Showing 45001 words to 47415 words out of 47415 words
Chapter 16 - GOJE part 1 By Binta Umar Abbale-1.pdf
mahaifiyar tata sun jefeta cikin rud'ani mai tsanani
ashe kallon 'yar iska tantiriya jama'a suke mata.
Ta katse mata tunani ta hanyar fadin." Daga yau sai yau babu ke babu Maijidda mutukar ni na
haifeki na rabaki da ita ban hanaki gaisheta ba amma kada ki kuskura ki sake shiga sashenta
ballanatana wata mu'amula ta had'aku, duk wani abu da kika sani naki ne to ki tura a dauko miki
kada na sake ganin kafafunki a sashenta, bayan haka kuma ki tashi kije sashen 'yar uwata ki
nemi afuwarta akan irin abubuwan da ki kayi mata, idan kin gama da wannan to d'aya bayan
d'aya ki kira wayar 'yan uwanki ki gaisa dasu, har shi babban yayanku Magajin sarki wanda ki
ka dauki karan tsana ki ka dora masa har kina gaba dashi saboda yana nuna miki hanya mai
kyau, to shima ki nemi number sa don yanzu haka yana Egypt ki kirashi ki nemi gafararsa,
wannan kadai za kiyi ki faranta min rai."
Ajiyar zuciya ta sauke murya a dashe! tace."Shikkenan Mammah zanyi duk yanda ki kace
amma don Allah kema kiyi hakuri ki gafarceni ki kuma dena yi min mugun baki."
Girgiza kai tayi da fadin." Tunda kike shaid'ancinki na ta'ba jifanki da wata muguwar kalmar."?
girgiza kai tayi da fadin " A'a." tace." To yanzu ma raina ne ya 'baci da al'amarinki, idan kina
bukatar albarka to kiyi gaggawar gyara kuskuranki sai mu samu zaman lafiya da juna."
A sanyaye tace."Insha Allahu zan kiyaye amma kice kin yafe mun." jim tayi na 'yan mintina
kafin tace." Na yafe miki Allah ya shirya min ke shirin addinin islama Allah kuma ya baki miji
nagari wanda zaiyi jimiri da hakuri dake da halayenki."
A zuciyarta ta amsa da "Ameeen ta dan samu sassauci kad'an, da kyar ta yunkura ta tashi tace.
"Zan shiga gurin Mommy kamar yanda kika bukata." Shuru tayi ba tace mata komai ta bita da
ido har ta bude kofa ta fita.
*****
Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin, ta dan samu sassauci daga gurin mahaifiyarta, suna
zaune lafiya wani sa'bani bai sake shiga tsakaninsu ba, kuma tana kokarin yi mata biyayya
daidai gwargwado sai dai har yanzu mahaifiyar tata bata wani saki jikinta da ita sosai ba, A
gurin Safah kawai ta samun walwala dan wani sa'in ma can take yini, wannan ce damar da ita
Safah din ta samu take k'ara nusar da ita hanya mai kyau kuma take kwadaita mata son aure a
cikin zuciyarta, sai dai kuma inda gizo ke sa'kar a yanzu bata da wani tsayayye a hannu lokacin
da take kan ganiyarta take dasu rurutu amma duk ta koresu, a yanzu dai da zasu dawo da
tantance nagartacce a cikinsu, ba kuma ta tunanin neman daya daga cikinsu a ganinta kamar
hakan zubewar mutunci ne, ta san dai yanzu labarin dawowarta ya isa ace yaje kunnuwan
masoyanta to tana zuba ido duk wanda ya damu da ita a cikinsu zai kawo kansa daga nan sai
ta fitar da gwani.
Sai dai kuma a ranar tunaninta ya rushe dalilin hukuncin da mahaifinta ya yanke mata, be fito
fili ya sheda mata abunda ke zuciyarsa ba, amma yayi mata hannunka mai sanda cewa
mutukar bata fitar da miji a cikin satikan daya bata ba, to lashakka shi zai aura mata wanda yayi
ra'ayi.
