Showing 18001 words to 21000 words out of 47415 words
Chapter 7 - GOJE part 1 By Binta Umar Abbale-1.pdf
shirin aikatawa ba.
Tafiya suke tsakankanin bishiyu da manyan tsaunika, gami da kwazazzabe, gabadayansu, babu
alamun gajiya a tattare dasu, tafiyar suke suna bushe-bushe tare da farautar duk wata dabbar
data gilma a gurin, ita dashi ne a gaba, yayin da jama'arsa ke take masu baya, tayi masifar
galabaita! bakinta ya bushe cikinta in banda qugi! babu abinda yake, ba komai ke damunta sai
yunwa,
kallonshi tayi kamar tunda aka halliceshi be taba dariya ba, tunda ya rike hannunta da zasu tafi
be sake kallonta ba ballantana magana ta had'asu,
Magana takeso tayi masa amma tana jin shakka! don yanayin sa kadai dole ya baka tsoro! sai
taja ta tsaya cakk! tana sauke wani irin numfashi!
Kallonta yayi na minti biyu, kafin ya juya yayi masu magana da ido, sun gane abinda yake nufi,
sai suka samu guri suka zazzauna wasu kuma suka fara hawa kan bishiyu suna kad'o 'ya'yan
itace.
Kan wani ice ta zauna tana kallonsa sai kai kawo yake a gurun.........."Ina bukatar ruwa da
abinci." tafada tana dam hararar bayansa. Yana jin maganarta amma be juyo ba.
"Ina magana fa."! tafada kamar zata fashe da kuka.
" Alba." sunan d'aya daga cikin yaransa kenan. Yayi saurin zuwa gurin, yace."Ka bata ruwa da
abinci." Yace." An gama maigida.
Gabanta ya k'araso da wata 'yar jarka ruwane a ciki, ya mika mata da fadin." Kisha yanda kike
so"
Cike da k'yan'kyami take bin jarkar da kallo, 'ya'yan wasa sun tashi a cikin ruwan.
Tsaki! taje cikin tsawa! tace."Wuce ka ban guri waye zai sha wannan kazantaccen ruwan."
Maganar ta dauki hankalinsa ya juyo yana kallonta, shi kansa Alba d'in ransa ya baci da jin irin
tsawar data buga masa.
Ya kalleshi da fadin." Jeka kawai." Ya girgiza kai, da fadin" Angama." Gurin ya bari. Shi kuma
ya juya mata baya, tunda ba zata sha ruwan da kowa yake sha ba sai ta zauna a haka.
Ranta ya baci ganin ya juya mata baya tace." Wai me ake nufi ne."?
Ba tare da juyo ba yace." Ya kike so ayi miki? an baki kince bakya so akwai wanda kike so ya
zama ruwa a cikinmu kisha."?
Tace." Ruwan fa bashi da kyau, bayan haka ya za'ayi na hada bakina dana wannan 'kazamin."
Ya girgiza kai da fadin." Sai ki zauna da ishirwarki ."
Kuka! ta fashe dashi! da fadin" Allah ya isa tsakanina da kai mugu azzalimi."!!
Ya juyo da fuskar bacin rai yana kallonta.....Alba dake kokarin zuwa gurin yace."Oga wannan
yarinyar fa tana da matsala wallahi! da zaka bani dama sau daya dana koya mata hankali ."
Ya kalleshi na minti biyu kafin yace." Ko bana guri ban amince da hakan ba amana ce a gurina."
da sauri yace."Allah ya huci zuciyarka."
Ya gyada kai da fadin ." Wanke lemon ka bata." Da sauri yayi abinda aka umarceshi, ta kar'ba
tana yatsine fuska.
Yana kokarin barin gurin yace."Bani wannan jakar ruwan ta hannunka." Ya mika masa, a
gabansa ya bude murfin ya zubar da ruwan ciki. Ya bar gurin da ita a hannunsa.
