raurawa itama, da kyar ya iya
yace wanene kanin mijin nata? Ya ce.
“Zakari sunan sa, don kawai dan sa ya zo yace zai auri Hauwa-Kulu, shine ya sayar da
gidan don ya kore su ko ince yasa aka rushe shi, to ya ci galaba kam don daga ranar da aka zo
aka rushe gidan su basu kara waiwayar kofar Na’isa ba, kuma ba wanda ya kara jin duriyar su,
ina tabbatar maka bazasu zauna a Kano ba yadda suka fita a tagayyare, wutsiya zage, kuma
cikin mummunan bacin rai.
Jifa aka dingayi da komai nasu. Tausayi yasa na tattara tumakin ta da akuyoyin ta na kado
su gida na, na hada na nawa na cigaba da kiwata mata, muje in nuna maka su cikin shekaru
uku gasunan suna ta hayayyafa ban san ya zan yi da su ba”.
Sarham ya rasa a halin da yake ciki tsakanin tashin hankali da gigicewa, yace da Malam Isa
“basu da wasu ‘yan uwa da zasu iya zuwa wajen su?” Malam Isa yace “eh, toh, ai dukkan su
‘yan cikin Badalar nan ne a sanin da muka yi musu, in ma suna da su, to mu bamu san su ba,
basu da wasu ‘yan uwa da bamu sani ba, dangi kam sun kare ai, kuma bana jin a zuciya irin ta
Innar Hauwa zata yarda ta rabi wani nata in ma tana da shi.
Tun tali-tali tanada wani irin hali, tafi gane rayuwa ta tsayuwa akan kafafun ta fiyeda ta rabu
da wani ya taimaka mata, har kuwa bayan batan mijinta, bata taba neman taimakon kowa ba”.
Sarham yace “shin a ina wannan Zakari din yake?”
Zai so kwarai yayi ido hudu da wannan Zakarin, don kwatarwa su Inna hakkin su, zai so
kwarai yayi shari’ah da shi, daganan har kotun daga ke sai Allah ya isa! Domin ya kwatowa Inna
hakkin ta, a daure shi har sai igiya ta yi rara, amma Malam Isa ya gyara murya ya kuma gyara
zama, yace masa “ka manta da Zakari kawai, ka nemo su Hauwa din shine mafi a’ala, ganin
Zakari bazai kare ka da komai ba sai karin bacin rai, don zai iya yi maka mummunan bita da
kulli, idan ya gano su Safiya suna da wani gatan bayan shi a duniya.
Ai sanin cewa basu da kowa da zai tsaya musu ne yasa yayi musu haka!”.
Sarham yayi shiru, can yace Baba ina so in sake saye filin wajen ne, ina nufin filin gidan nasu
daga hannun wadanda suka saya”. Malam Isa yace, ai hakkin mallakar filin ya bar hannun
Zakari tuntuni, wannan mai kamfanin ruwan shi ke da wajen yanzu, kana iya tuntubarsa ko zai
sayar maka, amma lallai sai ka nunnunka masa kudi”. Tare suka je har gidan mai kamfanin ruwan ledan da ya kafa rumfa a filin gidansu Hauwa