Showing 6001 words to 9000 words out of 46557 words

Chapter 3 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf

na
bukatar rayuwa, balle yanzu da ya san ko yaya ta zama babbar likita tana aikin kanta kuma
kallo daya zaka yi mata ka san hankalin ta a kwance yake, tana neman cika shekaru talatin.
Abinda bai sani ba shine tana da aure ko bata da shi?
Wannan tunanin, da kuma sanin halin mahaifinta da yayi, su suka sa yayi maza ya shiga
taitayinsa, ya soma yaki da fade memories masu neman dawowa muhallinsu saboda ganinta.
Sosai ya kama kan sa, bai bari ma ta san ya gan ta ba har bayan sati guda da ganin da yayi
matan. Amma wani coincidence din, ashe ajin su daya a wannan karon ma, itama ta zo yin irin kwas
din da yazo yi, duk a specialization nasu na ‘ophthalmology’. Bayan kwashe shekaru biyu tana
practicing aiki a Dr. Siddiqah Hospital anan Jeddah.
Ranar da yi mata gani na biyu da yamma ne, ya je shan Gahwah (coffee) a wani Mud’am
dake cikin asibitin koyarwar nasu na Sarki Abdulazeez, bayan ya gama sha, ya tashi ya nufi
kantar biyan kudi, ya zaro khamsoona riyals dinsa daga aljihu zai biya, kawai ya ji cashier din ya
ce ai an biya kudin gahwar da ya sha. Ya juya cikin tsanaki da mamaki, nan yayi ido hudu da Madinah Attahiru, his ex Madinah
Sorondinki, tana masa kallon ashe kana duniya?
Zuciyar sa ta harba. Makwallaton wuyan sa ya motsa, amma ya kasa hadiyar miyau.
Donhaka wani abu ya tokare a wuyansa. Madinah muguwa ce ta karshe ya sani in dai akan
soyayyah ne, idan ta samu dama zata iya kisa, har lahira kuwa, don haka nisa da ita shi ya fi wa
bawa kamarsa kwanciyar hankali. Juyawa Dr. Sarham yayi cikin daure fuska kamar bai san ta ba, ya soma takawa don barin
mud’am (restaurant) din gabadaya.
Madinah ta saki malalacin murmushinta, ta riga ta san halin kayanta bashi da jarumta in dai a
kanta ne, tanada yaqinin bazata sha wuya ba wajen dawo da shi ruwa tsundum cikin soyayyah.
Ba da sanin sa ba Madinah har sujjadah ta fadi ta yi a nan inda take zaune, (for the second
phase) na rayuwarta ta sake haduwa da Sarham Shanono, a muhallin da ta fara haduwa da shi
a can baya.
Ta tako cikin kasaitar ta har inda yake tsaye yana shirin barin wurin shan coffee din, ba tare
da ko an gode yace ba, daga abinda aka biya masa. Madinah ta sha gaban sa, ta kashe shi da
murmushin nan nata kamar na koren furen fulawa, da ya dade da daina gani, zuciyar sa kuma
bata bar mararin ganin murmushin ba all those years, Madinah ta ce, “ai in da alkawari zai zamanto cewa ko gaisuwar musulunci ce akwai a tsakanin mu Dr.
Sarham, idan ta SO da KAUNA ta gushe ko tayi fading, a matsayin mu na dalibai duka, sannan
‘yan kasa daya kuma ‘yan aji guda, dana tabbatar abinda nazo yi shi ka zo yi, ba laifi bane don
hanya ta hada mu mun tsaya mun yi gaisuwar musulunci”. Wannan karon ma bai yi niyyar bata amsa ba yasa kai zai wuce abinsa, a ran sa yana fadin
“Allah ya shiga tsakanina da ke Madinah!
Mumini na kwarai sau daya maciji yake saran sa a rami guda”. Amma sai Madinah bata yi
fushi ba, ta sake shan gaban sa. Ta ce,
“Assalamu alaykum warahmatullah wa barakatuhu!”

