Showing 30001 words to 33000 words out of 46557 words
Chapter 11 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf
Innar Hauwa bazata zauna babu sana’a ba, musamman ta abinci, don aljanunta
na girki da tsaftane. In ta fara girki duk gidan sa sai miyau ya tsinkewa kowa, saboda kamshin
girkin ta, yanzu ma ashe shiyasa ta zabi sana’ar abinci, Malam Isa ya kara da cewa Sarham, “to Allah yasa ba’a tashar suke kwana ba, ko don ‘yar makauniyar nan Hauwa-Kulu, kada
mazan tasha su dinga yi mata dan kira”.
“A’uzubillah!”
Sarham ya fada a zuciyar sa, lokacin sun kawo kofar rumfar abincin Inna mata biyu da
dattijuwa daya suna ta kula da kwastomomi daya na zuba abincin in anzo saya, sukayi musu
sallama, suka amsa suna tambayar su “me za’a zuba musu?” Kai tsaye Malam Isa ya ce nawa
kwanon shinkafa da wake da miya da nama? Sarham yayi masa kallon takaici ya ce “Malam Isa abinda ya kawo mu kenan?” ya ce “au, yi
hakuri na manta ne, ‘yammata Innar Hauwa-Kulu muke nema”.
Dattijuwar mai zuzzuba abinci ce ta basu amsa. “Ayyah ai Innar Hauwa jiki ya ki dadi, yau
wata guda kenan bata zo shagon nan ba, na ji ance ma bata gari, wani makwabcin su ya kai ta
gidan mai maganin gargajiya na ‘ciwon zuciya’, a can wani kauye wai Albasu, don Innar Hauwa
sam-sam ta ki zaman asibiti. Allah ne yayi Innar Hauwa na da nisan kwana da yanzu wani zancen ake akan jinyar ta ba
wannan ba”.
Sarham yace cikin yanayina gigicewa “na roke ki da Allah da Manzon sa ki raka ni gidan nata
yanzunnan”.
Numfashin sa har gwamuwa yake tsabar yadda ya saka Innar da son ganin su a ransa, dama
tace watakila bazasu kara ganawa ba, watakila sallamar su kenan, Allah ya gani yayi duk iya
kokarin sa a kan ya san halin da suke ciki a wancan zuwan nasa Allah bai yi sun hadu ba.
Matar ta sallami kwastomomi sannan ta baiwa ‘yammatan sallahun abinda zasu yi mata kan
ta dawo, daga nan ta bi bayan Sarham da Malam Isa zuwa mota.
Suna tafe tana basu labarin ai Innar Hauwa ta dade a kwance, watakila tayi shekara tana
jinya, shagon ma yanzu ya zama nata.
Don dama haya muke kamawa, a da ina mata aiki ne da ta kwanta ta bar sana’ar sai nikuma
na kama rumfar hayar, ba don ‘yar ta makauniyar nan mai kokari ba da tuni Innar Hauwa babu,
da tuni ta kashe kanta da ciwo a gida, don bata son maganin asibiti.
Sarham ko magana ya kasa, yana jin ta ita da Malam Isa suna ta maganar kin asibiti irin na
Innar Hauwa, yace ai tun sanin da yayi mata a haka take da akidarta ta amanna da maganin
gargajiya.
Malam Isa yace “kuma fa akan kin asibiti ne har idon Hauwa ya mutu da hakiya, ni nan ba
yadda ban yi da ita ba akan ta kai ta asibiti tun yana apolon sa, sai da ta ga ‘yar ta gama
makancewa sannan ta kaita, a lokacin aka ce ido ya mutu, yadda suka je haka suka dawo.
Matar na nunawa Sarham hanya har suka isa wani dan mitsitsin gida a wata unguwa can ciki,
kamar duk rabin unguwar kwatami ne, kasancewar unguwa ce ta masu karamin karfi sosai.
Amma gidan nata sai suka same shi a kulle.