Tabbas mahaifinta yana tsananin sonta irin son da bayayi wa sauran 'ya'yansa amma ta sheda
cewa shi din kaifi d'aya ne, a haka yake baya ta'ba yanke hukunci ya janye, ita a ganinta kamar
hukuncin yayi tsauri da yawa, har yaushe ta dawo da za'a d'ibar mata sati biyu ace ta fito da
mijin aure kamar akwai rashin adalci a cikin al'amarin.
Ta samu mahaifiyarta da maganar cewa sati biyu yai mata kad'an tayi masa magana ya 'kara
mata sati biyu ya zama wata daya, Gimbiya Aysha ta nuna sam babu ruwanta a cikin maganar
dalili ta riga ta san abunda yake rufe wanda ita Zinat din bata san dashi ba..........da ta samu
Safah da maganar itama cewa tayi babu ruwanta kawai dai tayi kokarin ganin ta fitar da miji
kafin lokacin daka a bata ya cika, sosai ta shiga cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa tunani
kaf ya ta'allaka a gurin neman mafita, babu yanda za'ayi tabi wani daga cikin samarinta nada
tace yazo ya aureta wannan zubar da mutunci ne, tsintar kanta tayi da tashin tsakiyar dare
domin neman zabin Allah, duk da bata da wani cikakken ilmin addini, a hakan take gabatar da
nafila ta zauna saman dadduma tana salatin Annabi kafin ta mika kukanta ga mai kowa da
komai.
*****
To kamar yanda suka tattauna maganar commissioner of police da Asp abunda ya faru kenan,
domin a daran ranar da ya dawo ya bukaci zama dashi..................Suka fara tattauna
maganganu kamar gaske sai dai kuma tafiyar ba tayi tsayi ba suka samu sa'bani dalili
bambacin ra'ayi, a take gurin ya nuna masa cewa shi din *Jan wuya!* ne tafiyar su ba zata zo
daya ba, ya nusa masa cewa bashi yakewa aiki ba 'kasar sa yakewa aiki don haka bai isa ya
gindaya masa wasu sharud'a wanda suka sa'bawa dokar aiki ba. mutukar yana bukatar
tafiyarsu tazo dai-dai to kowa ya zauna a matsayinsa.
Sosai commissioner din yayi mamakin yaron, koda yake tun yana can ya samu labarinsa da
kuma irin alakar dake tsakaninsa da Asp Musa Baharu wanda ya zame masa kadangaran bakin
tulu, babu shakka ya sake ya bar wannan ala'kar ta cigaba da gudana to akwai matsala, dole
ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu, domin samun cigaba da gudanar da al'amuransa hankali
kwance.
Ganin cewa ba zai samu yanda yake so ba yasa yayi saurin b'oye manufarsa yayi saurin gyara
kuskuransa, kwantar da kansa yayi ya nemi maslaha dashi, sannan ya sheda masa cewa ya
shirya tafiya training a sati a mai zuwa zai turashi can *Abeokuta* 'karo sani akan aikinsa."
Cike da kwarin gwiwa ya amsa masa ba tare da wata fargaba ba.
*******
Yau ne ya kasance cikar kwanakin da aka d'iba mata, kwance take sai juyi take ta rasa yanda
za tayi da rayuwarta, tabbas da kuka yana magani da tuni yayi mata, babu yanda ba tayi da
mahaifiyarta kan cewa ta sa baki a cikin al'amarin ba amma fafur! tace babu ruwanta ta dinga
kuka tana rokonta amma taki sauranata, sai ta shiga kiran wayoyin 'yan uwanta tana sheda
musu halin da take ciki, 'yan uwanta mata ne kawai suka saurareta amma Magajin sarki kashe
wayarsa ma yayi yace hakan shine daidai idan bata fito da miji ba to duk wanda ya dace a
daura mata aure dashi.
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta mike zaune tare da sauke kafafunta k'asa! kawai ta tsirawa
kasan kafet ido kamar me neman wani abu.
