Showing 3001 words to 6000 words out of 46557 words

Chapter 2 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf

da kowa ba. In yaso ta hakura da ko me take samu a tashar don kare mutuncin Hauwa.
Don da yawa suna amfani da sabo da mutuncin dake tsakanin su da Innar ne, su soko mata
zancen suna son Hauwa, sabida kirkin Inna da yadda ta ke sakarwa kowanne kwastomanta
fuska yasa take da jama’a, yawanci matafiya da masu shigowa Kano ta tashar tasu da direbobi
dake cin abinci wajen ta. Ga ita Hauwar kam! Ai duk iya rashin kunyar mai zuwa cin abinci
teburin su, bai ma isa ya tunkare ta da wata magana wadda ba ta sayen abinci ba, don babu
fuska sam. Zata iya wuni bata yi koda murmushi ba. abinda Kawu Zakari yayi musu yayi mata
illah a zuciya sosai ya rage mata walwala. “Hauwa-Kulun–Majadun” kenan.
​ Duk da cewa bayan sun dawo tashar Kano-line sun kama gida a unguwa uku shima mai
daki biyu ne, amma sun fi ciniki sosai a tashar kuka, wani ko ba don Allah ba zai sayi abincin
Inna a tashar kuka saboda daukar hankalin sa da makauniyar ‘yar nan tata tayi, wadda ke taya
Innar ta aikin abincin da sayar da shi wa masu bukata da zarar ta dawo makaranta.

A wancan lokacin Hauwa ta gama isa aure har ta na neman wucewa don gab take da zana
jarrabawar fita sakandire wato SSCE, ta samu damar da ‘yammata da yawa a zamanin basu
samu ba, saboda da sun fara makarantar ake cire su ayi musu auren wuri, amma Inna bata
bada fuskar da wani zai zo mata da zancen son Hauwa ba kwata-kwata, itama Hauwan ba
fuska ko kadan. Don kullun Inna na gaya mata “da tun farko baki baiwa Jamilu fuskar zuwa inda
kike da sunan neman aure ba, da har yanzu muna zaune gidan mu cikin sutturah, rufin asiri da
kwanciyar hankali, da yanzu bamu zama masu sayar da abincin tasha ba”.
​ Sai Hauwa ta cuno baki gaba tace cikin kunkuni “to Inna Yaya jamilu ba dan uwana
bane? Duk kin bi kin tsani Yaya Jamilu, kamar shine Baba Zakari, ina laifin sa? Halinsa daban
na uban sa daban”.
Inna ta kama baki, ta bude shi ta mayar ta sake rufewa cikin al’ajabi, wai ta san soyayya, ta
ce “hakane, dan uwan ki ne, na jini ma kuwa, amma wallahi ki sani ko shi ya saura da namiji a
duniya, kema kika saura diya mace a duk fadin duniyar nan in dai ni SAFIYA ni na haife ki,
kuma ina raye, to baza ku yi aure ba, ke ko ina gargarar mutuwa zan bar wasiyya ga duk wanda
na samu cewa ba zuri’a ta babu ta Zakari”.
​ Hauwa aka kumburo baki sai ka ce zumbutu ta ce cikin wani sabon kunkunin “to ai ni
dama ban sa aka ba, in dai maganar aure ne Inna, kawai na san ba’a raba hanta da jini, Yaya
Jamilu dan uwana ne dana ke kauna tunda ba wani jini na da ya taba nuna min kauna bayan
shi, kogobe na kara ganin sa In sha Allahu zan kula shi, zan tsugunna har kasa in gaida shi don
bana manta alkhairin da yayi min, kuma bani da masoyi duk duniya bayan ke irin sa”.
Inna ta harzuka, yau akan Jamilu tana fade Hauwa na mayar mata? Tace “hantar taku sai in
ba’a saka mata soson karfe da farin omo da sabulun dan jangabo ba, tuni in taji karta jinin zai
rabu da ita koda zata kukkuje ta karce, wawuya kawai, mara kunyar wofi.
Ke na bi zumuncin naku da soyayyar taku da gudu na tattake su ba takalmi a kafata!”.
​ Hauwa sai ta kama dariya ta ce “tsakani da Allah Inna ban san ki da dorawa mutum laifin
da ba nasa ba, duk da haka Inna Allah ya huci zuciyar ki, ni ba bakuwar zafi bace a kan Yaya
Jamilu, ina ni ina wani aure alhalin ba ido?
Kawai ina son Yaya Jamilu a rai na, kasancewar duk cikin ‘ya’yan Baba Zakari wa ya taba
nuna min zumunci da kauna ta fisabilillahi idan bashi ba? Kiyi tunani Inna, ki rage kin Yaya
Jamilu, laifin Baban sa ne ya shafe shi, yasa kike ganin bakin sa. Shiyasa kome zai yi bazai
burge ki ba, tunda Baba Zakari ya riga ya shafa masa, amma ko kadan bashi da laifi”. ​ Haushi ya ishi Inna, tayi mata shiru ta rabu da ita ta kaiwa banza ajiyarta, don ta dade
da sanin in za’a kwana ana kushe Jamilu, to kuwa Hauwa bazata gaji da kwana a hanya tana
kare shi ba.