Ita dashi duk suka bishi da kallo yana tsallake manya duwatsu kafin su daina ganinsa, gabanta
ya tsananta fad'uwa ganin baya gurin, ta dora idonta kan Alba dake tsaye yana zazzare mata
jajayen idanuwansa, saurin sunkuyar da kanta tayi, tsoro takeji kada yayi mata wani abun, sai
da ya gama cije-cije kafin ya bar gurin.
Ya kasance sai ita kadai a gurin, sai motsi da maganarsu da takeji a saman bishiyu, ta daga kai
tana so ta hangesu, amma ta kasa ganinsu,
Dajin ta dinga bi da kallo, kanta yana juyawa, manya dutsina da tafka-tafkan bishiyun dake
gurin sun juyar mata da kai.
Da sauri ta kama hanyar da taga yabi, tana tafiya tana waiwayen bayanta.
Sai da yayi tafiya mai tsayi sannan ya cimma ruwa yana gudana daga kasan wani tsabtataccan
dutse gare-gare dashi.........Ya haura wasu manya duwatsu kafin ya samu nasarar d'ibar ruwan.
Yana juyowa kibiyar ta gilma ta gefan fuskarsa, da alama saita shi akayi Allah be bada nasara
ba.......Da mugun sauri ya daga kanshi sama, can ya hango su saman wani dutse sun kai su
biyar, yayi gaggawar fitowa daga tsakanin ruwan.
Suma basu fasa harbinsa da kibiya ba.
A gaggauce ya fara kurd'awa inda jama'arsa suke baya su cimma inda suke ba tare da shiri ba.
sai dai me! biyoshi sukayi suna sakar masa harbi ta ko'ina!!
K'aro sukayi da juna!! ya rike hannunta tamau! bayan wata bishiya suka 'buya, suka 'karaso
gurin suna sassare matattatun itacuwan da suke gurin.
Hannunsa dake cikin nata yake kokarin cirewa ta rike da kyau! tana girgiza masa kai! wai
kada ya fita, ya sake yunkurin cire hannunsa ta rike! hawaye masu tsananin zafi suka wanke
mata fuska, bakinta tasa a kunnansa, a hankali tayi magana "Kada kaje."
Jajayen idonsa ya tsira mata! ta marairaice fuska, tana ro'konshi da idanuwanta.
Tausayi ta bashi ganin yanda jikinta ke wani irin karkarwa, cikin zuciyarsa yace."Ba yanda
za'ayi yana ji yana gani nasara ta kufce mai wannan ce hanya mafi sauki da zai tunzura
zuciyar abokin gabarsa.
Kafin ta ankara, ya fuzge! hannunsa, ya fice! ta leqa kanta tana hango artabun da suke a
tsakaninsu, su biyar ne shi d'aya, amma cikin ikon Allah ya samu nasara a kan mutum biyu
ukun kuma suka gudu!.
Ya k'wace wukaken dake jikinsu, da sauran kayan ta addanci, kana ya d'aure musu hannuwa,
gaba ya tisa su har inda suka yada zango shida jama'arsa.
*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin Airtal ko mov
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*í ¼í¿¹
í ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURNí ½í±‘í ½í²«_)
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONí ½í¶Šï¸í ½í³š_*
_____________________
*RASHIN ADALCI A TSAKANIN MATA*
___________
_*Mata da yawa su kanyi kukan rashin adalci da mazajensu keyi a tsakaninsu. maza kuji tsoron
Allah kuyi adalci a tsakanin matanku. lallai wajibi ne kuyi adalci tsakanin matayenku ga wanda
yake auran mace sama da d'aya dole yayi adalci, ya sani cewa dukkan abinda yake gudana
Allah yana sane kuma yana ganinsa, kuma wallahi sai Allah ya tambayeshi akan zaman da yayi
dasu a goben kiyama.*_
*Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkan wanda yake da mata biyu sai ya karkata ga daya
baya yiwa dayar adalci, to zai zo ranar alkiyama bangaran jikinsa guda a shanye)*
*Malamai sunce karin aure ba wajibi bane, ba mustahabi bane ga wanda yake da ikon ya 'kara
amma wajibi ne kayi adalci, idan har kasan ba za kayi adalci ba to kada ka fara neman k'ara
auran ma domin k'arin zai iya kai ka zuwa ga halaka.*
*Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkaninku masu kiwo ne kuma dukkan ku abin tambaye ne
akan abinda aka baku kiwo a gobe kiyama)*
*Allah a cikin alkur'ani yayi hani akan kada maigida ya karkata gabadaya zuwa ga wata daga
cikin matansa ya kyale sauran matan saboda rashin adalci*
*Allah ya baku ikon adalci a tsakanin matayenkuí ½í¹í ¼í¿»*
FREE PEGE
*25&26*
"Kada ku yarda ku bari ya kubce daga hannunku, mugu! ne macuci! ya jima yana ta'addanci a
k'asa! kuyi masa hukunci mai tsauri! domun da bakinsa yake fadin cewa yafi karfin hukuma!