Kamar yadda ta dade da sani, Sarham Abbas nada wani hali daga halaye masu kyau, wato
baya iya maida gaisuwar musulunci a kwandon shara, ta hanyar kin amsata, wato duk inda ya ji
ta sai ya amsa koda ba da shi ake ba, ba don komai ba sai don cika sunnar Manzo SAW.
To yau ma hakan ce ta faru kuma yanzun ma. Sarham ya kasa kin amsawa don cika umarnin
addinin musulunci, sai ya ce kasa-kasa kamar yaci madaci,
“wa alaykumus salam warahmatullah wa barakatuhu”.
Daga wannan sai aka shiga kallon-kallo, koko in ce ‘kallon kuda’ kallon debe shakku ko debe
tsammanin gizo ido ke yi, kallo ake babu ko kiftawa haka babu kakkautawa tsakanin SARHAM
DA MADINAH. Suka yi wa juna kiriii da ido.
Kallon da ya dawo masa da duk abinda ya faru cikin shekarun soyayyar kurciyar su kan idon
sa, koko ince, kan idon kowannen su, komai da ya gabata (in the past) ya zo yana gilmawa a
idanun kowannen su, tamkar yadda sinasinai ke wulgawa a majigi, suna tariyo kan su, suka
kuma shiga warware tsohon kullin dake zuciyar Sarham akan Madina, tamkar ana tariyo tsohon
kaset na faifan bidiyo.
A hakikanin gaskiya Sarham na kullace da Madinah kullata mai yawa, wadda ta janyo ya
maida kansa ba namiji ba, ta hanyar daina sha’awar soyayya da sha’anin mata gabadayansu.
Madinah tasa ya hada su itada sauran matan duniya yayi musu kudin goro da cewa
dukkansu maciya amanar kauna ne, kuma basu san darajar soyayya ba, mata irin Madinah in
ka bari ka fada komarsu zasu iya kashe ka har lahira akan soyayya.
Yana tuhumarta ne da rashin alkawari da cin amanar kaunar da suka yi wa juna.
Son data ke ikirarin tana yi masa yayi ittifakin ko kusa bai kai rabin nasa ba, shiyasa ta iya
bari har aka raba su cikin matukar sauki haka, kamar kwace goriba a hannun kuturu.
Abu daya ya sani kuma yake da tabbacin sa; Madinah Attahiru, bata taba raina shi ba, wai
don shekaru biyu ko uku kawai ya bata a haife, Madinah bata taba raina arzikin mahaifin sa ba,
wai don bai tara dukiya kamar nata mahaifin ba, baya ga kasancewar sa malamin
makaranta/malamin jami’a. Yana son Madinah har gobe, domin ta hada duk wasu halaye na kwarai da nagarta da
kyawun sura dake sawa a so mace, a yi mata So na musamman. Duk wasu ‘attributes’ da yake
so a matar aurensa Madinah ce ta hadasu ita kadai ranta.
Ya ci buri mai yawa a kan Madinah Attahiru, haka ya sha wahala lokacin da ya rasa ta farat
daya. Haduwar su ba zato a yanzu, karo na biyu cikin shekarun girmansu, a lokacin da suke da
cikakken hankalin su bata nufin komai sai fami a kan gyambon da riga ya warke.
Kafin wannan lokacin sun yi alkawarirrika masu dimbin yawa shi da ita, kai har yawan adadin
‘ya’yan da suke burin haifa ra’ayin su ya zo daya, wato ba masu yawa ba, shi da Madinah
kamar Lailah da Majnoun ne. Daga cikin manyan alkawuran su na can baya, har da na yin aure
daga zarar sun kammala MBBS, koda basu samu ayyukan yi ba a Jeddah, sun ajiye a ransu
zasu yi ko ayyukan philanthropy ne a private clinics na Jeddah don rufa asirin juna indai zasu
rayu tare.
Rana daya Madinah bai san ya aka yi ba, bai san me ya faru ba Madinah ta yarda mahaifin ta
ya ci zarafin sa, ya kuma canza mata makaranta, duk dai don ya raba su, ya rasa mai yasa
Baban Madinah ya ki jinin sa ya kuma raina arzikin su shida iyayensa har haka, tunda daidai
gwargwado iyayensa nada abin yin su, da rufin asirin su basa nema a hannun kowa, ko da yake
ya taba gaya masa fuska da fuska;

