Showing 1 words to 3000 words out of 4595 words

Chapter 1 - FAHIMA BOOK 3 part 3 END Complete by Takori Kabara .pdf

FAHIMA
BOOK 3 END



A firgice Uwais ya ce, “Kada ki yi mana haka Ammi, Fahimah ba ta da kowa a kasar nan sai ke,
ni ma ba ni da kowa sai ke Ammi, we need you behind us, burina shi ne in mun koma Abujan ki
dawo gidanmu ki zauna tare da mu Ammi”.
Ammi ta shafo lallausar sumar kansa, ta ce,
“No Uwais, ku yi hakuri ba zan bi ku ba, I’m going back to Khartoum. Dukkanku kun kai
munzalin da za ku tsaya da kafafunku ku tara iyali ku yi musu tarbiyya irin wadda ku ka samu.
Ku yi hakuri ina Sudan ina Najeriya tunda kullum akwai jirage masu zuwa? Sannan ga waya, ko
tari ku ka yi zan jiyo ku ta cikin waya”. Ammi ba ta san yaushe Fahimah ta fito ba, ta kuma tsinkayi karshen maganganunta na
komawa Sudan. Ai sai ta dora hannuwa biyu a ka ta saka kuka wiwi.
Ta fada jikin Ammi tana ta yi, Ammi na lallashinta tana fadin, “Ai da saran lokaci ba gobe ba
zan tafi ba, na ce sai kun nabba’a a waje guda tukunna”.
Fahimah ta ce, “Ammi lallai sai na amsa sunan marainiyar da gaske? Idan ina ganinki kullum
manta ko ni wace ce nake, idan ki ka tafi ki ka bar mu zan tabbata marainiya, rayuwata ba za ta
taba zama cikakka kuma mai dadi ba kamar da”.
Ammi Safeeyyah na murmushi, ta ce, ‘Bayan ga ki ga Uwaisun naki? Uwaisu sarkin soyayya,
baban soyayyah?”
Kunya sosai Fahimah ta ji, ta sunne kanta a jikin Ammi tana cewa, “Kai Ammi". Uwais waya
yake amsawa don haka bai san me suke cewa ba”.
Ammi ta ce ta kwashe kayan nan duka ta tafi da su dakinta tsarabarta ne in ji Uwais.
Fahimah ta ce, “Ammi ai ban ga naki ba”.
Ammi ta ce, “Na tsufa da lesussuka Fahimah, don haka na bar miki”.
Ta sanya hannu ta dauki atamfa Vlisco guda biyu ta aje a gefe, ta ce, “Ga shi na dau wannan
Allah ya yi muku albarka”.
“Ammi zan je na kwanta. Na gaji sosai”.
Ammi ta ce, “Fahimah kin gyara misni dakin in ce ko?”
“Na gyara Ammi, har maganin sauro na fesa kada sauro ya ciji dan kasar sanyi daga
dawowarsa”.
Dariya Uwais ya yi ya wuce yana kada kai, ya ce, “Kin ci bashi kuma za ki biya”.
Ammi ta ce, “Kayya da ba ki fesa ba, da kin barshi ya gane cewa ya dawo kasar haihuwarsa,
kowa ya bar gida ai gida ya bar shi”.
Fahima tana dariya ta ce, “Kai Ammi”.
Ya wuce ya barsu suna ta barkwancinsu kamar jika da kaka.
Da wuri ya kwanta don da gaske yake ya gajin. Da asubah da ya dawo sallah daga
masallacn kusa da su ya ce, bari ya tada Fahimah ta yi sallah. Don wasu lokutan tana da
nauyin barci.
Ilai kuwa ya same ta ta yi dai-dai tana barci da wata ‘yar kyakkyawar nighty a jikinta wadda
ita da babu duk daya. Uwais ya runtse ido a hankali amma sai ya ce bari ya mata mugunta
tunda ta gota lokacin sallah.