Rayuwa ta mikawa Hauwa da Innar ta cikin rufin asirin Allah a tashar Kano-Line, inda suke
gudanar da sana’ar su. Har gashi yau Hauwa sun fara zana jarrabawar WAEC wadda aka fi
sani da SSCE a wannan watan da muke ciki.
Wadda da zarar sun kammala ta, Hauwa tayi sallama da makarantar kwalejin ilmi na
musamman. Tunanin Hauwa kullum a yanzu shine, shin ko yaya rayuwa zata kasance mata
bayan kammala sakandire?
Tunda dai Innarta ta ce bazata taba yi mata aure kamar kowacce mace ba wanda shi tafi
bukata a wannan matakin? Ta sani ba don komai Inna take wannan kaffa-kaffan da ita ba, sai

don kare mata martaba da mutuncin ta, har ma da tattalin kwanciyar hankalin ta, Inna tana bata
kariya ne daga shiga matsalar gidan aure alhalin tana fama da wannan nakasar mai girma. Har
ila yau, Inna tana guje mata shiga jami’a ne domin bata kariya daga fadawa ga soyayyar duk
wani namiji da zata wahalar da ita a matsayin ta na karamar yarinya kuma mai raunin halitta na
nakasar idanu, wadda har yau bata kai ga cika shekaru ashirin da haihuwa ba.
A wannan gabar da Inna ta san aure ne kadai ya ragewa Hauwa-Kulu, kuma ta fahimci tana
ra’ayin yin sa da dan uwanta Jamilu ko bata furta ba, to bazata taba bari Hauwa ta kai kanta ga
kowacce matsala ba.
Da dukkan karfin ta zata kare Hauwa-Kulun ta daga duk wata soyayyar da bazata yi mata
amfani ba.
Inna tayi wa kanta alkawarin bazata bar Hauwa-Kulu taje jami’a ba, koda tana da ido kamar
kowa, balle kuma BABU! Bazata lamunci shigar Hauwa jami’a bane don kada a gurbata mata
tunani, ko kuma wani da yafi Jamilu iyawa ya hilace ta ya hure mata kunne, a karshe ya saka ta
a matsalar da bazata iya fiddata ba. Tana da yaqinin yadda Ubangiji Subhana ya nufe ta da yin ilmin sakandire ba tareda
dabararta ba, ya kuma tsara mata yin rayuwa cikin nakasa ba tare da ta tagayyara ko ta tozarta
a dalilin nakasar ba, (kamar yadda dan uwan mahaifinta ya so su wulakanta), sannan rashin
mahaifinta tare da ita duka bai sa sun kasa numfashi da motsi cikin kudurar sa cikin duniya ba,
ta tabbata shi din dai sarkin wannan kudura da iradar wato (Ubangiji Subhana) bai manta da it
aba, shi zai cigaba da tsara mata sauran rayuwarta ta can gaba, kamar yadda ya tsara ta baya
ta hanyar da bata taba tunani ko tsarawa kanta ba, tunda shi dai Ubangijin KOWA. In tace
KOWA tana nufin KOWA, har da ita HAUWA-KULU!
Abin nufi anan, daga mai lafiya har mai nakasa duka nasa ne. shi ya halicci abunda yadda
ya ga dama wato “Fa’alun lima Yureed ne”. Shi din, (Ubangijinmu), mai yawan hikima ne ga
rayuwar duka bayinSa.
Bai kuma halicci wani a mai nakasa wani a mai cikar lafiya don baya son dayan ba, ko don
ya kaskantar da shi cikin bil adama, ko don ya saka shi cikin bakin cikin rayuwa mara yankewa,
kamar yadda ya dade da fada mata ne;
“Nakasa ba komai bace face jarrabawar Imani ga wasu daidaikun bayin Allah - (LIKITA
SARHAM)”.