Sarham kamar ya dora hannu aka yayi kuka, don matuka ya saka ran sa da ganin Innar
Hauwa da Hauwa a yau ba sai gobe ba, koma musu yayi kamar sabon kamun hauka, don cewa
yayi da matar ba inda zai bari ta je sai ta hada shi da Innar Hauwa, ta ce itafa bata san gidan
mai maganin da aka kaita ba, sai yace to su kai shi gun makwabcin nata da ya kai ta Albasu ne
koma ina ne, in ba haka ba itada makwabcin na Inna zai yi karar su ga hukuma kan cewa sun
batar da bayin Allah.
“Yau nake ganin abun da ya gagari Kakata” in ji Tafada mai Tuwo, daga abun arziki zaka
daura min jakar tsaba kaji su bi ni, ni fa tsakanina da Innar Hauwa mutunci ne kawai, Allah ya
gani ko a kwanciyar nan da tayi sau biyu ina taya Hauwa kinkimar ta ta kai ta asibitin Kuroda
amma bata yarda ta kwana, yadda kake tunanin mu muka batar da su, to akan me? Daga
zaman amana???”
Malam Isa ya lallashi Tafada yace, “kada ki damu ba kya ganin a fusace yake? Ina ne gidan
makwabcin nasu?” Ta nuna gidan dake jikin na Innar.
Aka yiwa makwabcin su Inna sallama ta hanyar tura yaro cikin gidan sai gashi ya fito, suka
gaggaisa da Malam Isa yace “Tafada ya akayi? Tace ga masu neman makociyarka nan, har
suna neman kala mana sharri wai mun batar da ita”. Malam Sani Albasu yayi dariya yace,
“Innar Hauwa mai jama’a, ho! Tana can kauyen mu gidan Malam Bagobiri mai maganin
gargajiya na Albasu, in kuka je Albasu duk wanda kuka tambaya gidan Malam Bagobiri ya sani,
ko daga tashar Albasu ne kukayi tambaya za’a kai ku har gidan sa”.
Sarham yace “me zai hana ka daure ka rakamu kawai, ina ganin zaifi sauki, tunda kai ka kai
ta?
Malam Sanin ya yarda zai rakasu har Albasu, Amma yace saidai su dawo gobe yanzu
yamma tayi.
Sarham, Wanda hakurin sa ya tuke a lokacin sai yace da Malam Isa su je kawai su yi
tambayar har su samu gidan. Malam Isa ya yarda don yaga damuwar sa karara, ya yarda cewa
wannan bawan Allah Sarham, da gaske ya damu da Innar Hauwa Allah kadai ya san tsakanin
su. Musamman filin gidan su da ya saye dinnan ya hau ginewa, duk da bai yi masa wani bayani
ba ya fahimci yana da niyyar sake mayar musu da gidan su ne. Wanda baya ko tantama
kulafucin ta da gidan, da unguwar bakidaya, da mutanen ta na arziki da aka raba ta dasu rana
daya, sannan da makancewar tilon diyar ta rana daya, da kuma damuwar batan mijin ta Malam
Bilyaminu dare daya, su suka taru suka haifar mata da kamuwa da ciwon zuciyar da ake cewa
tana fama da shi a yanzu.
Malam Isa ya tuna Innar Hauwa yanzu mijin ta ya fi Shekara biyar da bata, me zai hana ta
yarda tayi GAIBA in ya so shi ya aure ta ya rike mata 'yar ta guda daya ya killace su a gidan sa
su daina rayuwar sayarda abinci a Tasha?
Shi kadai yake wannan tunanin na babu gaira babu dalili har suka isa Albasu.
Malam Isa ya tafi tunani bai san har sun shiga garin Albasu ba, sai da Sarham yayi
masa magana yace “gamu cikin Albasu” suka tsayar da motar a gefen titi Malam Isa ya tambayi
wani mai Amalanke ko ina ne gidan Malam Bagobiri mai maganin gargajiya?”