“me na sama ya ci bare ya baiwa na kasa? Kuma yayi yarinta da auren ‘yarsa a lokacin”
Shine kawai hujjarsa.
Babban laifin da Madinah ta yi masa shine, bayan an canza mata makarantar, bai kara ji
daga gareta ba, Madinah bata kara waiwayarsa ba, bata kara neman sa ba, koda da gaisuwar
zumunci ne. Ai yasan Madinah nada email adireshinsa, da adireshin sa na gidan wasika, da
lambar talfon din gidan su, amma ko sau daya, bata taba tunanin gwada neman sa ba, wanda
ke nufin ta datse duk wata alaqar soyayya da sanayya dake tsakanin su.
Koda ba don maganar alkawarin aurensu ba, ai ta nemi inda yake ta ji yana raye ko ya zarce
ta dalilin kisan gillar soyayar da suka taru suka yi masa itada mahaifin ta, tunda dai ta kwana da
sanin irin son da yake mata, ba irin wanda zai gushe farad daya bane.
Wannan shine babban laifin da Madina tayi masa da ba zai yafe shi ba wato kin neman sa
ko sau daya cikin shekaru bakwai da rabuwarsu, tun bayan komawar ta Yamboa inda a can tayi
nata consultancy din, tsayin shekaru biyar, da komawar sa shima zuwa gida Najeriya na dan
wani lokaci, inda daga baya ya dawo shima yayi consultancy dinsa ya sake komawa gida. Wanda ya yi shi ne da kyar da sudin ludayi shikadai a [KAU] a dalilin rashin Madinah tare da
shi.
Saboda tunda suka fara MBBS suke tare, har zuwa karshen sa. Karatun dukkansa, da aikin
gida (assignment) da halartar lacca duk tare suke yin komai. A lokutan jarrabawa kuwa duk
zaka same su tare a library, sun dukufa basa komai sai fatan isa ga ‘goal’ din rayuwarsu. Don
haka shekaru goma kenan ya kwashe a cikin hidimar dakon son Madinah Sorondinki, idan har
lissafin sa daidai ne; yayi shekaru biyar tare da ita cikin fafutukar hada MBBS, shekaru biyar
kuma cikin jinyar soyayyar ta, lokacin da yake consultancy, tun bai san so ba akan Madina ya
koye shi, wato tun farkon tashen balagar sa da soyayyar Madinah ya budi idanu.

Wannan shine tarihin soyayyar su shi da Madinah wanda ya tuna a wannan ‘yan dakikan da
suke kallon debe tsammani shi da ita.
**** **** ****

Da tunanin sa ya zo nan, sai ya dauke kai daga kallon kudar da suke yi wa juna, ya juya da
zummar cigaba da tafiya ya bar ta a wurin, ba tare da ya kara tankawa ba.
Madinah bata yi fushi ba, ta hakurkurtar da ranta da cewa fushin fari ba nata bane, Allah na
nufin su da wani al’aamri maigirma da ya sake hada su (at appropriate time), ta sake biyo bayan
sa jiki babu karsashi, yana saka kafa tana mayas da tata duk inda ya cire tasa, cewa tayi cikin
muryar dake raurawa. “Sarham, yaya bayan rabo?”
Cikin dakiya da tsare gida yace “bayan rabo kuma? Sai tarin alkhairi” “Kamar baka gane ni
ba?” Madina ta fada kamar zata fashe da kuka wannan karon, idanun ta na kallon kasa, sun
kasa rike hawayen yanzu, suna cigaba da tafiya zuwa dakin karatu, hawaye na tsirgo mata.
Sarham yace. “Madinah kenan, ni kuwa na gane ki, ko ba Madinah Attahiru diyar masu Bankin Musulunci
na Duniya bace? Idan na gane ki sai me hakan zai kare ni da shi, ni Sarham dan yaku-bayi?”
Madinah tana hawaye tace “zaka iya fadin komai a kaina ba tare da na ga laifin ka ba
Sarhm, laifi kan laifi na san na yi maka amma ina da DALILI na.

Abu daya nake so ka gane yanzu, Daddyna daka sani a da can, to bashi bane yanzu.
Wannan sabon Attahiru SoronDinki ne, wanda duniya ta biyar dashi, yanzu ya gane cewa
rayuwar kanta da dan adam kansa komai mukami da mulkin sa, da dukiyar da yake tinkaho
duka ba a bakin komai suke ba. ​ To cut it short, Daddyna ya dade yana neman ka ido rufe domin ya nemi afuwar ka, ya
kuma baka damar da ya dade yana hana ka”.
Murmushin da Dr. Sarham Shanono yayi irin wanda yafi kama da a kira,
“na dade da baiwa wannan tatsuniyar baya” ne.
A fili kuma yace “Madinah Soron Dinki, takamaimai me kike so da ni yanzu a takaice, da yasa
kike min wannan binbinin haka?”
Ai jin haka Madinah ta tabbatar yanzu kam Sarham ya gama da babin ta, yau ita Sarham ke
cewa tana masa binbini! Wannan ba Sarham din data sani a baya bane halinsa duk ya canza,
wancan jovial ne mai saukin kai da dadin sha’ani, ko dai wani ne mai tsananin kama da shi da
irin sautin sa ta gamu da shi saboda yadda ta saka shi a ranta??? Sai kawai Madinah ta durkushe anan inda take tsaye, cikin korran grass carpet (ciyayi) ta
saki kuka mai cin rai.

