Showing 12001 words to 15000 words out of 46557 words

Chapter 5 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf

nan
zuwa (handsome man), son kowa, kin wadda ta san ba zata samu ba.
​ Madinah (couldn’t control her tears) wadanda (emotion na radadin soyayya) yayi
sanadin zubowar su, a lokacin da zai bar wurin ne ta bi bayanshi shine ya yi mata wannan
yarfawar. Shin meye laifin ta a duka wannan tsarin da Ubangiji ya yiwa rayuwar ta? Me tayi ma
Sarham da yayi zafin da gaisuwar musulunci ma sai da kyar zai amsata tsakaninsu? Ba mai bata wannan amsar sai SARHAM din. Ta sani bai dace ta bi shi har gidan sa ba, kai
baima dace ba mace kamar ta ta dinga bin namiji komai tinkahon sa yana yarfata irin haka,
balle ita Madinah Attahiru, da bayan aji har ajujuwa gare ta. Amma haka ta take PRIDE din
nata, da kafarta ta taka zuwa gidan da ta san acan yake da zama, bata da tabbacin har yanzu
acan din yake, ko kuma ya canza gida, amma dai tace bari ta fara duba can din ko zata dace.
Ubangiji da kan sa yace “SULHU ALKHAIRI NE!”

To gata ta zo neman sulhun abin kaunar ta yau da kafafunta, kamar yadda tasan tana cin
alfarmar sunan ta kullum a wurin sa, haka yau ma take da wannan kyakkyawan fatan, tana da
yaqinin wannan karon ma zata ci wannan alfarmar daga gareshi, wadda tafi ta koyaushe girma
a wurin sa, wato ya sauke fushinsa ya tsaya ya saurareta ko na minti biyu ne albarkacin
sunanta da yake girmamawa na MADINATUL MUNAWWARAH… Madinah garin Manzo,
Madinah mafaka ga dukkan musulmi, duk da tabbas ta san an bata masa, kuma laifi kan laifi ta
san ta yi masa. Ko tace sun taru sun yi masa itada Daddy dinta.
​ Ilai kuwa tana tura karamin gate din ta hange shi daga can saman bene, tsaye a jikin
balcony, ya harde hannayen sa a kirjin sa ya juya bayan sa daga kofar shigowa, don haka bai
ga shigowar ta ba, da alama yayi zurfi a cikin tunani.
Madinah tana tura kofar cikin sa’a ta taddata a bude, don haka kai tsaye ta sa kai, ta kuma
haura ta matattakalar benen ta cimmasa har inda yake.
​ Kamar cikin mafarki, kamar kuma irin gizon da ta saba yi masa cikin ido biyu, haka ya ga
Madinah Attahiru tsaye a gaban sa, (for the second phase) na rayuwar su. Tana sanye da
shudiyar abaya kirar Dubai da mayafin ta, ya sha mamakin biyoshin data yi, a irin sanin da yayi
mata wajen tsare mutuncin ta da tsare ajin ta, wato tun saninsa da ita… maintaining self-esteem
dinta yana sama da komai a gareta, a kuma irin yarfawar da yayi mata dazunnan.

Wadannan, dama wasu dalilan, su suka sa ya kasa wofintar da ita, ko bar mata wajen kamar
yadda yayi niyya da farko. Musamman ganin kyawawan idanun ta sun cika taf da kwallah, gab
suke da ballewa bisa sassalkan kundukukinta, tace cikin rishin kuka.

“Yau ma in ci albarkar garin MADINAH……Madinah garin Manzo, in ci albarkar kasancewa ta
MADINAH AL-MUNAWWARAH, mafaka ga kuncin dukkan musulmi, a lokacin da suka shiga
cikin matsin mushrikai, da abokan gaba, suke neman inda zasu samu tsaro da kwanciyar
hankali, Madinah ta zamo mafaka ga Manzonmu (SAW), don haka nake rokon albarkacin ta ka
saurare ni, ka bani mafaka daga kuncin zuciyar dana ke ciki a cikin kirjina”.
​ Bai ce komai ba, amma a fuskarsa wannan karon akwai sassauci, a idanun sa wannan
karon akwai rahma, kai har da wani boyayyen sirrin da baya so ta ankara da shi. Yace.
“Me zan saurara daga gareki Madinah? Kada ki manta ni Sarham ba kowa bane, ba kuma
dan kowa ba, dan Malaman makaranta ne, wadanda basu aje ba, basu kuma ba wani ajiya ba,”
Madinah ta runtse ido kalamansa na mata zafi, tace “ka saurare ni ko na minti biyar ne, in
labarta maka duk abubuwan da suka faru dani a lokacin”. Sarham yace “abu daya zan saurara
daga bakin ki shine, meye DALILIN KI na kin nema na duk tsayin wannnan lokacin?”
Madinah ta ce “ban da dalili, bani da hujjar kare kaina” “then why are you here?” Tace
“saboda in baka hakuri, in kuma kai ka gaban Daddyn nawa, don ya dade yana neman ka, ya
gana da kai”. Sarham yace “ai in baki sani ba, duk wani mumini sau daya maciji yake saran sa a
rami guda bisa kuskure ko kaddara, amma sara na biyu, saidai idan shi ya kai kansa da kansa”. Madinah ta ce “duk da haka Sarham, na kuma yarda da kai. Wancan lokacin haka nazo na
daukeka na kaika gabansa ba tare da sanin zai ci mutuncin ka da zarafinka ba, to yau ma
hakan, at the same time, wannan lokacin ma ban san meyasa yake neman naka ba. But do me
this favour, ko da itace alfarma ta karshe da zaka yi min a rayuwarka!”. Daga wannan Dr. Sarham bai san meyasa bai kara musawa ba, ya samu kansa da bin bayan
Madinah zuwa motar ta tamkar rakumi da akala.
**** **** ****

