Showing 3001 words to 4595 words out of 4595 words

Chapter 2 - FAHIMA BOOK 3 part 3 END Complete by Takori Kabara .pdf

Amrah ba ta da laifi ko me za
ta yi, laifi ne ka yi mata, sai ka karba a wuce wurin kawai".

Uwais ya yi shiru bai sake ce mata uffan ba, amma a cikin ransa ya janye sakin da ya yi wa
Amrah.

Sun kwana da niyyar washegari Uwais zai tafi Abuja bikon Amrah.
Don haka Fahimah da wuri ta tashi ta sallame shi da dukkan abin da zai bukata. Karfe
takwas na safe Uwais ya kama hanyar Abuja cikin motarsa Elantra.

A hanya ne ya kira Jabeer, yana dagawa kafin Jabeer ya ce komai ya ce,
"Friend, I'm on my way for biko".
Jabeer ya yi ajiyar zuciya, don ya san mawuyaci ne Daddy ya sake sauraron Uwais a kan
batun Amrah. Amma bai fada masa hakan ba, don ya sani kullum Uwais mutum ne mai sa'a.
Auren Amrah ma da ya yi ba karamar sa'a ya taka ba, don haka yanzun ma ba shi da tabbacin
ko Alhajin nasu zai sauko daga fushinsa tunda ya yi tattaki ya zo don ya amsa laifinsa. Ya isa Abuja wajejen azhar sannan ya karkata kan motar sa zuwa Apo.
Daga Amrah sai Mama a gidan yau Aunty Wasila ba ta zo ba. Maigadi ne ya shigo ya fadi
cewa Uwais mijin Amrah ya zo yana waje.

Mama ta dubi Amrah don ganin reaction dinta sai ta ga fuskarta kamar an mata bushara da
zuwan mala'ikan daukar ranta. Sosai Mama taji dadin hakan, wannan ya nuna Amrah ta dauki
zugar da suke kwana da yini yi mata.
Dare da rana ba abinda familyn Amrah ke yi sai zugata akan rabuwa da Uwais, in har
tana so rayuwar ta ta gyaru. Yau da gobe aka ce 'zuga' abu ce mai matukar illah, in bata dau
wata ba tana daukar wata.
Don haka auren Uwais ya fucewa Amrah a ka, tana ganin gara ta hakura ta huta akan
taje ta yi zaman kishi da Fahimar da bata san Yaya tsakanin ta da Uwais yake ba har yau, tunda
su munafukai ne.
Da farko ma cewa tayi da maigadin ya je ya ce bazata zo ba. Mama tace.
"Ba za'ayi haka ba Amrah, gara kije ki san matsayin ki, in yin-yin in barin-barin". Sannan
ta yi kwafa tace.
"Wannan Uwaisun, ya gama rainawa mutane hankali. Har yana da 'guts' din kwaso
doguwar kafarsa ya sake kawo mana nan?"
A fusace Amrah ta zari mayafi ta fita, a dakin da suka saba zama lokacin da yake zuwa
zance acan ta sameshi.
Uwais na tsaye har lokacin bai zauna ba, da hannuwa zube cikin aljihu, yana zuba idon
ganin ta inda Amrah zata bullo, zuciyar sa cike da waswasi. Ba jimawa Amrah ta bayyana a
gaban sa cikin wata fuska da wani yanayi irin na kamar dadai duniya bata taba sanin sa ba.
Daga bakin kofa ta tokare ta tsaya, Uwais ba ya son tuna yanayin da ya ga idanun
Amrah a wannan lokacin; babu komai cikin su sai tsananin tsanar sa zallah.
A hankali yayi tattaki zuwa gaban ta, yana nan har yanzu a Uwaisun sa data sani mai
kayatar da zuciyar ta, but he lose his magical appearance of love and trust. Dan burbushin son
da ya rage a cikin zuciyar ta yanzu ba zai hana ta komai a rayuwa ba.,
Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna kamar zakaru, kowanne striving yake da zuciyar
sa don son gane cewa soyayyar tana nan ko ta ragu? Ko kuwa gabadaya ta kama gaban ta? Ta
Uwais tana nan, amma ta ragu 50%. Ta Amrah na nan, amma bacin rai, kishi tsana da tunanin
betrayance din da Uwais yayi mata ya kashe shi da 70%. Sauran kashi talatin din da ya rage, Amrah ta sabya shi matsayin sabo da juna, kuma
na tunani; zata iya overcoming dinsa da zarar ta koma Malaysia.
"Ina fatan ka taho min da takarda ta UWAIS SHAGARI?"
Amrah ta fada kai tsaye, da sunan da bata taba kiran sa da shi ba.
Murmushi yayi, wanda da gani iyakar sa fatar bakinsa, sannan cikin karfin hali irin na
maza gogaggu da suka yarda da kan su, yace.
"Amrah ko gaisuwa babu? Na dauka tsakanin mu ya wuce haka?"
Wani irin kallo Amrah ta yi masa, tana mai tariyo kalaman data ji yana fadawa wata
mace ba ita ba a waya, watan ma da ya ce 'yar aikin gidan su ce. Kalamai masu tsauri da matar
ka ta sunnah kadai ya kamata ka iya gayawa.
Kuma in a gaban idon ta ne ya nuna ko son zanen yarinyar baya yi. Wanda ke iya fadar
wadannan tsauraran kalaman a waya, a fili wace irin soyayya yake aikatawa a gareta? Allah
kadai ya sani.
"Ban fito nan don kayi min dadin baki ba, na fito ne in karbi takarda ta, domin na yanke
shawarar dana ke ganin tafi amfani a gare ni. Itace rabuwar auren mu".
Da kyar Uwais ya zuki numfashi ya fesar.

