Showing 21001 words to 24000 words out of 46557 words

Chapter 8 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf


yana sana’ar ruwa, suka gaisa, Sarham yana hadiye hawayen sa yace, so yake ya sayar masa
da filin wajen, inyaso ya yanka masa kudin ko nawa ne zai biya shi, ya bashi takardun mallakar
kangonnan. Hakan kuwa aka yi, da mutumin ya ga kudi ya amince, ya yanka kudin da yaga dama
Sarham ba musu yace gobe zai kawo masa su (in cash) ya karbi takardun wurin bisa idanun
shaidu kwarara da sabon mai unguwa.
​ Bayan ya bar Kofar Na’isa kasa komawa gida yayi, ya kuma kasa tuka motar, ya koma
gefen titi ya kashe motar ya kifa kansa a kan sityarin, yana tuno fuskar HAUWA-KULU da
kyawawan manyan idanun ta da ya nakasta mata su bisa kuskure, da kuma murmushin Innar
ta. Daga baya ya ja motar ba tareda ya san wurin zuwa ba, haka yayi ta yawo kwararo-kwararo
titi-titi a cikin BADALOLIN KANO, ya taho tun daga Kofar Na’isa, ya isa Kofar Gadon kaya, ya bi
ta kofar Dukawuya, ya bulla ta kofar Kabuga, daga can ya karya kan motar yayi kofar Kansakali,
ya taho har Kofar Ruwa, bai ga ko mai kama da Inna ko diyarta Hauwa ba, ya dawo baya ta
cikin gari ya bulla ta Sabuwar Kofa, kafin ya isa kofar Nassarawa ya dawo da baya ya isa kofar
Dan agundi yana ta fatan Allah yasa ya ga Inna da Hauwa koda a hanya ne, amma har duhu ya
baibaye sararin samaniya, wanda yasa ya daina shaida fuskokin mutane, kuma man motarsa
ya kusa kafewa, ko mai kama da su bai gani ba, duk kuwa da irin kallon kurillar da yake yiwa
mata da musaki bisa tituna da Kofofin Kano, da cikin unguwannin Badala.
​ Allah sarki Dr. Sarham! Kafin ya koma gida har rama yayi, yayi zuru-zuru yayi dan wuya
sabida yunwa da damuwa da gajiya da bacin rai. Kamar ba sabon ango ba, na Madinah bada
kanka a sare! Ya koma gida a jigace, wajen karfe goma na dare, amma sai ya kasa zaman falon
duk kuwa da cewa ya gansu a zazzaune duk zaman jiran dawowar sa suke yi har Abba, domin
a bashi hakurin laifin Surayyah gareshi.
​ Ganin yana nema wucewa dakin sa bayan ya gaida Abba da Mama, ba tare da ya ko
zauna an yi hira yadda aka saba ba. Abba ya dakatar da shi, ta hanyar bashi kujera da hannun
sa ya ce ya zauna, Sarham ya tsaya a tsaye kamar mai ciwon kafa, sai Abba yace,
“lelen Abba daga ina kake haka, kamar an maka dukan tsiya? Ka gan ka kuwa?”.
Sarham bai yi aune ba yaji wata irin hajijiya na neman kayar dashi saboda yunwa da gajiya,
ba shiri ya lalubi kujerar ya zauna yace “wash! Abba, kai na!” Ya kama kannasa da hannu
bibbiyu. Abba ya ce “sannu, Sumayyah kawo masa ruwa da abinci, hajijiya ai yunwa ce, me ke
faruwa?”

