Showing 1 words to 3000 words out of 46557 words
Chapter 1 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf
‘YAR CIKIN BADALA
(HAUWA-KULU)
2
SUMAYYAH ABDULKADIR babbangoro2015@yahoo.com
07030137870
(whtsp only)
PAID BOOK
SADAUKARWA
SADAUKARWA NE GA DUK MAKARANTA LITTATAFAINA ‘YAN CIKIN BADALAR KANON
DABO.
HAUWA-KULU-2
M
ota na tsayawa agaban su ta ce masa “Kurna”. Ba don ta san kowa a Kurnan ba, sai don ta san
tayi nisa dai da cikin gari, ta tafi can wajen fita garin Kano, shi kuma mai mota ya ce naira biyar,
duk da Inna ta san zuka musu kudin yayi don ya gansu hajaran majaran amma bata ko nemi
ragi ba, ta kama hannun Hauwa suka shige da katon bakkon kayan su. Aka zo Kurna, sai ta rasa inda zata ce ya sauke su, shi kuma ya gaji da yawo dasu a
Kurna sai yace ko tasha zan kai ku in gari zaku bari? Inna ta samu kanta da cewa “eh”, sai ya
kai su tsohuwar tashar nan wato Tashar Kuka ya ajiye su.
Inna ta kama hannun Hauwa duk sun yi wujiga-wujiga da gajiya da yunwa, suka je
rumfar wani mai shayi, a daidai lokacin hantsi ya dubi ludayi, ta zaunar da Hauwa a bencin da
babu kowa, mai shayi ya zo wajen su yace “Iya lafiya? Ba’a bara a kan benci na, na sana’a ne”.
Hauwa ta fiddo manyan idanun ta tana sama tana kasa da su, wai dai ya san hararar sa take
yi, don ba abinda ta tsana a ambata mata irin a dangantata da kalmar “BARA” don tana
makauniya mara ido, ba don Inna ta koyar da ita kyakkyawar tarbiyyar rashin saka baki a
maganar manya ba, da ta zage shi, mai shayi ya ce, “bayin Allah ku kara gaba don Allah, kada ku kashe min kasuwa da wannan daurin bakkon
naku duk warin tsummokara”.
Inna ta daure ta ce “don Allah zuba mata shayin ta sha, zan biya ka, nawa ne kofi daya? Ka
yanka mata biredi”.
Nan ne Hauwa ta kasa daurewa, ta ce “Inna ko wannnan shi ya saura shayi a duniya, ko
yunwa zata kashe ni, ba zan sha ba, tun da ya ce mana mabarata” ta fashe da kuka, sannan ta
mike tana laluba bakkon su, ta dauka ta dora akan ta, Inna ta mike ta kama hannun ta suka tafi,
yana cewa “Umma ta gaida ashsha, dama makafi akwai fadin rai, da zuciyar tsiya kamar kutare,
ni bana son harkar mabarata da nakasassu”.
Inna ta hango rumfar wata mata mai saida abinci, ba yawan mutane a wajen, sai ta ja
Hauwa suka nufi wajen, matar tana ta kai kawo da masu sayen abinci uku dake kan tebur, da
ganin ta ka ga ‘yar Kano-Jeddah, Inna tayi mata sallama, da mutuntawa ta amsa ta ce “Iya
sannu ko? Abinci zaku saya?” Inna tace “eh, zuba mata ta ci ta koshi kisa mata yankan nama,
nawa ne kwanon shinkafa da miya?” Matar ta ce “naira bakwai”, haka ta zuba ma Hauwa abinci
mai rai da motsi ta shigar da ita rumfar da babu mutane sosai ta bata ruwa ta wanke hannu.
Inna tana zaune tana sakawa da kwancewa, ko yunwar ita bata ji saboda duhun zuciya da
bakin cikin abinda Zakari yayi musu. Tana matukar son gidan ta, duk wani tarihin ta da mijin ta
da ‘ya’yan ta, duk wata dabdalar gidan aure, dama jin dadin rayuwar ta ya ta’allaka ne a cikin
gidan nan na bayan BADALA. Amma ace yau rana daya….??? Ta sa gefen zaninta ta share
hawaye tayi sharbe, wanda Hauwa ta ji shi.
Tadago gululun manyan idanun ta zuwa sashen da taji sharben Inna “Inna ke bazaki ci ba
ke?” “Ci Kulu ki rabu da ni kinji, ba zan iya kai ko ruwa baki na ba yau”.
Sai itama ta tsame hannunta, ta koma jikin bangon wurin ta jingina itama, kamar yadda Inna
tayi, ta hade jikin ta cikin hannayenta ta takure kai a cikin kafafunta, ta ce “to shikenan nima ba
zan ci ba, tunda kema Inna ba zaki ci ba”.