yau tsayin kwana shida kenan daya raba ni da iyayena yayi kidnapping dina domin samun
makudan kudi daga gurin mahaifina, " Sunana ZINATU ni 'yar asalin jahar kano ce mahaifina
kuma shine sarki dake kan kujerar mulki a jahar." Bilhaki da gaskiya take maganar.
Gabad'aya hankalinsu ya koma kanta a lokacin da take wannan maganar, da yawa daga cikinsu
ba su lura da ita ba, maganarta ce ta janyo hankalinsu kanta. ganinta a firgice babu sutturar
arziki yasa suka gazgata maganarta, babban cikinsu ya kwantar mata da hankali da cewa
komai yazo karshe kuma sunyi alkawarin kaita gaban iyayenta idan sun gama gudanar da
binkice.
Beyi mamaki da jin furucinta akansa ba, ita kad'ai ce zata bada cikakkiyar sheda a kansa,
amma ba tayi hakan ba, to ba zai tsananta ba, ba kuma zaiyi jayayya da hukuma ba, zai bi
doka da odar amma ya san ita gaskiya d'aya ce kuma a kanta yake babu gudu babu ja da
baya babu shakka! Allah za bayyana mai gaskiya.
Da kansa ya haura ya shiga motar ya zauna, sojoji uku suka zauna hagu da damanshi, ya kalli
na hannun damansa cikin nutsuwa yace." Akwai sauran yarana da suke n........ ya katseshi ta
hanyar buga masa tsawa da fadin.
"Rufe mana baki ko kai zaka nuna mana aikinmu."? Kansa ya girgiza, yace." To kabi umarnin
mu domin shine samun zaman lafiyarka."
Be sake cewa komai ba ya kauda kansa gefe yana hangensu suna ta binkice a gurin...........Can
ya hango sun taso sauran yaransa a gaba! suna dukansu! bai dauke idonsa ba har sai da suka
karaso gurin, gabadaya sun galabaita domin wasu harda rauni a jikinsu bayan wa'inda suka
kone sakamakon bomb din daya tashi, ya tausaya musu sosai, domin ya san shine mujaza!
domin da yawa daga cikinsu ba'a son ransu hakan ta faru ba.
Suka dinga turasu cikin motar suna dukansu da wata murtukekiyar bulala irin ta karfe!
To duk iya binkincensu a gurin Allah bai nuna musu dungulmin hannun *Uban daba!* da 'kasa
ta turbudeshi a gurin ba, Yana kallonsu suka 'karaci dube-dubensu suka shishshiga mota da
niyyar fita daga dajin.
'Bude baki yayi da niyyar magana kawai ya hangota tare da wani soja yana kokarin bude
mata gaban mota domun shiga........Yaji wani irin ciwo a cikin ranshi! bakinsa ne yayi nauyi ya
gaza furta maganar dake cikin cikinsa har suka fita daga cikin dajin bai dago kanshi ba! wani
irin kuttun bakin ciki ya tsaya masa a wuya, tunda yake bai ta'ba ganin butulu irinta ba.
Da yayi motsi zasu saita shi da bindiga! da fadin." Ya kiyaye idan kuma yayi wani yunk'uri na
gudu to zasu harbe shi! murmushi kawai yake musu, wanda hakan ke 'kara tunzura musu
zuciya.