Mai Amalanke yace “kun baro gida can farkon shigowa gari, ku koma da baya ku tambaya”
Sarham yace “in dai ka san gidan shigo ka kai mu, zan baka kudin Babur ka dawo”.
Hakan kuwa aka yi, mai amalanke ya shiga bayan motar yana nuna musu hanya har kofar
gidan malamin.
Wato abun babu kyawun gani, Yaa Subhanallah! Marassa lafiya ne rututu a zube a kasa
tun daga zaure, cutututuka iri daban daban masu tasa tsigar jiki. Sarham sai da ya dauke
numfashin sa na lokaci mai tsaho sabida kazantar gidan da cunkoson marassa lafiya. Tausayi
da haushin Inna ya kama shi, wato har yanzu tana nan da halin ta na rashin yarda da asibiti
kamar bai isa ace ta dau darasi tun akan Hauwa ba?
Ganin cewa jinin sa na neman hawa, sai ya umarci Malam Isa ya yi musu sallama da
malamin, aka ce ai sai sun hau dogon layin ganin sa yanzu kuma dare yayi, saidai su dawo
gobe da safe.
Malam Isa yace da Tafada “shiga kawai ki fito mana dasu, ya gansu hankalinsa ya
kwanta, don ni kam ban iya kwana garin nan”.
Tafada ta shiga gidan da sallama, wani ikon Allah da Hauwa ta fara tozali, wadda ke
bakin kofar dakin da Inna ke kwance, Hauwan kuma nan da nan ta dauki muryar ta, ta kira
sunan ta da ‘yar dusassar murya.
“Tafada, kamar muryar Tafada nake ji”.
Tafada ta isa ga Hauwa da sauri, wadda tayi kozai kozai tayi zuru-zuru, rabon ta da wanka
yau kwana bakwai, wato tun kawo su da Malam Sani yayi kauyen nan ya tafi, ya kuma karbe
duk ‘yan kudaden hannun su da sunan yana biyan mai magani, amma kullum jiya I yau, babu
wani sauki a tare da Inna sai na Allah. Yau kam wuni tayi tana suma babu wanda ya tsaya a
kanta sai Hauwar da ba gani take ba, itama an gaya mata dai uwarta na suma.
Don haka yau Hauwa ta wuni kuka wurjanjan har ta gode Allah, idan ta rasa Inna, bata san
yaya zata cigaba da rayuwa ba.
Tafada ta gaisa da mutanen data gani a zazzaune kafin ta kama Hauwa ta ce “nice
Tafada, ina Innar taki wani ke ta son ganin ta tun daga Kano ya sako mu a gaba saida muka
kawo shi nan, kamar dai dan uwanku ne”. Babu wanda ya zo wa Hauwa a rai da zai biyo bayan
su har nan, cikin ‘yan uwan su duka sai Yaya Jamilu! Watakila yayi ta tambaya ne a kansu har
ya gano inda suke.
Tafada tayi mata jagora suka fito, a yadda Hauwa ta lalace ba don yayi mata farin sani
ba da bazai gane ita ce ba, sabida yadda tayi baki ta kuma rame, Sarham ya runtse idon sa
cikin tausayi marar misali, muryarsa na shakewa da sarkewa yace.
“MAI-JID-DAH!”.