Inna ta ce “Kulu yunwar ce bana ji sam”. Hauwa ta ce “na san bacin rai ya hana ki ci, amma
abu daya nake so ki tuna Inna, idan Kawu Zakari ya rushe gidan mu, ya kwace ta karfin tsiya
saboda iya zaluncinsa ai Allah ba azzalumin bawanSa bane, kuma baya yafe hakkin wanda aka
zalunta. Ba kuma zan gushe a cikin sujjadar salloli na biyar na farillah ba face ina mai kai karar sa
wurin Ubangiji.
Inna ki manta da Baba Zakari, mu fuskanci wadda zata fishshe mu. Son samu Inna mu fara
sana’ar abinci muma a tashar nan, tunda na lura akwai kudi a jikin ki”.
Inna ta ce “eh da kudi, wadanda yaronnan Jamilu ya bani kan ya tafi, amma Hauwa ai baka
fara sana’a farat daya baka zauna a wajen ka fuskanci yanayin wajen dana mutanen wajen ba,
da irin zaman da ake yi a wajen, dabi’un su da yanayin mu’amalar su.
Ta yaya zamu zauna a Tasha bayan matattara ce ta rashin arziki ga ‘ya’ya mata? Ki dai bari
mu kara gaba, in ya so ko a masallaci sai mu dinga kwana”.
Duk hirar nan da suke yi a kunnen Hajiya Ladi mai abinci, tana kirga kudin cinikin ta tana
sauraron su da kunne daya, don ta gama da girkin safe, zata fidda riba ta dora na rana.
Ta ji tausayin Inna ta kuma ji Hauwa ta burge ta, wadannan idanu na ta da alama basa gani,
amma duk da haka zuciyar ta bata mutu ba, ba ta ce tunda gasu a tasha su yi bara ba, don ita
makauniya ce zata zamewa uwarta hajar samu, gata budurwa son kowa, sai ma cewa uwarta
take su kama sana’a. Hajiya Ladi ta matso inda suke ta zauna, tace “naji duk abinda kuka tattauna a junan ku, duk
da ban san daga inda kuke ba zan baku masauki a gidan da nake zaune, in kuma dinga baku
aikin abinci kuna taimaka min, sai mu dinga zuwa nan tare kullum in mun sayar mu koma gida
tare, ni kuma zan dinga baku abinci sau uku a rana.
Ban yi karyar biyan ku ko sisi ba, abincin da zaku dinga ci da wajen kwanan da zan baku
shine ladan aikinku, in ya so in kika gane yadda ake sayar da abinci a nan tashar kina iya kafa
naki tebirin daga baya.
Baiwar Allah muma da Allah ya rubuta mana samun na abinci a Tasha, ba zabin mu bane ba,
da gaske akwai bata gari, kuma matattara aikin ashsha kala-kala, amma yaya zakayi da abinda
Allah ya rubuta cewa anan samunka yake?”.
Inna da Hauwa suka hau godiya ga Hajiya Ladi mai abinci, kuma tun daga ranar ta basu daki
guda a gidan ta wanda ke nan unguwar Rijiyar Lemo, ta kwashe shirgi tace su dinga kwanciya a
dakin. Amma da wuri zasu ke tashi su tafi tasha a dora mata abincin safe, zuwa karfe hudu sun
saida na rana sais u dawo gidanta tare. Ta koyawa Inna kalolin irin girke-girken da take yi, ga mamakin ta sai ta samu Innar
Hauwa kwararriya ce a fannin girki har ta fita kwarewa. Gata da tsaftar jiki data muhalli, tuni ta
kara rike Inna da kyau.
Tun daga ranar suka soma yi wa Haj Ladi aiki, Hauwa ma ba’a barta bata aikin komai
ba, ita ke wanke wanke na kwanukan da aka bata, tsaf take wanke su ta dauraye ta kife a
kwando.
Kafin sati ya zagayo sun kware da aikin abincin Haj. Ladi, sun saba da sauran ma’aikatan
Hajiya Ladi biyu Zulai da Amuna.
Hajiya Ladi na da ciwon Asma duk ranar da ta motsa mata bata iya tabuka komai, sai
kwanciya sai tari, sai ta danka komai a hannun Inna, ganin ita babba ce ta girmi su Amuna
kuma ta fi su hankali da kula, wannan ya fusata Zulai ta bar aikin, don a ganin ta an fifita bakin
zuwa a kanta. Ya zama saura Amuna da Hauwa kadai ke yin sauran ayyukan, har aikin da baka tsammanin
mara ido zai iya Hauwa ta iya, su yankan alayyahu da yankan salak, kuma ba tare data yanke
hannun ta ba, haka duk wani aiki da za’a iya yi daga zaune, ita Inna ke baiwa tayi.