Toilet ya je ya debo ruwa a kofi mai sanyi da shi ya zo ya yayyafa mata. Ai kuwa ba shiri ta
mike a razane. Ganin shi ne ta shagwargwabe fuska, “Kai Yaya Uwais, wannan ai mugunta ce”.
Ya ce, “Yanzu wannan barcin da ki ka ware minshari kina yi kin yi sallah ne?”
Da sauri ta mike tana fadin, “Ya salam”. Ta yi toilet, shi kuma ya fita zuwa dakin Ammi.
Bisa sujjadah ya same ta tana lazimi, ta jima da idar da sallah. Ta ce, “Uwais har ka dawo
masjid?”
Ya ce, “Na dwo Ammi sabahul khair”.
Suka yi gaisuwa cikin harshen larabci tana fadin, “Bari in je in tashi Fahimah ban ganta ta
shigo ba”.
“Na tashe ta yanzu tana sallah. Ammi da na yi breakfast zan tafi can UDB (inda yake ginin
Fahimah) in tsaya a kan ma’aikatan nan sai komai ya kammala. Sannan Ammi na tura kudi a
wayarki da za a yi mata kayan daki, duk da ba zama za mu yi sosai ba a sayi komai ya dace a
zuba, don duk sanda muka zo Kano a nan za mu zauna. Sai maganar komawarki Sudan, don Allah Ammi ki barta”.
Ammi ta girgiza kai zuciyarta cike da jin dadin abin da ya yi kuma yake kan yi a kan Fahimah,
mai nuna a karshe ya gama maraba da ita cikin rayuwarsa, ya ba ta matsayi mai girma kamar
ko ma fiye da na Amrah. Don tun saukarsa ba ta ji sunan Amrah a bakinsa ba, Fahhimah…
Fahhimah dai kamar shi ya rada mata sunan. "Kada ku bata ranku a banza, kai ma ka san bana magana biyu, Sudan na koma ta na gama
insha Allahu.
Fahimah na godiyar kayan daki daga Yayanta, wannan ya nuna min Uwais ko babu raina za
ka rike min Fahimah da amana. Kuma da ma ko ba kai Fahimah ta aura ba hakkin kayan
dakinta yana wuyanka. Sai ka yi amai ka lashe abinka”. Ta karasa cikin zolaya.
Cikin murmushi Uwais ya dukar da kai ya ce, “Ammi for the first time ina bada hakurin duk
abin da na yi a baya cikin ajizanci irin na dan Adam. Ammi kin ce watarana zan zo in gode miki
ba ki yi karya ba, yau ga ni gurfane a gabanki ina miko kwandon godiya ta. Kin ce da kaina zan
zo in gaya miki wace ce Fahimah, kuwa ba ki yi karya ba. She’s a darling (ita din abar so ce, kuma sai mai tsananin rabo zai yi sa’ar samunta a
matsayin matar sa. Sai namijin da Allah ke so da rahma. Ammi na I remain loyal, grateful, and I
remain regretful’.
Ammi ba ta san lokacin da ta kama tausasan hannuwan Uwais ta rike cikin nata ba, tana
murmushi ta ce.
“Ban rike ka da komai ba Uwais sai tarin fatan alkhairi, ko babu komai ka yi gaggawar gane
gaskiya kafin lokaci ya kure maka, ka zo ka yi nadamar da ba ta da amfani. Yanzu kuwa
repentence dinka bai makara ba, ka yi shi a lokacin da ya dace.
Nasiha ta da kai Uwais ita ce, in za ka so abu ka so shi sawwa-sawwa, haka in za ka ki shi,
kada ka zurfafa kiyayyar. Domin Allah shi ne kadai masnain gobe da abin da ya boye cikin
rayuwarmu”.
Uwais ajiyar zuciya ya sauke yana mai AMANNA da kowacce kalma da ke fita daga bakin
Ammi.
Fatansa Allah ya bar masa Ammi. Ya tsawaita rayuwarta, Ya inganta lafiyarta har sai ta yi wa
‘ya’yansa da Fahimah aure.
Wayewar gari ke da wuya ya nufi gidansa na UDB Road, a wannan tafiyar Uwais ba kananan
kudi ya samu ba, don haka akalar ginin ta sauya gabadaya, gini ake sosai na gani a fada. Kafin

ya dawo dama sun kammala komai, yau ya zo ya tsaya ne don a karasa kananan abubuwan da
ba a karasa ba.
Ammi da Fahimah kuma suka tafi zaben kayan daki. Ba yadda Ammi ba ta yi ba Fahimah ta
zabi abin da ta ke so ta ki, ta ce, “Ammi, duk abin da ya yi miki ni ma ya yi min. kin sani kullum
ra’ayinmu yana zuwa daya, don haka ko me ki ka dauka zan so shi”.
(Me ya fi danka ya auri matar da ta san mutuncinka ta ke girmamaka fiye da mijin kansa?)
Ammi Safeeyah ta fada a zuciyarta.
Don haka ita kuma ta zage ta yi wa Fahimah kayan daki na gani na fada, wadanda sai
‘ya’yan gata kadai ke samunsa. Bayan kudin da Uwais ya bayar, Ammi ta zuba nata har ba
adadi.
In ka ga gidan Uwais da Fahimah komai ya yi acan-acan na masu ilmi da iya tsari, babu
almubazzaranci ko kadan, komai da ke dakin Fahimah da kicin dinta mai amfani ne.
Inda Uwais ya sa aka yi mata english kitchen duk wata na’urar saukaka girki ta zamani Ammi
ta saka wa Fahimah.