Sai tayi sak! Da rai da kwakwalwarta cikin son tuno inda ta san sassanyar muryar, da kuma
inda ta taba jin an kira ta da wannan kebantaccen sunan. Duk fadin duniya mutum daya ne ya
taba kiran ta da “Maijiddah”, ya kuma ce sunan nashi ne shi kadai, bai yarda kowa ya
kwaikwaya ya kira ta da shi ba wato LIKITA SARHAM!!! Hauwa-Kulu ta yi shiru na wucin gadi, kwakwalwarta na faman processing tattausar muryar
data kira sunanta. Muryar Likita Sarham ce tabbas, wadda ko mutuwa tayi ta dawo bazata
manta ‘accent’ dinta ba. Wani kwayan mutum guda daya da komai nisan shekaru bazata taba
mantawa da shi ba, saboda kyakkyawar rawar da ya taka cikin rayuwar ta da gudunmuwar da
ya basu, a lokacin da rayuwarta gabadaya ta dauko nakashewa. Duk da a cewar Hauwa, shi
Sarham din shi ya karasa mata idanu, wato shi ya karasa makantata, amma bayan faruwar
hakan ya kyautatawa rayuwar su, ya kuma taimaka ya hana rayuwar ta karasa rugujewa, ya
karfafa mata da cewa kada ta bari ta durkushe a dalilin makanta.
Rawar da Dr. Sarham Abbas Shanono ya taka cikin rayuwar su, duk da cewa ta dan
lokaci ce, to fa hakika mai girma da muhimmanci ce domin ya nuna musu kauna da mutunci na
masu ilmi. Da wuya ka samu mutum irin sa a wannan zamanin da yake yiwa talakawa da yafi
matsayi da ajin rayuwa kamar su daukar mutane. Balle don wani tsautsayi ya faru a dalilin
aikinsu su tsaya su yi waiwaye a kai. Ta tabbata da ace bai tafi inda ya tafi ba, da ba’a kawo
wannan matakin ba a lafiyar Inna, da karatun ta, da komai ma na rayuwar su, ta tabbata zai
cigaba ne da tsayawa rayuwar su kamar Baba da Zulkiflu na raye. Da bazai bari Zakari ya
tozarta rayuwar su ba ya raba su da farin cikin su.
Bata yi masa farin sani ba, saboda ko sanda yake tare da su kullace take da shi, bata tsaya
ta saki jiki dashi ba, balle ta saba da shi, ko tayi masa kyakkyawan sani, amma ko daga sanin
nesa nesa din data yi masa a gidan su ta shaida cewa shi din mutumin kirki ne, mai taimako ne,
mai yawan alkhairi ne, ya san (human dignity), kuma yana matukar kaunar su sosai. Sai hawaye ya soma zubo mata, don ji tayi ma kamar BABANTA MALAM BILYAMINU YA
DAWO! Tamkar wani ‘SAVIOUR’ (mai ceto) ya iso cikin rayuwar su, koko tace kamar wani
Mala’ikan rahma ya riske su, a lokacin da Inna ke kan gargarar mutuwa cikin rashin gata, kuma
a lokacin data fidda rai da tashin Inna. A can cikin kunne da kwakwalwarta, Hauwa ta tsinkayi muryar nan ta Dr. Sarham mai
sanyi da gardi tana tsokanarta, zolaya irin wadda baya rabo da ita, kuma ya saba yi mata don
ya samu ta kula shi. Aka ce a bar hali a ci me? Dr. Sarham har yanzu yana nan da (jovial
personality) din sa. Hausawa suka ce in ka shekara baka ga mutum ba, ranar da kuka hadu,
tambaye shi wani abun daban amma banda halin sa.
Wato a nufin bahaushe halin mutum baya taba canzawa sai dai ko mu ce Sarham ya rage
wasu daga cikin halayen sa na sakin fuska, da yawan magana, a dalilin girma da nauyin iyali da
yanzu ya hau kan sa.
“A yi magana ki ce an yi miki “GORIN IDO”, dubi kwala-kwalan idanun nata a jike jagab,
jawur dasu, kamar kosan da ya soyu a cikin mai don kuka, maimakon ta saki far’a tace
“Jabbama-jabbama…lale-maraba da bakon KANO. Ko tace YAYA SARHAM SANNU DA
ZUWA”. A’ah ta tsaya tana mana ambaliyar hawaye, watakila anan garin nasu na Albasu, da haka
ake saukar bako”.