SULHU
S
un zauna shi da Daddyn Madinah a falon ganawa da bakin sa, Alhaji Attahiru yace “Sarhamu ba
wani abune dalilinta ba, wanda ya hanata nemanka all this while, face BIYAYYAR IYAYE, ina
fatan hujjarta wadda ta isa hujja a takaice, ta samu karbuwa a wurin ka, tunda kaima kana burin
naka ‘ya’yan watarana su yi maka biyayya irin wadda Madinah take yi min. Autata Madinah mai gudun zuciyar iyaye ce da son gamawa dasu lafiya, shiyasa bata daga
ido akan duk wani umarninmu zuwa gareta, ba don ta daina son ka bane taki neman ka, a duka
shekarun nan tana dakon soyayyar ka ne, ni da bata fadawa hakan ba amma nine shaidar
hakan, amma a haka na rufe ido nayi mata aure da wanda hankali na ya kwanta da shi. Wani irin dago kai Sarham yayi cikin slow motion, jin furucin Baban Madina na karshe, Alhajin
bai damu da reaction dinsa ba ya cigaba da bayani,
“kafin Allah ya nuna min ayar sa a kan ku, wato kafin in kai ta gidan mijin ya dauke abin sa, a
hanyar sa ta zuwa daukan ta zuwa gidan sa, ta sanadin hadarin jirgin sama.
Idan nace maka I was extremely shocked da mutuwar AVM as at that time, kaima ka san yayi
kadan ya bayyana dimuwar tawa.
Da albarka ta yau nake cewa idan har yanzu kana ra’ayin auren Madinah to kaje ka turomin
mahaifan ka su karba maka auren ta, bana bukatar komai sai sadaki”.