​ Idan haka ne kuwa zata tsaya tsayin daka wajen ganin cewa ta cinye wannan babbar
jarrabawa da DR. SARHAM ya kwadaitar da ita muhimmancin cinyeta da TAUHIDI da IKHLASI
(ta bakinsa), daga yau ta daina fito na fito da Innarta akan Yaya Jamilu, daga yau zata yi wa
mahaifiyarta biyayya irin wadda wani da bai taba yi wa Uwarsa ba (koda ya san abun da take so
din ba daidai bane), ita HAUWA_KULU zata yiwa Inna biyayya kan jiki kan karfi, akan duk
abinda take so da ita da rayuwar ta, musamman hakura da rayuwar aure domin tserar da
kwanciyar hankalin su.
Ta san Inna tana yi ne don amfanin ita Hauwan ba don nata amfanin ba.
Hauwa-Kulu ta cigaba da gayawa kanta daga yau ta cirewa ranta burin yin aure kamar
kowacce mace mai lafiyar yinsa, ta barwa Allah ikonsa a kanta, ta daina yarda zuciyarta na
kwadaita mata Yaya Jamilu, kai dama duk wani Da namiji bayan shi da zai biyo hanyarta, ta
yarda da nakasarta babban gibi ce da zata hanata jin dadin rayuwa ta wani bangaren, ta kuma

karbeta hannu bibbiyu, ta yarda nakasar ido bazata bata damar yin abinda ke kira “MARITAL
LIFE” da “MOTHERHOOD” ba, wadanda sune ginshikin rayuwar kowacce diya mace, kuma su
suka fi komai dadi da muhimmanci ga rayuwar kowanne dan adam.