Don haka a washegari ma bai samu zuwa Abuja ba, kuma ba su samu komawa a ranar da
aka gama komai ba sai washegarin ranar.
Washegarin kuma da asubah Ammi ta ce su tafi, don an fi so a shiga sabon gida da asubahi.

Da daren ranar Fahimah na gaban Ammi kuka kawai ta ke yi, Ammi na hada mata sitturunta
da ke dakin da duk wani abin amfaninta, ita ma dauriya kawai ta ke yi, amma ta gama karaya.
Shekaru kusan goma sha tara ban da zuwansu Lagos da Sudan ita da Fahima ba su taba
kwana ba gida daya ba. Lallai aure ya ci sunansa yakin mata. Ban da shi din, wa ya isa ya raba ta da Fahimarta?
To amma me? Uwais ne mijin. Uwais dinta kwalli daya, don haka Fahimah sauyin muhalli
kawai ta samu, amma tana nan cikin gidanta.
Wannan tunanin ya sa Ammi Safeeyyah ta rage wa kanta damuwa, ta koma tsokanar
Fahimah wai ai yanzu 'yammata sun daina kukan aure. Ita mai auren gata ma auren gida, auren
cikin daki, auren da babu mai raba ta da Amminta.
Washegarin ranar da karfe 5:30am Ammi da Talatu suka raka Fahima har motar Uwais.
Tunda ya dawo masallaci bai koma gidan ba ya yi zamansa cikin mota don ba ya son ganin
rabuwar Ammi da Fahimah. Ko shi da yake namiji ya ji barin gidan a ransa kamar wannan ne
karo na farko da ya fara yin aure. Yanzu ne yake jin barin gidan sosai a ransa, ko don Ammi ta dage ita ma barin gidan za ta yi
oho! Gida ne da ya kunshi tarihin duk wata dabdala ta kuruciyarsu. Ya sabbaba aure mai dimbin
tarihi tsakaninsa da Fah-himah, Fah-himar da ta juya duniyarsa da tunanin sa baki daya.
Talatu ce ta rufe mata kofa don Ammi ba ta iya tsayawa ganin tashinsu ba. Kukan Fahimah
ya karya zuciyarta sosai. Ta koma cikin gida cike da kewar Fahimah amma tana mai hamdala a
zuciyarta. Yau ta sauke babban nauyin da burin kowacce UWA ta sauke shi, sai ta koma binsu
da addua kala-kala. Uwais ya kashe motar a harabar flat dinsu, wanda aka yi wa rufi da dark blue roofings. Bai
cika girma sosai ba, amma ya tsaru iyakar tsaruwa daidai bukatar kowanne mai rufin asiri. Duk
abin da Uwais ya samo a course dinsa na World Bank a gidan Fahimah ya kare.

Amma ji yake inda yana da abin da ya fi hakan zai yi, don Fahimah da yayanta masu zuwa a
gaba.
Ya kashe motar a inda aka tanada don adanata, sannan ya mika wa Fahimah kamsassan
hanky dinsa,
If you are done with the cry sai ki goge hawayen mu shiga da kafafun dama, Im sleepy.
Farin cikin yau zan mallaki Fah-himah by my side a matsayin uwargida a duniya da lahira, bai
barni na runtsa jiya ba.
Burina da fatana kawai gari ya waye in shaida wannan rana mai nisan zuwa kamar eternity.
Ki shigo gidanki cikin aminci, so da kauna da yardar mijinki. Na yarda da ke Fahimah na
amince da ke matsayin uwar yayana.
Ki yi hakuri da ni a inda na kuskure don yanzu ne rayuwarmu ta hakika za ta fara. Rayuwar
da duk son da ake wa juna sai an yi hakuri da 'flaws' din juna.
Sabida yanzu ne zan koma Uwaisu ki koma Fah-himatu, not Uwais and Fahimah sarauyi da
budurwa".
Maganarsa ta karshe ta ba ta dariya duk da hawayen da ke fuskarta sai da ta murmusa tana
share su da hanky din da ya ba ta, Uwais ya bude suka fita, sai ya zagayo ya sakalo hannunsa
a kugunta, a haka suka shiga falon farko na gidan.
Fahimah ta ga cewa in ta tsaya kallon gidanta wanda ko a mafarki ba ta taba yin na mallakar
kwatankwacinsa ba, to kuwa Uwais zai ce 'yar kauye futuk ya aura. Gara ta adana kallon zuwa
sanda ba sa tare.
Soyayyar yau daban ta ke, domin ta zarce ta birnin Ikko wannan ta nutsuwar zukata ce. Mai
licence, sannan ba hobbasar Uwais shi kadai ba, Fahimah ta agaza ta taimaka fiye da zatonsa.
Shi da kansa ya yi mamaki domin ta sakar masa komai fiye da koyaushe. Ya ce,
"My wife today deserves an accolade!"

