Showing 3001 words to 6000 words out of 47415 words
Chapter 2 - GOJE part 1 By Binta Umar Abbale-1.pdf
izzah! isa!
jiji da kai maganar abinda ya shafi addini bata san komai ba tafi karfi bangaran boko gami dabin
dabi'ar 'ya'yan nasara.
*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*í ¼í¿¹
í ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURNí ½í±‘í ½í²«_)
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONí ½í¶Šï¸í ½í³š_*
_____________________
FREE PEGE
_Ina mika sa'kon ta'aziyya ta ga al'ummar musulman duniya baki daya, Na babban rashin da
mukayi, hakika ba zuri'ar Malam kadai ne sukayi rashi ba duk duniya ne, muna rokon Allah ya
jikin Malam Ahamad B.u.k (Bamba) Ya sanyashi cikin Aljanna madawwamiya Allah ya kyauta
namu zuwan bayan tasuí ½í¹_
*9&10*
Ya jima yana kokarin kawar da yanayin daya yake ciki amma abun ya gagara! yakan zama
sakarai mara dubara a duk sanda irin wannan yanayin zai shiga jikinsa, gabadaya wayo da
dubararsa nemarsu yake ya rasa, jikinsa ya takure guri daya, yana jin wani irin sanyi tare da
tashin tsigar jiki. Ba da son rasa ba ya juya kanta, yaga tana wanke fuskarta da ruwan daya
ajiye,
Asuwaki ya mika mata tabi asuwakin da kallon banza kafin tasa hannu a wulakance ta karba,
duk da asuwakin sabo ne sai da ta wankeshi sannan tasa a bakinta, dauke kansa yayi yana
girgiza kai ya lura da yarinyar kyankyaminsa take, a tunaninta ko yasa asuwakin a bakinsa.
Wani buhu ya janyo ya dauko wasu mangwaro masu nuna manya guda uku, ya wanke tas
karamar wuka ya zaro daga jikinsa ya mika mata mangwaron da hade da wukar.
Hannu na rawa ta kar'ba yawunta na tsinkewa, bala'in yunwa takeji dama.
Kafin tayi amfani da wukar sai data tasa ruwa ta wanke duk da tana ganin acikin gidanta ya fito
da ita amma bata yarda da tsabtar duk wani abu da zai fito daga jikinsa ba.
Inda Allah ya taimkashi, kayan dake jikinsa masu kauri ne wannan dalilin ya hana girmanshi
fitowa amma a zahiri gabanshi yana tsaye kyam! sama da awa daya da rabi yaki kwanciya duk
da 'yan dabarun da yayi abun yaci tura, sa'i da lokaci yana shiga irin halin amma na yau yafi
muni.
Itacuwa ya had'a ya kunna wuta ya zauna yana gasa jikinsa duk a kokarinsa na ganin ya kawar
da abunda ke damunsa.
Ita da take zaune ba tsirara ba ba kuma mai suttura ba, ta yun'kura ta mike da kyar take tafiya
har ta cimma inda yake jin zaune.
Zata zauna ya daga mata hannu, ba tare da ya kalleta ba yace."Ki koma ki zauna a inda kike ko
kina bukatar wani abu ne."?
Hararsa tayi tana murguda baki kafin tace."Naga kana shan dumi kai kadai shiyasa nazo nima
ina bukata.
Tana maganar tana kokarin zama kusa dashi.
Tun daga sama har kasa yake bin ta da kallo, har ta samu guri ta zauna tana kara hannuwanta
a jikin wutar, yanayin zaman da tayi yayi masifar jefashi cikin tashin hankali, inda ita kuma a
wautar ta bata kawo komai ba tana ganin ai da tun farko yayi niyyar lalata da ita to da yayi
amma ta lura sam ba wannan ne a gabanshi ba.
Ya dinga kokarin dauke kansa da kanta amma Shaidan yana kara 'kawata masa suffarta, gaza
dauke idanuwansa yayi daga kanta, ya cigaba da satar kallon wasu guraran da suka bashi
sha'awa a jikinta, amma be yarda ta fahimci halin da yake ciki ba.