Turo kofar dakin yaja hankalinta ta tsirawa kofar ido har sai da ta shigo tare da sallama a
bakinta, ido kawai ta zuba mata har ta 'karaso kusa da ita, ta zauna gefenta tare da ajiye ajakar
dake hannunta, wani irin kallo take mata kafin tace." Me zan gani haka ni Sakina 'kawata haka
ki zama kamar wata zautacciya shin wai bayan kin dawo jinyya kika kwanta dubeki don Allah
kin rame kinyi wujiga-wujiga dake."!
Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta kalleta da fadin." Sakina baki da kirki wallahi ace wai don
wulakanci sai yau ki kaga damar zuwa duba ni bayan ta dalilinki na samu matsala, yau satina
uku da dawowa amma saboda baki da mutunci sai yau ki kazo."
'Yar dariya tayi da fadin." Ki bari kawai 'kawata wallahi abubuwa ne sukayi min yawa kin san dai
harkar siyasa sai a hankali kullum cikin uzuri muke wannan dalilin ya hana ni zuwa duba ki
amma wallahi kina cikin raina."
Tace."Ban yarda ba Sakina ai na gane matsayina a gurinki kin nuna min kudi ya fini babu komai
ai." Da sauri tace."Don Allah kada wannan ya janyo mana samun sa'bani 'kawata kiyi min uzuri
ki kuma yafe min, kina nan a zuciyata."
Ta'be bakinta kawai tayi ba tace komai ba.
Tace." Zinat kina da damuwa gaskiya ba haka na san ki ba, ko dai mutanan nan sun samu
nasara akanki ina nufin sunyi keta miki haddi"?
Girgiza kai tayi da fadin." Ko d'aya Sakina kawai ina cikin wani lamari ne wanda na garara fita a
cikinsa na rasa yanda zanyi."
Tace."Menene yake damunki."? Kallonta tayi ta girgiza kai kafin ta sheda mata abunda ke
faruwa.
Taja tsaki da fadin." To yanzu ke ya za kiyi ? tunda kince ke ba zaki nemi tsoffafin samarinki ba,
hakan yana nufin cewa kin amince da zabin mahaifinki."
Hawaye ta share da fadin." Sakina kai tsaye ba zan saduda ba, na san tabbas yau zai kira ni
domin jin ta bakina ni kuma anan zan sake rokar alfarma ya kara min kwanaki ina tunanin kafin
lokacin na samu mafita."
Ta'be bakinta tayi da fadin." Shikkenan ai amma wallahi da nice kai tsaye zan bijire na nuna
rashin yarda ta, haba ai tuntuni an daina yayin auran dole."
Girgiza kanta tayi da fadin." Sakina ni yanzu sulhu nake nema da iyayena farin cikinsu nake
bukata dole nabi komai sannu a hankali amma ni kaina bana tsammanin zan amince da auran
wanda bana ra'ayi."
Tace."Wannan shine tunani mai kyau, ki zauna kiyi nazari da kyau domin ki taimaki rayuwarki."
Haka suka wanzu a daki suna k'ulle-k'ullen yanda za'ayi su rusa hukuncin da yake da niyyar
tabbata a ranar.
Sai yamma likis tayi mata sallama ta tafi bayan ta bata shawarwarin da take ganin sune
kwanciyar hankalinta.
Lokacin da sakon maimartaba ya sameta sai da cikinta ya murd'a tsabar fargaba da tashin
hankali, ta kai minti goma a zaune tana sa'kawa da kwancewa kafin tayi namijin kokarin amsa
kiran.
Tun kafin ma ya fara magana ta fara kuka, kawai sai ya zuba mata ido yana kallo, ta rarrafa har
inda yake ta rirrike k'afafunsa tana wani kuka da fadin." Ranka ya dade kaji tausayina don Allah
kada ka tarwatsa min farin cikin rayuwata bana so ka aura min wanda bana ra'ayi yanzu an
dena auran dole idan kace za kayi min hakan zai janyo matsala babba.