Sarham bai san lokacin da yace “Abba na neme su na rasa, ba inda ban dub aba, ba Badalar
Kano da ban zagaya ba, ko mai kama dasu ban gani ba, duniyar nan cike take da azzaluman
‘yan uwa Abba, kowanne dan uwa ya samu faraga sai ya ci amanar dan uwan sa in baya nan,
why?” ​ Surayyyah ta saka kuka don ta dauka wannan maganar da ita Sarham yake ta ce
“wallahi Bhaiya ban yi da niyyar cin amanarka ba, na tuba ni kam na shiga uku! Ka dauki
abinnan da zafi har fiye da kima Bhaiya” wata uwar harara daya zabga mata ya ce a fusace “na
saka ki a cikin magana ta? Kin san wa nake nufi ko su wa nake magana akan su?” Mama ta ce “kayi hakuri Sarham, zancen nan ya wuce don Allah bazata sake ba na mata
fada sosai”.
Yace Mama ni ba zancen ta nake ba Mama, already na yafe mata, na fadawa kaina da kaina
na yafe mata yafi sau shurin masaki, tun fita ta ban fita da ita a raina ba, zancen su Inna da
Hauwa nake,”
“Su waye kuma Inna da Hauwa kuma?”
Abba da Mama har suna hada baki wajen tambaya, da tunanin ko gamo yayi, ya ce “yarinyar
da ta makance a hannu na, (excuse me) na makanta ta by mistake, tun daga lokacin kuma
nake kula da karatun ta.”
“Au ho!” in ji Mama, ai kuwa ban manta da zancenta ba, da yadda ka shiga damuwa a
lokacin, har yanzu idon nata bai gyaru ba? Kuma wai basu da Uba ne?”
Sarham ya baiwa iyayen sa kaf labarin su Inna, tun ranar da suka fara haduwa a asibitin
Murtala, da aikin da yayi mata da sabon da ya shiga tsakanin su aftermath wato bayan hakan,
da yadda aka yi ya kai Hauwa makarantar (Special School Kano), da yin sallamarsu lokacin da
zai tafi Jeddah, zuwa yanzu da ya dawo yaji abun da ya faru da su daga kanin Baban ta, ya
kuma gaya musu batan Malam Bilyaminu tun kafin haduwar sa da su.
Mama don tausayi har da kwallah tace “Allah to ya jefa su a hannu nagari, ya kuma bata
lafiya a duk inda take, kai kuma ya baka ladan taimako”. Abba yace “amin, Allah kuma ya saka
musu. Ya bi musu hakkin su. Amma don Allah ka ci abinci, ka huta, ka nutsu, ka tuna cewa kaifa
sabon Ango ne akwai nauyi yanzu a kan ka. ​ Ya gaya masa cewa sunyi waya da Daddyn Madinah dazu, nan da kwana uku za’a taho
da ita Kano, ba sai ya koma Jeddah dauko ta ba, Babanta yace ya daina cewa ango ya zo ya
dauketa kasa-ya-kasa tun daga abinda ya faru kan mijin ta na fari, ina ya tanadar mata domin a
sauke ta? Sarham babu wani doki a tare da shi don zuciyarsa bakidaya bakikkirin take, yace shi ginin
da ya fara bai kammala ba, sai dai Abba ya ara masa gidan sa na Rimin Gata (nan baya
sabuwar jami’ar Bayero) a sauketa acan. Yace amma in son samu ne shi ya fi so Madinah ta
zauna a nan gidan su tashin farko, ba don komai ba sai don ta saba da su Mama tunda na dan
lokaci ne zasu koma Jeddah.
(A baya baiyi niyyar komawa Jiddah ba amma yanzu Kano ta fice masa a rai). Daddy ya ji
dadi sosai, don a yadda na gina rayuwar iyalinsa da so da kaunar juna, kwarai yake so matar
duk da Sarham ya aura ta zamo daya daga cikin iyalin sa, baya so don yayi aure yayi nesa
dasu, musamman saboda shakuwar sa da kanwarsa Sumayyah, shakuwar dake tsakanin su
har tsoro yake kada yayi aure mace ta zamo sanadinta, Abba ya ce,
“shike nan hakan yayi kyau, madallah, ita Sumayyah sai ta koma dakin Surayyah, su zauna

tare for the mean time, sai a gyara ma Madinah dakin Sumayyah ta zauna har zuwa lokacin da
zaku koma Jeddah din, Abba ya tambayeshi ko ya gama kwas din sa? kuma yaya batun aikinsa
na Murtala da yake batun komawa? Ya gaya masa cewa ya gama, amma zai koma bikin
kammalawa da karbo shaidar kammalawa, shi da Madina har yanzu basu zauna (officially) sun
magantu sun yanke shawarar inda zasu zauna ba. Amma yanzu kam yafi so ya koma Jeddah.