Sarham ya fada cikin zolayar Hauwa-Kulu, don rabata da hawayen dake ta satatar mata, da
kokarin sa na hadiye nasa hawayen. Ba kankanin abu ke sa shi kuka ba, amma a yau ya san in
bai yi da gaske ba ‘he cannot control his tears’ a gaban Hauwa, abinda bazai so hakan ba ko
kadan. Kokarin gaske yayi da ya iya hadiye hawayen sa a kan idon Hauwa, wadda yake ma
kallon kanwa ta jini, kamar Sumayyah, yadda ba zai iya bari Sumayyah ta ga raunin sa ba, haka
ba zai bari Hauwa ta gani ba, ba don haka ba da tuni ya sake su sun shatato shima akan
kundukukinsa, kamar yadda Hauwan ke faman yin nata, amma fa ita nata na farin ciki ne.
Ganin yanayin wahala da rashin lafiya da ya same su ciki kuma a kauye ya karya zuciyar sa,
wanda ba cikin sa ya tafi ya barsu ba.
Cikin muryar kuka Hauwa ta ja sheshsheka ta ce “Likita sannu da zuwa”, tana mai yi ma
saitin da muryarsa ke fitowa kallon ga ZULKIFLU YA DAWO.
Sarham ya matso gaban ta har tana iya shako kamshin hamshakin turaren sa na ‘Oud
Abyad’ ya ce “to ko ke fa Maijiddah! Amma kawai daga ganin mutane sai ki balle da bokitin
hawaye? Ai sai su Malam Isa da Tafada su dauka baki yi maraba da zuwa na ba sam”.
Tayi murmmushi, har kuncinta ya lotsa ciki sosai, wani abu da ke kara ma Hauwa’u
kyau, yace “maza je ki kwaso kayan ku, Inna Tafada taimaka min ki dauko Inna don Allah a sa
min ita a bayan mota, in yi maza in kaita asibiti, a kula min da ita da kyau”. A yau yana dakacen
inama shi ba likitan ido bane, na zuciya ne! So that ya iya duba Innarsa da kansa”. Hawayen dadi ya sake kecewa Hauwa, don ita ai tayi-tayi Inna ta yarda ta zauna a
asibitin Murtala a cigaba da dubata ta ki, tace in mutuwa ce ta isko ta, a barta ta mutu a cikin
dakin ta yafi mata, ta fi so ta mutu a gida akan gadon asibiti, kada taje a kai gawarta mutuware
a ajiye a firinji, a kuma jinkirta yi mata janaza. Kuma ita har gobe bata yarda da maganin asibiti ba, don bata ga ranar da ya yiwa idanun
Kulu ba, aikin Kulu yasa ta kara nesanta kanta da asibiti, dama dole ce ta kaita a kan Hauwa
dinma, shi yasa tunda ta fara ciwon nan suke dambarwa ita da Hauwa akan zuwa asibiti, daga
bisani Hauwa ta dauko shatar mota tace mata zasu je asibitin Kuroda a bata magani kadai su
dawo, da suka je asibitin, kallo daya likita yayi mata yace kwanciya zasu bata.
Hauwa bata ankara ba sai ji tayi Inna ta tashi tsaye tace ta tashi su tafi, data tsaya yi mata
magiya da gardama kan ta tsaya sai Inna ta kamo hanya abinta, ta kyale Hauwa a tebirin likita,
dole Hauwa ta taso ta biyo bayan ta tana kira. Tausayi yasa ta dakata ta kama hannun ta, a
lokacin suka taho gida. Hauwa bata daddara ba, washegari tayi ta rokon ta kan su je asibitin Murtala, ta tabbatar
mata su bazasu kwantar da ita ba, da kyar da nacin kukan Hauwa Inna ta yarda suka je
Murtala, nan suka hau layi har suka samu ganin likita, anan ne likita ya yiwa Hauwa bayanin
dole Inna ta kwanta