"Ko rabuwar kika zaba Amrah, yana da kyau ki saurari kalaman baki ba, kafin ki yanke
kowanne irin hukunci, ban ce lallsi ki yarda dasu ba, amma inada hujjojina, tunda dai soyayya
ce da yarda suka hada mu ba akasin su ba".
Amrah tayi wata irin dariya tace "soyayyah........ Uwais? Really? Does it really exist a
duniyar nan kuma a zamanin nan?"
Uwais ya shafo lallausar sumar kansa cikin damuwa yace "It really does, and i still love
you Amrah. Kamar yadda nake son Fah-himah itama. Amma ki yarda cewa aure na da
Fah-himah wata rubutacciyar kaddara ce daga Allah wadda tafi karfin na tsallake ta....".
Tiryan-tiryan ya soma bata labarin Fahimah, tun daga lokacin da Ammi ta dauko ta daga
'orphanage', kuruciyar su, yadda ya rayu yana uzzura mata, da goranta mata halitta, zuwa
haduwar shi da ita Amrah a gidan Jabeer.
Yadda Ammi ta kafe in bazai auri Fahimah ba itama Amrah ba zai aura ba. Artabun da
Ammi ta sha da shi akan Fahimah, kafin ya yarda su tafi Ikko tare.
Ya takataita zancen sa da cewa. "A wannan tafiya da nayi tare da Fah-himah, a dalilin
rashin zaman ki wuri guda, al'amura suka sauya beyond my capability to escape. Kada ki manta
ni namiji ne kuma mai cikakkiyar lafiya kamar kowanne dan adam, wanda Allah ya baiwa damar
auren abinda yayi masa dadi daga daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hurhudu. Ko Ammi bata aura min Fahimah ba, a irin rayuwar da kika zaba mana, dole in kara
aure. Don haka Amrah bai kamata ki ga laifi naba don na so Fah-himah at this expense tunda
aure ne na sunnah a tsakanin mu, kamar yadda yake tsakanina da ke.
Laifi daya na san na yi muku Amrah, na rashin gaya muku tun farko, sai na gina neman
aure ne a lullube, abinda ya kamata in yi a wancan lokacin shine tun farko in fada, cewa ku biyu
za'a aura mini a lokaci guda, da ke zabin rai na da zabin mahaifiyata, in ya so in kin ga zaki iya
aure na a haka ayi, in kin ga bazaki iya ba na hakura. To amma Amrah idanuna sun rufe, na kurumce na makance a dalilin son ki, burina
kawai na mallake ki. Ina tsoron duk wani abu da zai shiga tsakanina da wannan burin nawa. Na
san

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login