Sun jima a haka babu wanda yayi magana a cikinsu, kafin suji bushe-bushe na kusanto inda
suke da alama yaranshi ne suka dawo daga farauta.
Ta kalleshi a lokacin da ya tsirawa shara'ban kafarta ido. Tayi saurin gyara kafafunta tana watsa
masa harara.
Ya sauke ajiyar zuciya tare da sake tamke fuskarsa cike da bada umarni yace."Ki tashi ki bar
gurin nan."
Yanda yayi maganar babu wasa yasa ta tashi tsaye, yayi saurin dauke kansa, kawai sai taja
masa tsaki ta wuce!
Abin ya bashi mamaki mutuka! ya girgiza kai tare da nazari da tunanin matakin da zai dauka a
kanta
Gurin gabad'aya ya rikice da gangi da bushe-bushe duk a sakamakon dawowarsu, hannu tasa
ta toshe kunnuwanta takaici kamar ya kasheta, da yake da akwai hasken wutar daya kunna
tana kallo suka dinga firfito da matattun macizai da mesa tare da sauran dabbobin da suka
farauto, Abun ya dinga bata mamaki ganin sun daga wani lafcecan maciji sun sanya wuka mai kaifi sun
rabashi gida biyu, suka tsire shi a jikin wani itace kafin su barbada masa gishiri da wani abu ja
da alamar manja ne sannan suka sanyashi a wuta suna gasawa.
Hankalinta yayi bala'in tashi, karni da wari duk ya cika gurin zuciyarta ta dinga hantsilawa
saboda tsabar kyankyamin abunda suke.
Tana nan zaune tana kallon ikon Allah suka gama gasa maciji nan wanda bai sani ba sai yace
bushashshan kifi ne suka fara yankarsa da wuka suna ci hankalinsu a kwance.
A gurin ta dinga kyalaya amai duk sai da ta amayo mangwaron data sha, taja gefe guda tare da
toshe hancinta.
Sai da dare ya tsala sosai sannan kowa ya nemi makwanci, yana sanya kafarsa yaji ya taka
abu cabal! yayi saurin kunna fitilar hannunsa yana dubawa, aman da tayi ne duk ya bata kan
shimfidar, tana rakube a gefe guda bacci ya dauketa.
Yaji takaicin bata mai shinfida da tayi yaja tsaki tare da samun ruwa ya wanke kafarsa ya dawo
yana tunanin inda zai sanya hakarkarinsa ya kwanta ba don bacci ba.
Kusa da ita ne kadai babu kazanta kuma baya so ya kusanceta gudun abinda ka iya zuwa ya
dawo, domin har yanzu yanayin be bar jikinsa ba.
Kawai sai ya yanke shawarar zuwa gurin yaranshi domin samun matsuguni, tsakaninsu babu
wata tazara mai tsayi kuma yana da tabbacin babu abunda zai sameta, rigar jikinsa ya cire ya
rufa mata a jikinta sannan ya bar gurin.
Da yake baccin ya dauketa a cikin tsoro da fargaba yasa ta dinga munanan mafarkai da namun
daji sun biyo ta zasu cinyeta sai ta farka a gigice! tana kwalla ihu! da fadin." Kura ce! kana
inaaaa! *GOJE!!* zata cinyeni."!
Gabadaya suka tashi tsaye da shirin ko ta kwana, amma ba subi bayansa ba, shine ya cimma
inda take tsaye sai rawar dari take a tsaye.
Yana zuwa ta rungumeshi, tsam! tsam! tana wani irin kuka da fadin." Kura ce ta biyo ni."!!!
Ya dinga nanata mata addua a kunnuwanta har ta samu nutsuwa, ya zaunar da ita, amma fafur
taki zama wai dole sai sun zauna tare. ta rike masa hannu katamau!
Shi kam taushin hannunta da dumin da yake shine yayi masifar sanyayyar masa da jiki,
Babu zato babu tsammani ta janyoshi duk karfinsa, sai ya tsinci kansa a zaune a kusa da ita,
yayi mamakin hakan mutuka
A maimakon ta saki hannunsa, tunda yana kusa da ita, sai ma ta sake shigewa jikinsa, tana
boye fuskarta a kirjinsa dake waje babu riga sai singlet.