Bayan ya koma dakin sa yayi wanka ya yi sallolin dake kansa sai ya samu kansa da zama
dirshan akan dardumar sallahrsa ya rasa abinda ke masa dadi, abun mamaki ga kiran Madinah
na ta shigo masa akai-akai don tun bayan da aka daura musu aure basu yi magana ba, amma
ga mamakin sa ya kasa dagawa, a lokacin damuwar da yake ciki tasa komai ya fita kan sa, ya
samu kan sa da daga hannu yana yiwa su Hauwa addu’a, damuwa tasa a ranar ko runtsawa na
awa guda bai iya yayi ba.
​ Washegari yaje ya kai kudin filin gidan su Hauwa, ya karbi takardun filin a gaban
kwararan shaidu dattijan unguwa su malam Isa da sabon mai unguwa, kowa yana ta mamakin
ko me zai yi da filin, shi ba dan unguwar ba, ba kuma dan Malam Bilyaminu ba, amma dai ai
yace shi dan uwan Innar Hauwa ne. Wayar da ya sayawa Inna sai ya samu kansa da mallakawa Malam Isa, ya kuma karbi
lambarsa yace zasu dinga gaisawa kuma zai dinga turo masa kudin abincin dabbobin Inna da
yake kiwata mata, ya fadi hakan ne a lokacin suna cikin garken dabbobin, suna zagawa yaa
kallonsu, ya ga yawan su ya karu nesa ba kusa ba akan sanin da yayi musu, sosai ya jinjinawa
Malam Isa da iya kiwon dabbobi da zuciyar makwabtaka irin ta mutanen da, ya kuma yanke
shawarar taimaka masa akan kiwon dabbobin shima daga ranar da kudin abincin su.
​ Malam Isa yana ta murnar mallakar waya, saboda a lokacin bata zama a hannun
talakawa, ya sakawa Sarham albarka yafi cikin carbi. Da zasu rabu kuma Sarham ya gaya
masa niyyar sa, wato yana so ya gine filin nan, so yake ya a gina musu gida kwatankwacin
nasu a filin su, gini na zamani, ya ce shi ba mazauni bane don haka zai turo magina kuma zai
bar komai a hannun sa da masu ginin, yana so Malam Isa ya kula da ginin har a gama, don zai
jima bai dawo Kano ba.
Malam Isa yana ta mamaki, ko meye alaqar wannan matashin mai kirki da kyakkyawar zuciya
da su Innar Hauwa haka, haka suka yi sallama bayan Sarham yayi masa kyautar kudi, kuma a
washegari aka saka tubulin harsashin ginin gidan su Inna da kudin da jima yana Tarawa don yin
nasa ginin gidan. ​ Kwana uku bayan nan, ba abinda Sarham yake yi sai yawo a cikin garin Kano yana
faman neman INNA da HAUWA har tambaya yake yi ko an san su, ya fasalta kamannin su,
maimakon ya maida hankali wajen shirin taryar amaryar sa Madinah-Munawwarah mai isowa
daga Jiddahn Saudi Arabia. ​ Amma ko wanda yace ya san mai kama da su bai samu ba. Wannan yasa duk zaman
garin Kanon da dokin amarcin dake gaban sa ya kara fita a ran sa. Ya sa a ransa da Madinah ta
zo bazasu dade ba kamar yadda yayi niyya zasu koma Jeddah, in yaso ya karbi tayin aikin da
aibitin “SAUDI-GERMAN” suka yi masa, wanda a baya yaki karba, don ya so ne ya dawo gida
kwata-kwata ya cigaba da aikin gwamnati a manyan asibitocin Kano da ya tabbatar sun fi
bukatar sa, in yaso ya bude private clinic nasa na kansa ya hada, amma a yanzu bai san haka
zuciyar sa ta dauki su Inna da matukar muhimmanci ba sai yau da take gaya masa rashin su ba
zai sa ya ji dadin zaman Kanon bakidayanta ba, duk da gatan iyaye dana ‘yan uwa dake

baibaye da shi, ga na cikar buri, wato na mallakar Madinah abar son sa.