**** **** ****
(A GIDAJEN MALAMAI NA SABUWAR JAMI’AR BAYERO).
G
idan Prof. Abbas Shanono ya kacame da hayaniya a tsakanin jama’ar gidan da kawayen
‘ya’yansu da jama’ar mahaifiyar su da aka gayyato domin taya Surayyah Shanono, murnar
kammala digirin ta na farko, bayan dawowar su daga filin ‘convocation’ na cikin jami’ar Bayero.
​ Anan cikin gida bayan kawayen Surayyah sun gama dabdalar su sun tafi, Mama ta hada
musu (get together party) su’I’su, domin kwarai tayi alfahari da sakamakon Surayyah, koda yake
abin kamar a jinin ‘ya’yan ta ne, in dai ta fannin karatun boko dana addini ne basu da na biyu.
‘Get together party’ din da Mama Mai Shari’ah Haj. Maimuna ta shirya na abu biyu ne; bayan
taya Surayyah murnar kammala karatunta da kyakkyawan sakamako (first class degree) ya
kuma kunshi sallama da auta Sumayyah, wadda ita kuma zata tafi Jeddah nan da kwana uku
domin fara nata karatun, can a jami’ar da Abba Prof. yayi mata alkawari tutuni, wato Sumayyah
zata tafi inda Bhaiyanta (SARHAM) yake itama a cikin satin nan da yardar Ubangiji.
Tsananin kaunar juna irin na wannan family, da yadda basa yin wani abu babu sanin dayan
su, yasa sun kasa cika farin cikin ranar yau ba tare da shi ba, musamman da ya kasance a
lokacin wayar zamani ta tafi da gidan ka ta fara yawa a Najeriya (amma dai ba a kowanne gida
ba), to shima dai Abba Prof. kamar sauran manyan ma’aikatan gwamnati a Kano ya mallaki
tasa, har yana arawa iyalin sa lokaci-lokaci su kira dan uwan su dake nesa su gaisa.
To yau ma hakan ce ta kasance. Sumayya ta ce “Abba ka kira mana Bhaiya ayi komai ‘live’ a
kunnen sa”. Abba yace “kin manta Sarhamu jarrabawa yake yi?”
Sumayyah ta hau roko “Abbah don Allah, ko na minti biyu ne, bazan ja shi da surutu ba”.
Surayyah kuma ta ce “Abbah ni zan biya ka kudin da zamu cinye maka a wayar”. Abba Prof.
yace “da can dana ke baku aron wayar kuyi wayar da shi biyana kuke yi?” Suka hada baki
wajen cewa “tuba muke Abbanmu! Abbanmu like no other Babanmu maganin kukan mu”. Prof. yayi dan murmushi kafin ya danna masa kira, ba jimawa Sarham ya amsa masa da
cikakkiyar amsa sallama, da muryarsa dusassa, wadda a kullum yanayinta kamar na mai fama
da mura. Sarham yace (cikin hausar shi wadda yanzu ta daina fita sosai yadda ya kamata).
“Daga bangarena ina kokarin kiran ku ne fa Abba, naka kiran ya shiga nawa shiga, in ban
manta ba yau ne graduation din ‘Surry Darling”.
Surayya ta saki dariyar farin-ciki jin yau wai Bhaiya ya kira ta da ‘Darling’ tana fadin “yau
kuma?” Shima daga nasa bangaren dariyar yayi, yace “Surry rigima, Surry masifa Surry
mathematician, Surry Darling!”. Duk falon aka kwashe da dariya da alama yau dukkansu cikin
nishadi suke, abinda basu sani ba ya fi su nishadin wannan ranar, domin tayi daidai da ranar
zagayowar haihuwar sa, kuma a daidai lokacin wani babban abun farin ciki ya same shi, wanda
daga shi sai Allah suka san shi, wato wani ‘gift’ ne na musamman na taya murnar zagayowar
ranar haihuwa Madinah ta kawo masa...
Don haka don yau ya kira abokiyar fadansa da ‘darling’ bai ji faduwa ba ko kankani, karewa
ma, har shirin fita ‘outing’ (picnic) na musamman ya yi niyyar shirya mata shima idan yazo, ko a