Numfashi ya sauke kafin ya tallafo fuskarta, ya sanya hannu yana share mata hawaye
rarrashinta yayi da fadin tayi shuru suyi magana ta fahinta.
Da 'kyar ta iya dakatar da hawayen dake zuba, ta zuba masa idanunta dake cike da fargaba
burinta kawai taji abinda ke bakinsa.
Babu alamun wasa a tattare dashi yace." Wannan shi ya nuna min da cewa baki da matsaya kin
dauki maganata a banza ace duk a cikin mane ma auranki baki da gwani wanda kike ganin zai
zama abokin rayuwarki, wannan karon ba zan tausaya miki ba, domin ni na haifeki amma na
gaji da ganinki a haka babu aure, tunda har na baki dama kika watsar to ni ina da wanda nake
ganin ya dace dake wanda kuma nake da tabbacin cewa idan na bashi auranki zai rike min ke
da gaskiya da Amana, wannan hukuncin nawa babu wanda ya isa ya janye shi ZINATU
mutukar ni na haifeki to baki da mijin aure wanda ya wuce takwarana UMARU ina nufin yaron
nan daya cece rayuwarki a daji a kwanakin da suka wuce shine wanda na za'ba miki a matsayin
mijin aure, kuma na sheda masa kyautar da nayi masa a ranar suka dawo dake gida, shi din ya
kuma tabbatar min da cewa ya kar'ba kyautar da nayi masa saboda haka kada ki bani kunya ko
kiyi jayayya da umarnina, insha Allahu nan da wata biyu auranku zai tabbata da ikon Allah."!
Wani irin bugawa! gabanta yake kanta yana juyawa! tunda ya fara maganar ta nemi yawu ta
rasa a bakinta! wani rikitaccen yanayi ta shiga wanda ta kasa fassarashi! kuka take ta
gayyatowa amma fafur! yaki amsa gayyatarta idanuwan ma soyewa sukayi sai wani dan banzan
zafi suke! jijiyar idon data kanta sun had'u sun d'aure guri daya wanda hakan ya janyo mata
mugun ciwon kai irin na 'bari guda, sama-sama takejin maganarsa a lokacin da yake bata
umarnin tafiya.
Jiki a masifar sanyaye ta iya kai kanta dakinta, kawai ta zube kasan kafet tana janyo numfashi
da kyar! ke kace ita din mai jinyya ce wacce ke fama da cutukan dake da ala'ka da numfashi.
Wai ace kamar ita jinin saurata gaba da baya, sannan kuma bata rasa komai ba na matantaka
ba, Matar manya manyan mutane masu kudi da mu'kamai! aka dauketa kacokan aka bawa
wani ma'kaskanci kyauta! mutumin data riga ta raina masa hankali, bashi da komai na rayuwa!
bak'auye dashi, wanda ko direbanta be kai matsayi ba amma wai yau shi mahafinta ke ikirarin
bawa auranta, koda wasa ba tayi tsammanin hakan na iya faruwa ba! har yanzu ta kasa gano
dalilin da yasa mutane suke k'aunarsa! a'iya nazari da tunaninta, ta fahimci cewa jarumtarsa ce
take kawai ke burge mutane.......Wannan shine babban dalilin da sanya mahaifinta yin sha'awar
bashi ita a matsayin matar aurensa, tabbas kuwa idan ya sake akayi auran nan to zai gane
shayi ruwa ne a hannunta, domin sai ta nuna masa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane,
sam-sam! ba zata yarda wannan karan ya samu nasara a kanta ba, babu ruwanta da
jarumtarsa! tunda a zahiri ta fishi komai, to dole shi zai rusana mata!!!!
*TURKASHI!!*
*Tofah! yanzu za'a fara wasan ko ya zaman auran nasu zai kasance oho? ni ban san ma
me zance muku ba, amma dai muje zuwa..............!*
*Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, don darajar Allah da Annabi idan kin san ba siya za
kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min maganaí ½í¹í ¼í¿»*
*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp
da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number....
22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*