**** **** ****
Ciwon asma mai tsanani ya kwantar da Hajiya Ladi sosai, baiwar Allahnnan sai ta soma
tsoron kada ta mutu ba’a san kowa nata ba, yanzu kam tayi nadamar rayuwarta da kuruciyarta
data karar a Kano-to-Jeddah, harta soma tunanin iyayenta ko suna raye yanzu?
Haj Ladi ta soma istigfari daga kwance, rannan cikin dare ta tashi, ta kuma tashi Innar
Hauwa, tana kuka ta soma gaya wa Inna ita asalinta. Tace ita ‘yar kauyen Billiri ce, Billiri ta
Gombe, ita ‘yar mai garin Billiri na lokacin ce, tace abinda ya fiddo ta daga gida auren dole ne
suka samu uwar daki ta haure da su Makkah suka jima cikin rayuwa ta Kano-Jidda, daga baya
aka kamo su aka watso Najeriya, shine fa ta kama sana’a don tana tsoron karuwanci a Kano,
sabida shari’ar musulunci da aka kafa lokacin, har yau bata iya ta koma gida ba.
Tace “idan ta Allah ta kasance a kaina, na bar miki shagon nan ki cigaba da hayar sa saboda
rikon amanar ki, bamu jima tare ba, amma na yarda da halayen ki na kwarai, inaso ki cigaba da
sana’a ta amma ki tattara komai nawa ki kaiwa mahaifi na, ki roka min gafarar sa, zan kara jan
hankalin ki kan ki kula da mutuncin makauniyar ‘yar ki a rayuwar tashar nan, don akwai bata
gari, gashi ta cika ido ta kai munzali, Allah ya taya ki kula da ita.
Jikin Inna yayi sanyi ta ce “Hajiya Ladi tafi da kan ki nemi gafarar mahaifin ki, tunda da
sauran karfin ki, ciwo ba mutuwa bane, iyaye sun wuce komai kuma ba zaki taba samun
kwanciyar hankali ba in baki samu albarkar su ba. lokaci bai kure miki ba Hajiya Ladi”.
Inna da Hajiya Ladi sun yi wannan maganar da kwanaki biyu Inna ta wayi gari da asubah don
yin sallah sai ta fahimci Haj. Ladi bata tashi sallahr asubah kamar yadda suke yi kullum ba, tun
tana tunanin jikin ne ya motsa mata ta makara har garin Allah ya waye Haj. Ladi bata tashi ba,
sai ta matso ta duba ta, anan ta fahimci Hajiya Ladi, babu. Wato rai yayi halin sa. **** **** ****
Inna ta tsaya tsayin daka aka kai gawar Hajiya Ladi gidan mahaifin ta wato gidan
Maigarin Billiri, ta kuma isar da wasiyyar Hajiyar ta hanyar damka masa dukkan kudaden ta na
cikin lalitar ta, ya sakawa Inna albarka yafi cikin kwando, ya tambayeta ko ita ‘yar ina ce? Don
bata yi masa kama da ‘yan Kano Jiddan ba ita, Inna ta gaya masa daga cikin Badalar Kano
suka fito, neman abin rufin asirin rayuwa, sakamakon batan maigidan ta, shine suka hadu da
Haj. Ladi gun sana’arta, ta kuma taimaka musu a lokacin da basu da mataimaki sai Allah, ta
gaya masa sun yi zaman amana tare. Ta kwashe duk irin taimakon da Haj. Ladi tayi musu ta
fada masa, shi kuma ya ce albarkacin ta da mutuncin ta ya yafe wa Ladi duniya da lahira. Zai
taya ta rokkon gafarar Ubangiji.
Ta fada masa Hajiya Ladi ta bar mata shagon abincinta ta ce ta kama ta cigaba da yi,
tana da jari, don haka zasu koma Kano, yayi mata fatan alkhairi da godiya, bayan sadakar ukun
Hajiya Ladi suka koma gidan da take haya inda suke zaune, kasancewar kudin shekara data
biya bai kai ko rabi ba. Inna ta fiddo ajiyarta ta kudin da ta ke ta ajiye da su tayi cefanen abinci yadda suka saba
lokacin Haj. Ladi, daga ranar ta cigaba da sayar da abinci, ba maraba da Haj. Ladi na raye.