Tsigar jikinsa ta tashi gabadaya ya rasa nutsuwarsa, so yake yafi karfin zuciyarsa amma ta
kanainaiyeshi, ta hana shi tsira da mutuncinsa.
Haka suka wanzu har asubah! tana makale a jikinsa, ta hanashi sakat daga yayi motsi zata
zabura! ta matseshi, tana goga masa sassan jikinta.
Da kyar ya iya furta magana." Sai ki sakeni haka asubah tayi babu wata dabba da zata zo ta
cutar dake."
Kanta ta cire daga kafardarsa tana kallonsa da jajayen idanuwanta tace."Kayi wa Allah da
Annabi ka hada tawagarka mu bar dajin nan! duk abunda kuke bukata mahaifina zai baku kada
ka cutar dani ko kuma wata dabbar tayi sanadiyar rayuwata.
Ya jima yana mamakin furucinta ashe tana da hankali irin haka.
Sai shi ma yayi mata magana irin ta samu hankali yace."Bana bukatar komai a gurin mahaifinki,
kuma ki daina dora zarginki akaina ni ba 'barawo bane Allah ya nufeni ne da na taimaka miki."
Yana kare maganarsa ya nufi bakin kogi da asuwaki a hannunsa, kallo ta bishi dashi har
kurewa ganinta kafin ta girgiza kai tana tunanin wani abu akansa.
Sai da gari yayi haske sosai sannan ya dawo gurin dunga nesa yake hangota a kwance
rigingine, ta dogare kafafunta a kasa cinyoyinta a waje amma ta suturta gabanta, saurin dauke
kansa yayi har ya karasa gurin be sake kuskuran kallonta
Ya dauki rigarshi data cillar masa ya rufa mata a jiki, baya so yana ganin abinda zai tayar masa
da hankali.
Ai da sauri ta cire rigar ta cillar da ita can tana ya mutse fuska, zaune ta tashi tace."Idan zaka
kwana kana rantsuwa cewa kai ba dan ta addah bane ba zan yarda ba wallahi."
"Ke baki isa nayi rantsuwa a kanki ba, kuma idan kika sake kirana da wannan sunan zan nuna
miki ta'addanci na."!
Yanda yayi maganar shi ya tsorata sai tayi shuru amma bata fasa yi masa kallon banza.
Ya dauki rigarsa data jefar yana girgiza kansa ya rasa wace irin yarinya ce me manta alkairi ina
laifin wanda ya suturta ka.
Rigar ya sanya a jikinsa, can kasan makoshi tace." Kazami kawai." Yaji abinda tace amma be
tanka mata ba, ya juyo, tayi saurin dauke kanta, janyeta yayi kan daddumar ta fadi kasan gurin,
ba tare da ya saurareta ba ya bar gurin da daddumar a hannunsa.
Ta ciji yatsa tana bin bayansa da mummunan kallo.
Daya daga cikin yaransa ne ya karbi daddumar ya wanke tas ya shanya kan wata bishiya.
Ya umarcesu da suyi shirin fita shima tare zasuje don baya tsammanin zai zauna da yarinyar
tana 'bata masa rai bayan masifar data jefashi a ciki.
Be saurareta ba ya hada kan tawagarsa suka fice ba tare data sani ba, hankalinta ya kai
kololowa gurin tashi, lokacin data fahimci ita kadaice a cikin dajin sai ta raina kanta da wayonta,
tana kuka ta kama hanya ta cire tsoro da fargaba kokarinta ya za'ayi ta fitar daga kanta daga
cikin masifa.
Aikuwa kanta ne ya juye! a maimakon tayi baya sai ta dinga gaba, tana kutsawa cikin dogwayen
bishiyu na kuka da tsamiya nan ta dinga arba da manya manyan birai iyaye da 'ya'yansu,
hankalinta ya tashi, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, gwagwgwan biri! ido sukayi da wani
kato ya tsufa sosai! yana zaune duguzun-duzugun jikin wata narkekiyar bishiyar kuka!