Amma duka ya kasa enjoying ko daya. Saboda wasu bare? Ya ilahi, wane irin abune
haka??? Shi kansa yana mamakin karfin ‘bond’ din dake tsakanin sa da ‘Inna’ don bazai ce
‘Hauwa’ ba.
Don haka sai mu ce Amarya Madinah ta shigo kasar Nigeria da kafar hagu, don kuwa likitan
zuciyarta Sarhamu babu walwala kota kwabo a tare da shi, gabadaya ya birkice da neman Inna
da Hauwa, har iyayen sa suka fara damuwa da saka ayar tambaya, suka zaunar da shi suka ce
ya gaya musu gaskiya, bayan tausayi da taimako, meye alakar sa da mutanen nan ne? Ta yaya zai yi sabon aure amma ya raba hankalin sa da nutsuwar sa, ai sai suma ya saka su
a damuwa.
Sarham ya ce babu wata alaqa tsakanin sa da su, sai kauna ta fisabilillahi da haduwar jini,
yace shi kawai yana tunanin a wane hali suke ciki ne, yana tsoron fadawar su mugun hannu ko
fadawa hannun kanin uban Hauwa wanda baya kaunarsu kuma azzalumi ne, sannan basu da
kowa da zasu kira nau in ba shi din ba (Zakari). Mama tayi fuska ta ce daga yau bana son ka kara fita neman su tunda dai ba kananan yara
bane, Allah shi yake kula da bayinSa marassa karfi da masu karfi, kafin ka shiga rayuwar su ai
babu uban nasu, kuma hakan bai hana su rayuwa mai kyau da shaker numfashi ba. Saidai ban
sani ba ko kana da wani dalilin a kasan ran ka a kansu bayan wannan?” Wai meyasa mutane suke kasa fahimtar sa ne akan Hauwa da Innarta? Zai iya rantuwa babu
wani dalili a kasan ransa a kansu bayan wanda ya fada musu. Kwatakwata kenan babu alaqa ta
mutunci da zumunci a tsakanin al’ummar Annabi sai mai kunshe da MANUFA? Haka mafa
Sumayyah ta taba cewa wai….. abun babu ko dadin ji domin kuwa yadda yake kallon ta
muharramar sa haka yake kallon HAUWA-KULU.
​ Can tsakar kansa ya tsinkayi sautin Abba yana cewa “talakawa nawa ne a Nigeria da
suke cikin halin kaka-nikayi? In ka ce duka sai ka tsayawa rayuwarsu ka hada kan ka da abinda
ba zai taba yiwuwa ba, tunda dai kayi taimako iya yinka wanda dace ya kamata ka bar su a
hannun Ubangijin da ya halicce su haka, ka maida hankali ga abinda ke gaban ka yanzu. Wato
sabuwar rayuwar ka ta girma da yah au kanka”.
**** **** ****

THE ARABIAN BRIDE
M
adinah na gidan kakannin ta bayan saukarsu a Kano, a daren ranar za’a kawo ta wajen Mama,
an gyara dakin Sumayyah da kyau wato inda za’a sauke ta da ‘yan uwanta. Gidan ya dauki
kamshin turaren wuta dan Maiduguri ko ta ina mai dadin kamshi, Mama da kawayen ta su Barr.