​ Duk da haka, duk da wannan ban hakurin da dattaku da Daddyn Madinah ya nuna a
yanzu, da cewa da yayi yayi nadamar abinda yayi masa, ya kuma ce baya bukatar komai na
auren Madinah daga gareshi sai sadaki, bai wanke zuciyarsa ba. Madinah ta sha matukar
wahala kafin Sarham ya sauko, wato kafin ta samu ta shawo kansa ya sakar mata fuska ma
kadai, domin wata ‘yar karamar zautuwa ce ta same shi akan maganar auren ta da marigayi
AVM.
Duk da maganar ta zo masa bagatatan, amma bai yi mamakin jin ta ba, sabida shi kansa ya
san Madinah ba matar bari bace ga maza ‘yan uwansa, ya kasa sake mata fuska in ya tuna wai
har aure aka daura mata, shi bai yarda bama wai bata je gidan mijin ba, watakila Daddynta ya
fada ne don ya rage masa zautuwa, amma dai ko yaya Madinah take Madinah ce a wurin sa, ya
sani ba zai iya daina son ta ba, ko da kuwa ‘ya’ya goma ta haifawa AVM din, yaki yarda sam ya
koma mata ‘jovial Sarhamun sa’, duk wani annuri ya kau daga kyakkyawar fuskarsa.
Rabuwar su ta wadannan shekarun da maganar daura mata aure da mahaifin ta ya sanar da
shi sun sa ya canza da yawa daga halayen sa data sani na sakin fuska dayawan walwala, ko
ace ita Madinah ta canza shi, ta mayar dashi tattaura, mai tsauri, kuma mai wuyar sha’ani. Duk
da haka yana nan a ‘jovial’ Sarham din sa, wato mai far’a da faram-faram da mutane amma
banda ga ita Madinah, sau tari sai yayi ra’ayi zata ga hasken hakoransa, ko inda wasu mutane
daban yake tare. Duk Madinah ta jure wannan punishment din da bata da laifi, ta san wuyarta
kawai su yi aure kawai komai zai zama labari.
Wani irin kishi ke cin ransa akan maganar auren Madinah da wanin sa, kuma taki su
magantu akai sam, da ya kawo zancen zata bata rai, ta ki tankawa. In ya takura da tambayarta
wani abu akan aurenta da AVM ko makamancin haka sai kawai ta saka masa kuka. Ko yaki ko
yaso dole ya bar zancen. Ba kamar can baya ba da kullum zaka tadda fararen hakoran sa (in yana gaban Madinah) a
warwaje, ya kasa rufesu, kamar na mai tallan makilin dinnan ‘colgate’.
Yanzu kam saidai ka ganshi bay abo ba kuma fallasa, fuskar ta koma kadaran-kadahan a
gaban Madinah. Itama dole yasa saida ta rage nata far’an gareshi, ayi mutum kamar mutanen
farko ba yafiya ba afuwa ba manta abinda ya shige? Aka koma kadaran-kadahan din ita da shi,
amma dai suna tare koyaushe a cikin asibiti ko a cikin campus, ko a gidansu a weekend, haka
suka kasance har zuwa ranar da Surayyah ta gaya masa ‘graduation’ din ta daga BUK.
A ranar ne kuma Daddy, wato Alhajin su Madinah ya tabbatar masa ya bashi auren Madinah
halak-malak, yaje ya zo masa da iyayen sa a tsayar da magana kawai.
​ Ko yaki ko yaso, hakika yaji farin cikin hakan maras misaltuwa akan wannan albishir din
na Alhajin kamar yanzu ya fara jinsa, komai pretending dinsa kuwa, musamman da Daddyn da
kansa ya kira shi a waya ya gaya masa da bakin sa da nasa, don haka ya ajiye maganar kishin
matacce a gefe, yana cewa da sannu zai rama ne. Madinah bazata ci sadakin maza biyu
abanza ba dole ta gane shima yanada ajinsa in ta shigo gidan sa, sai ta gaya masa ko sau
nawa AVM ya samu alfarmarta, kafin ya yarda su yi rayuwar farin ciki irin wadda ya dade da yi
musu tanadi.
Da wannan shawarar da yayi da zuciyarsa ya ajiye kishi a gefe ya koma na shirin tahowa
gida, domin ya kammala kwas din da ya kaishi Jeddah gabadaya, a ranar yayi booking, zai taso
a washegari, suka yi sallama da Madinah a asibitin Sarki AbdulAzeez, yau kam taga ‘yar
walwalar Sarham, domin da zai tafi har yake ce mata duk ta yi baki ta rame, ina dalili?

​ Madinah taji wani irin sanyi a ranta sai ga hawaye sun digo. Shi bai san yadda canza
matan da yayi completely da yadda yake treating dinta yanzu ne wai don ta auri wani kafin shi
bisa rubutacciyar kaddarar ta ya ramar da itan ba, ya kuma maida ita bakar ba?
A lokacin sai bata bashi amsa ba, maimakon hakan, sai ta mika masa kyakkyawan kwalin
dake sunke a hannun ta, mai dauke da kyawawan furanni da katon HAPPY BIRTHDAY card
mai zanen zuciya. Sai a lokacin Sarham ya saki dariya don shi ya manta ma wai yau ne ya cika
shekaru talatin da uku a duniya.
Tunda ya hawo jirgi yake tunani, Allah dai yasa Surayyah na kaiwa su Inna kudin da yake
aikowa ta account din ta da yace ta dinga baiwa Sumayyah tana kai musu, ta san gidan, don
sun taba zuwa tare, ya san dai Innar Hauwa jarumar uwa ce, cikin kowanne hali zata kula da
kanta, kuma zata kula da Hauwa-Kulunta, ba zata bari ta zama (drop out from school) ba. Dan abinda yake tura musu duk wata ya san zai ishe su cin abinci har wata ya zagayo, duk
da ya san Inna bazata zauna haka babu sana’a ba, Allah yasa Sumayyahn kuma tana jure kai
musu, kodayake Sumayyahn sa ba daga nan ba, wajen aikin zumunci da taya shi son duk
abinda yake so, balle wadannan bayin Allah data fahimci sun mamaye rabin zuciyar sa! ​ Jirgin su ya taso daga Jeddah a washegari bayan sun yi sallama emotionally shi da
Madinah a filin jirgi, yanata kissima abubuwa daban daban a ransa, wadanda zai je ya tarar a
Kano, akan dai Inna da Hauwa, da rayuwar da suka samu kan su a bayan babu shi. Sarham ya
sa a ransa ba zai koma Jeddah dauko matar sa Madinah ba wannnan karon sai ya mallakawa
Inna wayar tafi da gidan ka komai kankantar ta, don dai ya dinga jin lafiyar su kai tsaye, ba tare
da ya saka ‘third party’ a tsakanin su ba.