Ciniki sosai suke yi da tsofaffin kwastomomin Haj. Ladi, a kullum ranar Allah sai ta dafa
shinkafa tiya uku, suka tara kudi masu dan yawa, daga nan Hauwa ta kawo shawarar su canza
gida mai dan kyau, abinda suka tara zai ishe su kama gidan haya tunda kudin Haj. Ladi ya kare,
Hauwa tace su kama gida a nan cikin Kurna ko dai wani waje kusa da tashar kukan. Hakan kuwa aka yi. Inna ta kama dan mitsitsin gida mai tsafta fiyeda na Haj. Ladi, mai
dakuna biyu da bayi da madafi a wani lungu cikin unguwar Kurna.
Sana’ar abincin Inna na kara bunkasa, don duk tashar kuka babu mai abinci mai kyau kamar
nasu, har ta kai Inna ta dauki ma’aikata biyu a karkashin ta da suke tafiya tun asubah su dora
abinci kafin ta iso, Saude da Hajara zawarawa ne, ita kuma sai gari ya fara haske tayi sallar
walha take tadda su, galiban zata tarar har sun dafa sun kwashe, sai ta zauna ta fara sayarwa
da kanta.
Basu jima a Kurna ba Hauwa ganin hankalin su ya kwanta, kuma samun su ya ninka na baya
ta tada kayar bayan komawa makarantar su, ga shekarar na neman wuce ta, za’a zana
qualifayin, tunda dai yanzu suna samun kudi daidai gwargwado Inna bazata kasa daukar nauyin
zuwan ta makaranta ba, dama jakar makarantar ta da komai na makarantar ta na nan har
lokacin bata rabu da goyon ta ba, hatta uniform da [photochromic Glass] dinta da takalminta
suna nan cikin jakar.
Inna ta ce Hauwa daga nan Kurna zuwa makarantar ku akwai nisa fa, kuma bazan iya kai ki
kullum da kaina in dawo dake ba, da girkin abinci da muka dogara da shi zan ji ko da kai ki
makaranta da dauko ki?”
Hauwa ta ce “Inna me zai hana mu samu mai Achaba wanda ya kasance dan unguwar nan
da aka san gidan su da komai nasa, ku tsadance, kullum ya kaini ya dauko ni, in yaso a dinga
biyan sa duk karshen wata”.
Shawarar Kulu ta samu karbuwa gun Inna, dama tasan dai Hauwa-Kulunta ba daga nan ba
wajen kaifin basira. Hakan kuwa akayi.
Hauwa ta samu komawa makarantar su special school ta Kano a ranar wata litinin, daga
malamanta har dalibai ‘yan uwan ta sun yi farin ciki da dawowar Hauwa Bilyaminu, bayan
kwashe watanni shidda rabon ta da makaranta.
Amma duk da haka saboda kokarin Hauwa malaman su basu yi mata rifitin ba, sun
tabbatar bada jimawa ba zata kamo duk abinda ya tsere mata.
Wani kabila dan bautar kasa mai suna Teacher Amos Hedimasta yasa yake yi mata lesson
fisabilillah, saboda kokarin ta, kullum na awa daya bayan tashi daga makaranta. Wannan ya
taimaka mata kwarai tayi saurin kamo ‘yan ajin nasu, ya zama da an fara sabon darasi Hauwa
zata cafke, musamman da yake akwai kishin abun a ranta da kulafucinsa, hadi da tsoronta na
zama MABARACIYA saboda rashin ido.
Hauwa ta jajirce, ko barci bata yi kullum ta dawo zaka samu tana karatu da Braille, har sai
Inna ta kwace littatafan ta, ta kashe fitila, ko ta ce, “karatun ya isa haka, dare mahutar bawa ne”.
Ba jimawa da komawar ta makaranta aka yi jarrabawar kwalifayin, aka yi hutu, wanda in sun
koma su Hauwa zasu shiga aji shidda na sakandire.
Sakamakon jarrabawar qualifayin din ta lokacin da ya fito, yafi na kowa a makarantar kyau,
yafi na kowa daraja, komai nata daga ‘A’ sai ‘B’. A lokacin kam makerin budurci ya gama kera
Hauwa Bilyaminu, da ka ganta kaga kyakkyawar bakanuwar budurwa, mai samun kulawar Uwa
da tsaftar jiki da abinci mai gina jiki, yadda ya kamata. Kafin su Hauwa su koma hutun da zata fara aji shidda suka bar sayar da abinci a tashar
kuka, suka dawo sayarwa a tashar Kano-Line, ba don komai ba sai don yafi kusa da
makarantar Hauwa kuma samarin tasha sun fara son matsawa Hauwa a can tashar Kukan, da
cewa suna son ta har da masu neman ta da sakarci, duk da idon uwar ta kuwa. Wannan ya tadawa Inna hankali ba kadan ba, ta ga dole su bar tashar kuka zuwa inda basu
saba