Hannatu Mahdi da ’yan uwanta suka shirya karbar amarya da danginta. Har falon Mama aka shigar da Madinah-Munawwarah cikin lullubi, kafin a yi addu’a ta
musamman ‘yan rakiyar amarya da ‘yan karbar amarya duk suka watse, gidan ya rage sai
mutanen gidan kadai.
Rana ta farko dasu Mama suka ga fuskar Madinan Sarham. So beautiful da ita, karshen
gayu karshen class, Masha Allah.
​ Mama ta ce a ranta dole kam Sarhamunta ya kamu ya tsunduma iya wuya, Madinah ko
daga cikin lullubi kafin a ganta a zahiri an san matar manya ce kuma ‘yar manya ce.

Tayi fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a mai alkbarka. Ya kade fitina, ya basu ikon
sauke amanarta da aka damka musu.
Yau Madinah ta samu kanta a gidan surukan ta wato iyayen Sarham suna ta haba-haba da
ita. Sumayyah da Surayyah ma ba’a bar su a baya ba wajen kula da bakuwar tasu, Surayyah
kuwa duk da ‘yar tsamar dake tsakanin ta da Sarham sai da ta kasa shiru, da ya shigo gaida
Mama bayan ya dawo gidan da daddare sosai tace dashi. “Yaya Doctor, wallahi ka iya zabo mata, class iya class malam, kyau iya kyau, dubi mata
kamar hurul- eeni, kamar ita tayi kanta don kyau da gayu.
​ Wata mummunar harara Sarham ya zabga mata yace “ki fita idona in rufe, ki bar shiga
harkata, na rantse Mama ki raba ni da Surayyah”. Sannan ya gaida Mama da gajiyar hidimar
jama’a, wadda keta dariyar masifarsa, Mama tace “ban taba ji ko ganin ango yana masifa ba,
duk wani ango far’a yake yi da farin ciki banda kai, tashi ka shiga dakin Sumayyah Madinah din
tana can”, cikin jin nauyin Mama irin wanda bai taba ji ba a rayuwarsa yace,
“Mama ki barta, sai da safe in Allah ya kaimu zamu gaisa in sha Allah, a barta ta huta, na san
ta gaji, gata bata jure hayaniya”. Nan kuwa kunyar idon Mama ya hana shi zuwa yiwa Madinah
barka da sauka cikin rayuwarsa.
​ Sai da ya koma dakin sa yayi shirin kwanciya sannan ya kirata a waya, Madinah ta fito
wanka kenan tana saka kayan barci zata kwanta kiran sa ya shigo mata, sai da ta ja aji, don taji
haushin kiran data yi masa bai dag aba kuma bai biyo bayan kiran ba, kafin ta dauka da
kyakkyawar sallama a bakin ta, maimakon ta ce tayi fushi, saboda bai zo inda take ba tun
saukar ta a Kano, ko irin kananan korafin nan na amare da ke cikin lokacin da ake mararinsu,
ina! Madinah nata salon daban ne, da wuya kaga bacin ranta akan abu, komai tana kokarin
maida shi ba komai ba a rayuwarta (banda kishin Sarham), don ko shi Sarham zai rantse bai
san me yake bata ran Madinah ba, sai ta karya murya cikin rangwadarta da zakin muryarta
tace,
“daga jin muryar ka mura kake, ina fatan angon Munawwarah yaci abincin dare?”
Sarham yayi wata wawuyar ajiyar zuciya, tuni ya manta da kishin da yaci alwashin gasata
akansa da zarar ta shigo gidansa, wato fushin aurenta da AVM Alkali, ya samu kansa da cewa
“kayya! Anyway, kin zo lafiya Madinahtul-Munawwarah, ya gajiya ya aka ji da zafin garin mu?”
Madinah tace “garin ku kai kadai? Ai ba’a canzawa tuwo suna.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login