TIGA DAM ko a DAMBATTA DAM, inda suka saba zuwa don ‘celebrating’ wasu ranaku masu
muhimmanci da suka shafi dayan su.
Sannan kuma gashi yana shirin ‘surprising’ dinsu su duka, domin a lokacin ya riga ya yanki
tikitin tahowa gida kwatakwata, ba tare da ya gayawa kowannen su ba, tuni kuma yayi ‘booking’
din jirgin dare, bayan kwashe shekaru uku yana zullewa Mamansa Haj. maimuna, a kan dai
maganar aure. Yanzu kam da kwarin guiwar sa zai iso gida, kuma da abinda ya tabbatar zai baiwa kowa a
gidansu kwanciyar hankali, abinda ya tabbata zai faranta ran Mama, ya kuma wanke bacin
ranta da shi, wato maganar auren sa. Shi yasan inda abinda iyayensa ke so su ji a yanzu to bai
wuce yayi aure hakanan ba, iyayen sa sun matukar daga hankalin su a kan rashin auren sa a
wannan dan tsakanin ya rasa meyasa, ya manta shekaru talatin da biyu a wancan lokacin har
ya wuce matakin samartaka, ya shiga na tuzuranci a al’adance, har hakan na neman ya shafi
zaman lafiyar sa da su, don Mama ta dade da daina kiran sa a waya tace yayi abinda yake so
tunda ya badawa idon sa toka ya ki auren diyar aminiyar ta Barr. Hannatu wato Sadiya
Maijama’a, har wani ma sa’ar yayi wuf da ita (ya aure ta).
A yanzu kam Dr. Sarham Abbas yana cikin wani farin ciki maras misaltuwa. At last, at very
long last, he found his first and true love, bama mai kama da ita ba, ba mai irin kokarin ta ko
kamanninta ba (kamar yadda Mama tai masa fata), a’ah, ita din ce da kanta ba sako ba, wato
(his ex) Madinah Attahiru ba wata ba! Kuma har sun daidaita sabanin dake tsakanin su, duk
tsayin wannan lokacin na komawarsa Jeddah suna tare da Madina Attahirusun sake hadewa
acan jami’ar sarki Abdul Azeez (KAU) Jeddah.
**** ***** ****

WAIWAYE ADON TAFIYA (1)
(DR. SARHAM SHANONO A JEDDAH)

Abinda ya faru shekaru ukun baya shine tun saukar sa a birnin Jeddah cikin wani ikon Allah
suka hade shi da ‘ex’ dinsa Madinah Sorondiki a cikin asibitin koyarwa na ‘KING
ABDUL’AZEEZ’, inda duk a can ne dukkansu suke kara zurfafa karatu.
Ba zai manta ba kwanansa uku da zuwa ranar nan ya zo wucewa, kamar daga sama ya
hangi Madina Attahiru tana shiga wata farar mota kirar ‘Audi’ don fita daga asibitin. Sarham ya
mutstsika idon sa, don da farko ya dauka gizo idon nasa yayi masa, irin wanda dare da rana ya
saba yi masa a kan ta, har saida ya dinga neman taimakon Ubangiji da sallolin dare kafin ya
samu Madinah ta daina yi masa gizo a kowacce kusurwa ta dakin sa.
A ranar da yayi mata wannan ganin a asibitin kusan karamin hauka yayi, bai iya yayi barci a
daren ranar ba ko na minti daya, ‘fade memories’ na komai nasu a can baya ya dawo masa
sabo, ya dawo da tsohuwar Madinah sabuwa a ran sa.
Amma a washegari da ya sake ganin ta, sai ya kuma tabbatarwa ba gizo idon sa ke masa ba,
Madinah ce. Har yau bayan rabuwar shekaru bakwai, tana nan a Madinah ‘yar gayun ta. Fara,
doguwar nan sambaleliya da ya sani hamshakiyar ‘yar hutu. Madinah siririya mai yalwar gashin
ido dana gira, ta kara tsayi da cikar halitta, ga sabon aji na musamman data kara a kan wanda
ya santa da shi a baya, ko dama can Madina classique lady ce balle yanzu da ta ke kusan
shekaru Talatin. Tana takunta akan kasa cikin rangaji da rangwada tamkar basarakiya, tabon

sallahr nan har yau yana nan a kan goshin ta, ya kara fitowa radau, shi ya kara tabbatar masa
har gobe tana nan a “Madinah” mai yawan ibada.
Madinah (Munawwararsa da ya sani) tuntuni mai aji ce, iyayenta sun wadatata da komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login