Da baya da baya ta farayi kafin ta juya a sukwane tana falfala gudu hade da kiran sunansa
*GOJE!!* shi kuwa Gwaggon birin nan dariya yayi da ya fahimci tsoronsa take sai ya kudiri
aniyar tsokanarta, ya fara bin jikin bishiyu yana tsalle yana mata dariya har ya dura a gabanta.
Zubewa tayi tana daga masa hannu yawun bakinta ya bushe "Don Allah kayi hakuri! wayyo
Allah na wayyo na shiga uku kuka ta dinga yi hawaye da majina sunyi kaca kaca da fuskarta.
Daya bayan daya suka kewayeta iyaye da kakanni! da alama sassaninsu ta shigo bata sani ba.
Kanta ne ya dinga juyawa a gurin kafin ta fadi, suma tayi, ba tare da bata lokaci ba wannan
dattijon birin ya dauketa yasa a kafada, kataf-kataf ya fara tafiya da ita iyalinsa suka rufa masa
baya.
Dabaru irin nasu sukayi mata ta dawo hayyacinta koda ta bude ido ta ganta a tsakiyarsu, sai ta
mayar da idonta ta rufe jikinta sai karkarwa yake, su kuwa suna zazzaune sai cin manya manya
ayaba sukeyi suna gurnani da alama zantuka suke a tsakaninsu.
Sai gefin magariba suka dawo, hankalinsa ya tashi lokacin daya duba sama da kasa be ganta
ba,
Dajin ya shiga yana yana sasssare mattatun itatuwan da suka cika gurin, ya fito da sarewa
yana busawa tare da cigaba da ratsa cikin dajin.
Zumbur! ta tashi zaune jin busar sarewar na kusanto gurin da suke, daga can nesa ya tsaya
yana hango tawagarsu tana tsakiyarsu sai kace 'yar tsana saboda kankanta.
Kai tsaye gurin ya nufa yana cigaba da busa sarewar dake bakinsa, tsakiyarsu ya shiga yayi
wani irin tsugo gaban dattijon birin nan yana me cigaba da busa abinda ke bakinsa,
Murmushi yayi ya dora hannunsa me cike da gashi da farata zako-zako a hannunsa a saman
kansa, kafin ya cire ya nuna masa ita, yana gurnani!
Kansa kawai ya girgiza ya nufi inda take, hannu ya mika mata ta mike tsaye kafafunta sai
kyarma! suke a haka suka bar gurin.
Saboda fargaba da mutuwar jiki yasa gabadaya kafafunta sukayi sanyi da kyar take iya jansu,
bakinta ya mutu murus! tsabar tashin hankali binsa kawai take duk inda yaja ta, b'angaransa
kuwa yana sane yaki goya ta saboda tayi bala'in bashi haushi, ya tabbata idan wata dabbar ce
sai yasha mutukar wahala kafin ya samu damar fito da ita daga cikinsu idan sun barta da rai
kenan.
Wannan Gwaggon birin sun saba dashi sosai duk sanda zasu shigo farauta dajin basu da
matsala dashi da iyalinsa, wani sa'in ma har kyautar ayaba mai yawa suke basu.
Cikin mawuyacin hali suka karasa gurin da suka yada zangon ya jefar da ita ta fadi kasan gurin,
zaune ta mike tana kallonsa ya juya mata baya gabadaya jikinta yayi sanyi domin ba tayi
tsammanin zata cigaba da rayuwa ba.
Cikin wani irin amo! taji maganarsa. "Kada ki kuskura ki sake barin gurin nan dana ajiye ki
domin kuwa yin hakan na barazana da rayuwarki, babu inda yake da tsaro a cikin dajin nan fiye
dana nan gurin, idan kika sake fita yawo to ba zan sake yunkurin ceto rayuwarki ba, yau
kwananmu biyu sai kuma munyi sati guda kafin mu koma gida don haka ki kiyaye rayuwarki kibi
umarnina kuma mutukar kina bukatar cigaba da rayuwa.''