Labari kaf ya cika garin Katsina da kewayenta cewa A yau 11/3/2007 jami'an tsaro sunyi
nasarar kama babban dan ta'addah nan wato *Mashekin daji!* wanda ya addabi k'asa da
jama'ar dake cikinta.
Headquarter 'yan sandan kuwa cike take da 'yan jarida da jama'ar gari masu ganin kwal uwar
daka.
Koda motocin jami'an tsaron suka shiga headquarter 'yan sandan sai gurin ya hargitse da
hayaniya kowa burinsa yayi ido hudu dashi, Mussaman 'yan jarida masu daukar rahoto.
Sai da suka rufe masa fuska sannan suka fito dashi a dadd'aure! Suka rirrikeshi da kyar yake
cire k'afa sakamakon sark'ar da tayi masa dabaibayi!
Duk da hakan sai da yan jaridan suka dinga daukar hotonsa tun daga sama har kasan
Kafafunsa, da yawa daga cikin 'yan jaridar da jama'ar dake gurin sunyi mamakin ganinsa
ingarmar namiji a labari dai sun san cewa ba haka kammaninsa yake ba gajere ne mara
fasali ya akayi kuma a zahiri basu ga haka ba.
Har sai da aka shiga dashi ofis din Asp sannan kowa ya watse, jama'ar gari suka tafi da zancan
a bakunansu, su kuma 'yan jarida suka fara gudanar da ayyukansu.
****
Cikin tsananin tashin hankali Saude matar Alba ta shiga gidan tana kuka hannunta rike da
jarida.
Uwale ta tare ta tana tambayarta abinda ke faruwa.
Jaridar ta nuna mata da fadin." Uwale kin san abinda yake faruwa kuwa."? ta kar'bi jaridar tana
dubawa tace." Saude kin san ban iya karatu ba me yake faruwa."
Tace."Ki duba hoton jiki mana Mijina Alba ake tuhumarsu da ta'addanci."
Gabanta ya fadi! tace." Ta'addanci kuma Saude! su da suka tafi farauta mai ya hadasu da
ta'addanci inace gobe zasu dawo."
Saude na kuka tace." Uwale kisa kunne da kyau ki saurari jawabin da zanyi miki."
Jiki a sanyaye tace." Ina sauraranki."
"Jami'an tsaro ne suka kama UMARU wato jikanki dashi da yaransa saboda zargin da ake
musu na ta'addanci, a yanda na karanta rahoton cewa wai ana tunanin shi UMARU shine
wannan d'an ta'addan da ya addabi kasa! yanzu haka dai gabad'ayansu suna hannun hukuma!
jama'a da yawa sunyi imani da cewa hukuncin kisa za'ayi musu."
Hankalinta ya tashi sosai sai ta fashe! da kuka ta tsirawa hotonsa ido duk da fuskarsa a rufe
take hakan be hana ta ganeshi ba, ta tsirawa kafafunsa ido tana wani irin kuka tace." UMARU
wannan ranar nake gudu a gareka, itace rana mafi muni da ba zan ta'ba mantawa da ita ba,
ashe tsautsayi ne ya sanya ka tsunduma kanka wannan harkar, ni na san halinka UMARU
kuma zan bada sheda a kanka, ka taka sawun 'barawo insha Allah sai Allah ya wanke ka daga
zargin da ake maka." Kuka sosai takeyi hawayenta duk ya jika takardar dake hannunta.
Hamra'u ta shigo gidan cikin kuka na fitar hayyaci! tana zuwa ta rugumeta da fadin."Uwale ya
za muyi da wannan kaddara hukuma ta kama Yayana da laifin ta'addanci! bayan bashi da laifi
Yayana bashi da mugunta baya cin hakkin wani burinsa kullum ya za'ayi k'asa ta samu cigaba,
amma ya taka sawun barawo jami'an tsaro sun kamashi dumu-dumu a cikin sansanin da *Uban
daba!* yake zaune da jama'arsa, Uwale ya za muyi bamu da kudi bamu da ikon da zamu
tunkari hukuma! domin kalubantar zargin da sukeyi akan wanda bai ji bai gani ba."