A can zamanin baya Sarham ba abinda ke daga masa hankali irin damuwar Madinah
Attahiru, amma wallahi yanzu bai ji ko gezau ba wai an tsikari kakkausa, ya yi kuka har fiye da
wannan da take yi yau akan rashin Madinah, da kuma wulakancin da mahaifin ta yayi masa
ranar da yace “ba zai taba baiwa dan almajirin gwamnati (dan malamin makaranta) ‘yar sa ba”. Ita nata kukan kuwa a yanzu ai na jin dadi ne, abinda bai sani ba, kukan Madina yau ya
kunshi abubuwa masu dimbin yawa, har da wadanda tunanin sa da tsinkayen sa bai bashi ba.
Bata taba daina son sa ba, a duka wadannan shekarun daidai da rana daya, ta yanke alaqar
su ne domin ta samu damar yin biyayya ga mahaifin ta, wanda ba abinda bai yi mata a duniya
ba, ya kuma fifita soyayyar ta akan ta ‘yan uwanta maza bakidaya kasancewar ita kenan masa
diya mace, kuma auta a cikin ‘yan maza bakwai. Wannan shine dalilin nata. ​ Sarham bai tsaya Madinah ta gama kukan bay a cika bujensa da iska ya bar wurin, sai
dagowa tayi bayan ta share hawaye ta neme shi a filin wajen ta rasa.
​ A lokacin ta cigaba da tuno rayuwarta ta baya tare da Sarham, abinda ya faru shekaru
bakwai da suka gabata, ta tuno asalin ta, haduwar su, lokutan su tare a campus, da abubuwan
da suka faru da ita bayan rabuwar tasu…….
**** ***** ****


WAIWAYE ADON TAFIYA! (2)
DR. MADINAH ATTAHIRU
A
salin mahaifin ta Bakano ne dan asalin Soron Dinki, Soron Dinki wata karamar unguwa ce mai
tsohon tarihi a jihar Kano, wadda ta haifi fitattun malamai da alkalai a tarihin jihar. Tana nan dab
da gidan Sarki (Emir’s Palace).
Mahaifin Attahiru wato Kakan su Madina tsohon Alkalin Alkalai ne na jihar Kano kuma
fitaccen mutum akan sha’anin shari’ah a Kano. Tun a tsakiyar shekarun 80’s Attahiru Habibu

Sorondinki ya tafi Jeddah kan wani kwas na aikin Banki, tare da matar sa Hajjah Ramlah da
manyan ‘ya’yan sa maza uku a lokacin, Abubakar da Omar, da Osman inda daga wancan
lokacin ya fara aiki da wani tsohon bankin kasar ta Saudi-Arabia.
Da tafiya tayi tafiya, zamani na garawa da shi a harkar aikin banki a can, har zuwa lokacin da
aka bude ISDB wato (Islamic Development Bank) Allah kuma ya zabe shi ya kai shi ISDB a
babbar ‘headquater’ din su dake birnin Jeddah. Ya rike kananan mukamai da dama a cikin ta,
kafin ya iso wannan matakin na yanzu. Domin kuwa a halin yanzu mahaifin na Madinah Alhaji
Dr. Attahiru Soron Dinki yana rike da matsayin (Chief Financial Officer) na ISDB. Alh. Attahiru
na auren Hajjah Ramlah, wadda ta kasance ‘cousin’ a gare shi, ta cika masa gida da kyawawan
‘ya’ya maza har su hudu, Abubakar, Omar, Osman da Aliyu, a Kano ta haifi manyan su uku,
wato Abubakar, Omar da Osman. Da suka zo Jeddah ba jimawa ta haifi Madinah da Aliyu anan.
Akwai ratar haihuwa sosai tsakaninta da Osman kafin su samu haihuwar auta “Madinah”.
Daga Abubakar har Umar har Aliyu da Usman ma’aikatan bankuna ne a kasar Saudi-Arabia,
saboda mahaifin su dake da wuka da nama a harkar aikin banki.
​ An haifi Madinah ne a garin Madinatul-Munawwarah lokacin sun je aikin omrah duk
gidan, shi yasa Baban ta ya kira ta da suna Madinah.
​ Madinah ta ga gata tun daga haihuwar ta har girman ta, Madinah bata taba sanin
wahala ko babu a rayuwar ta ba, ta tashi a gida na ilmi da tarin dukiya, wanda ya sa koda ta
shiga jami’a maza ke rububin ta, da yawa ko don su rabi alfarmar ISDB, da yawa kuma saboda
kyawun ta ne. Amma wani ikon Allah babu wanda tasu ta zo daya irin coursemate dinta Sarham Abbas
Shanono, wani siririn sardidin yaro, dan ajinsu, wanda ta fahimci yafi kowa a ajin su kokari,
kamun kai da kula da abinda ya kawo shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login