**** **** ****


T
axi din da Dr. Sarham ya dauko shata daga filin jirgi bata sauke shi a ko’ina ba sai a kofar gidan
su. Wanda ke cikin rukunin gidajen malamai na sabuwar jami’ar Bayero.
​ Surayyah ce ta fara hango shi daga tagar dakinta, daidai lokacin ta dage labule don
samun iska kasancewar ‘nepa’ sun yi mata halin su na dauke wuta tana tsaka da shaqar barcin
rana cikin A.C, wani hucin zafi ya tada ta, don haka ba shiri ta tashi ta dage labulen ta don ta
samu ‘natural’ iska ta shigo mata, wannan ne yasa duk gidan ita ta fara ganin sa yana fitowa
daga mota.
Banda ‘jini’ sunan sa ‘jini’ da Surayyah bazata gane Bhaiyan Sumayyah ba sam, ko ta ce
Yaya Doctor yadda take kiran sa ita, sabida girman da ya kara da irin canzawar da yayi a
shekaru ukun da ya kwashe a kasar Saudi-Arabia, ilhamarsa da cikar zati sun karu, sun ninku
akan wadanda ya bar gida dasu. Yayi haske kadan, fatar jikin sa ta yi ‘fresh’ kamar wanda ya
shiga injin wankin fata.
Karadin Surayyah shi ya tashi Sumayyah dake falo a gaban TV tana kallon diramar Hausa, ta
yo dakin nata a guje don ta dauka wani abu ne ya same ta, da karfi Surayyah tace, “Summy
Bhaiyan ki ne, Yaya Doctor ke shigowa”.
To amma me? Sai ta tuno wani abu, wanda yasa nan da nan ta nutsu, ta daina murnar

dawowar Bhaiya, gashi dai ya dawo ‘unexpected’, gashi ta masa babban laifi, tace cikin
damuwa.
“Summy na dauka ba yanzu zai dawo ba, na saka a raina kafin lokacin da zai dawo na hada
kudin nan na baki sakon nan na mutanen nan kin kai musu duka a dunkule”.
Sumayyah ta ce cikin mamaki “wane sako? Wadanne mutanen?” Cikin damuwar data fi ta
baya Surayyah ta ce. “Ki min afuwa Summy, ban taba gaya miki Yaya Doctor yana aiko kudi ta
account dina in baki ki dinga kaiwa mutanen nan nasa talakawa da ya likewa na kofar Na’isa
ba, ni wallahi na ma manta, sai yanzu dana ganshi na tuna”. Ta kara da cewa “Summy don girman Allah ki rufa min asiri in ya tambaye ki kice ina baki duk
wata kina kaiwa, in yaso zan dunkule duka abinda ke hannu na a yau in baki ki kai musu kafin
ya je gidan, wallahi cosmetics (kayan kwalliya) and other stuffs kawai nake karawa da su duk
wata, saboda Mama bata yarda ta saya min irin wadanda nake so.” Idon Sumayyah har rawa yake don bacin rai, da tsoro da mamakin abinda ‘yar uwarta ta
aikata, har ta fara hango irin hukuncin da Bhaiya zai mata, ta fara hango shi ya dauke Surayyah
da mari kodayae Bhaiya baya duka baya zagi, amma fa bai iya fushi bay a kuma kware da
(silent punishment), fatar bakinta ma rawa take yi, ta kasa murnar dawowar tasa ma don haushi
da mamakin Yayar ta Surayyah, da kyar Sumayyah tace,
“kin ci amana amma, Yaya Surayyah kin ci amanar Bhaiya, na rantse da Allah babu ruwa na,
count me out of your dirty game”.
Daga haka Sumayyah ta fice da gudu tana “Oyoyo! Bhaiya, Mama Bhaiya ya shammace
mu”. Sai ga Mama ta fito daga dakin ta itama kan ta ko kallabi babu, tace “really?” Surayyah
kuwa bayan gida ta shige ta boye kanta, jikin ta ba inda baya rawa.
Sumayyah ta kusa kai Sarham kasa sakamakon tsallen da tayi ta shako shi da sunan murna.
Haba! Sarham sai ya balle da fada blah! Blah! “Sumayyah meye haka? Baki san kin girma
bane? Ko an ce miki da da yanzu ma daya ne? Bana son irin wannan haukan welcome din, an
wuce wajen, kada ki kara”. Mama ta iso falon tana cewa “kai mai hali dai baya fasa halin sa, kai kuma daga zuwa sai
fada kamar tsiduhu? Shekara uku ba kwana uku ba basu saka ka a idon su ba, ba dole

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login