Tace."Hamrau bamu da komai wanda zamu tunkari hukuma dashi, amma muna da Allah shi
kadai zai ne zai mana jagoranci Allah ba azzalimin sarki bane yana tare da masu gaskiya insha
Allah cikin hikimarsa zai bayyana mai gaskiya."
Asp Musa Baharu shine shugaban 'yan sandan jahar, kuma duk wani jami'in tsaro a
karkashinsa yake, mutumin yana da hankali da nutsuwa gami da sanin makamar aiki, koda aka
shigar masa dashi ofis din kallo daya yayi masa ya tabbatar da cewa bashi suke da bukata ba,
amma be nuna hakan a zahiri ba, sai kawai ya bawa wa'inda suka shigo dashi umarnin fita, ya
rage su biyu kacal a ofis din.
Shi baya ganin komai saboda har yanzu fuskarsa a daure take, amma shi Asp din yana kallon
duk wani motsinsa.
K'ira ne ya shigo wayarsa, daga gidan gwamnati , cikin cikin girmawa ya daga da fadin."
Ranka ya dade barka da wannan lokaci."
Mai girma governor yace." Barka dai Asp barkanmu da samun nasara! wannan ranar ba zamu
ta'ba mancewa da ita ba, yana kuma da kyau ayi rubutu na mussaman domin ajiyewa a kudin
tarihi."
Asp ya d'anyi murmushi da fadin." Hakane ranka ya dade, labarin samun nasara ya cika gari da
sauran garuruwa jama'a da yawa sun kirayi waya suna yi mana murna! amma ban san me yasa
ni nake shakku! akan hakan ba."
Mai girma governor yace." Asp wannan wace irin magana ce? da farko kafin isowar rudunar
da muka tura kaine ka kirayi wayata kake sheda min cewa an samu nasara ya za'ayi kuma
yanzu kace na shakku akan hakan."
Gilashin dake idonsa ya cire ya ajiye saman tevur din dake gabansa, ido! ya tsira masa yana
sake nazartarsa, yace." Ranka ya dad'e ni da kai da sauran jama'ar gari bamu ta'ba ganin
*Uban daba!* a zahiri ba, sai dai muna hasashe akansa cewa shi din wani irin mutum ne mara
fasali sanin hakan ma ya samo asali ne daga bakin d'aya daga cikin yaransa da Allah ya bamu
ikon kamawa a shekarun baya, shine yake sheda mana kammaninsa, a lokacin da al'amarin
ya faru, banyi 'kasa a gwiwa ba na samu yaron daya haddace zane ya zana min kammaninsa
domin samun sauki gurin binkice a kansa, amma abin mamaki! a yanzu wanda yake gabana
a yanzu kuma muke hasashen cewa shine wanda muke nema ruwa a jallo kammaninsa yasha
bambam! da wannan hoton zanen da nasa aka zana min a shekarun baya."
Mai girma governor yace." Asp ya akayi hakan ta faru? kana so ka sheda min cewa bashi
bane."?
Ya mi'ke tsaye da wayar a kunnasa, kujerar ya janye ya fito daga tsakankanin kai tsaye inda
yake zaune ya nufa!.......Yana wayar yana kokarin kwance masa fuska dake d'aure.
Tsaf ya warware d"aurin fuskar, idanuwansu suka hadu guri guda, kujera yaja ya zauna suna
fecing din juna.
Ya cigaba da cewa." Gani gashi a halin yanzu kuma yanzu zan dauki hotonsa na turo maka
dashi domin ka sheda maganata, amma duk wani binkice zanyi a kansa domin samun tartibiyar
magana."
Mai girma governor ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Okey to babu damuwa ina tsumayinka."
sallama sukayi kafin ya kashe wayar, ya tsira masa ido! shima nasa idon ya tsira masa suka
dinga kallon kallo suna nazarta juna, shi Asp din shine ya fara janye idonsa daga kanshi, ya
jima kanshi a kasa kafin ya dago