Kuka ta fashe! dashi ra rarrafa ra rike kafafunsa, " Kada kace haka mana! ka tausaya min a
matsayina na mace mai rauni ka fitar dani daga wannan dajin ni ba zan iya sati a guda a cikin
wannan tashin hankalina ba, wallahi komai kake bukata mahaifina zai maka ka taimakawa
rayuwata."
Yanda take kuka tana rokonsa sai ku dauka mutuniyar kirki ce, haka take dama a duk lokacin da
zata ganta cikin wata ukubar takan gigice ta saduda amma daga an kwana biyu sai ta koma
baya.
Kafafunsa ya cire ba tare daya ce mata komai ba ya bar gurin, Hakan da yayi ya 'bata mata rai!
sai kawai ta kullaceshi a ranta, ta kuma kudiri aniyar wani abu a ranta zata tayar masa da
hankali wanda zai daga
Masa hankali dole ya kaita gaban iyayenta........
*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da
wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Katin Mov ko airtal
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*í ¼í¿¹
í ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶ºí ½í°•â€í ¾í¶º
_(SADAUKI OMAR RETURNí ½í±‘í ½í²«_)
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONí ½í¶Šï¸í ½í³š_*
_____________________
FREE PEGE
*5&6*
Kwanciyarta da kamar mintina goma bacci ya kwasheta sai dai baccin beje ko'ina ba dafin
kunamar ya fara yawo a sassan jikinta, a gigice ta tashi zaune gabadaya jikinta ya dauki rawa
ga wani irin gumi da yake karyo mata! rikicewa tayi ta rasa inda zata sanya ranta taji dadi.
Gurin ya karaso, yana tambayarta, abunda ke damunta, da kyar ta iya bude baki tayi magana.
Bece komai ba ya bar gurin, halin da take ciki besa ta bishi da kallo ba, har ya dawo kanta
yana kasa wannan karan kuka ya samu ta nayi, ta dan bashi tausayi kadan, amma bai nuna a
fuska ba.
Ya bude gwangwanin Milo din dake hannunsa, wani abune mai duhu a ciki, da alama magani ne
aka kwaba da mai, ya kalleta da fadin." Zaki iya nuna min gurin da kunamar ta cijeki."?
Wani irin kallo ta tsawa masa, ta dauke kanta, ranshi ya baci ya daka mata tsawa da fadin"
Taimakonki fa zanyi kike min kallon banza kin san wanene a gabanki kuwa."?
Hannu tasa ta goge fuskarta ta daure zugin dake damunta, cikin rashin tsoro tace." Sanin
wanene kai bai dameni ba, na dai san ka amsa suna biyu wato *barawo* kuma dan *ta'addah."!*
Ya tsira mata idanuwansa masu kaifi! yana mamakin maganarta, *'barawo kuma d'an ta'addah!*
tunda yake a duniya babu wanda ya ta'ba kiransa da sunan *barawo* sai ita, kalmar *d'an
ta'addah* kuwa yana ji tana yawo a gari a kansa.
Ya girgiza kansa cikin yanayin maganarsa yace." Wannan shine karon farko da aka ta'ba
kirana da wannan kalmomin a gaban idona, kiyi kokarin kiyaye harshenki kafin ki bar hannuna,
*GOJE!* nake ba'a kawo min wargi duk tsagerancinki ni zan daidaitaki.
Ta kalleshi a wulakance kafin tace."A hakan? babu tarbiyar! ka fara daidai ta kan............'Barin
makauniya yayi ya fuskarta, a take hancinta ya tsinke da jini, tasa hannu ta dafe, jiki na
kyarma! take kallonsa, fuskarsa ta rikide da zallan bacin rai!
"Zaki janyo nai miki mugun rauni a gurin nan, babu ruwana da kowace masarauta kika fito, ki
sani ba'a nuna ni da yatsa ban karya ba! sannan ba'a jayayya dani, kuma bana magana biyu,
*Billahil-lazi hurramanu!* duk sanda kika kara fadin wata