Kwana uku kenan suna barzar amarci kamar ba za su gaji ba. Takardar sakin ma bai san
inda ya jefa ta ba. Tsabar yadda Fahimah ta tafi da dukkan nutsuwarsa, ta zamo silar wani irin
'life contentment' ga rayuwar Uwais. Gabadaya ya mance da Amrah.
Da yammacin yau yana daga can bayan gidan inda shuke-shuke suke yana motsa jiki kamar
yadda yake yi a kowanne yammacin Allah iya dawo gida da kowacce safiya. Fahimah ta karaso
inda yake da kofi mai zurfi (jug) a hannunta mai dauke da sassanyan kunun aya da kwakwa da
ta matse da kanta. Ta zauna bisa fararen kujerun roba da ke gefe da tebiri a tsakiyarsu ta ajiye
a kan tebir din ta tsiyaya a tambulan tana sha. Uwais ya dakata da excercise din yana yarfe
gumi daga goshinsa ya ce.
"Abun naki ba ta yi? You know i'm thirsty".
Fahimah ta ce ba tare da ta dube shi ba, "Bari in dauko maka naka (power Horse) wannan na
mata ne".
Uwais ya karaso wajen ya dauke jug din gaba daya ya kafa kai ya shanye duka.
Ya ce, "Ki hada kayanmu yau na kwana biyu, gobe za mu je Abuja a yi miki visa".
Ambatar Abuja da ya yi ya sa Amrah ta fado mata a rai,
"Ya Subhanallah Ya Uwais, yaushe za ka je ka taho da Aunty Amrah?"
Ya dan bude ido yana kallonta bai ce komai ba sai da ta sake maimaitawa.
"In muka je goben zan biya". Ya ki yarda su hada ido kada ga gane rashin gaskiyarsa.

A cikin kayan da ya dawo da su ta ke cire masa wadanda zai tafi da su. Cikin haka
takardunsa suka zubo, wata 'yar farar ambulan ta fado da sunan 'Amrah' a jiki.
Ba ta yi niyyar budewa ba amma ta ji gabanta ya fadi, sabida rubutun na Uwais ne. An ce ba
abin da ya fi dagawa mace hankali irin miji ya ba ta wasika ba tare da ta san me ta kunsa na,
kuma an saka sunan Amrah baro-baro.
"Ya Ubangiji in na yi ba daidai ba ka yafe mini, but I must quench my curiosity".

******

Uwais na dakinsa yana fama da aiki cikin macbook sai ganin Fahimah ya yi tsaye a kansa
rike da takarda tana hawaye.
"Yaya Uwais!".
Ta fada cikin rauni. Ya dago lumsassun idanunsa yana dubanta ba tare da ya ce uffan ba.
Hawaye suka sake shimfidowa Fahimah, da kyar ta iya cewa, "Me Aunty Amrah ta yi maka ka
sake ta? Mene ne hujjar hakan? Yaya Uwais ko don mun daidaita ni da kai ne? Ta ya ya ni ma
ba zan yi tunanin in ta uku ta zo, ba za'a sake ni ba? Wannan shi ne ga mari ga tsinka jaka. A yi mata laifi kuma a sake ta Ya Uwais, don Allah na
roke ka don darajar Ammi ka janye sakin nan kada ka kai shi don Allah ya Uwais..."
Kukan da ta saki har cikin kwakwalwar Uwais, domin ta sanya gwiwarsa ta yi sanyi, jikin sa
ya mutu, ya ce.
"Fah-himah ba laifina bane, kuma ban daina son Amrah ba. Babanta ne ya ce na sake ta ko
ya kai ni kotu".
Fahimah ta ce, "Sai ka zage ka lallashe su dukkan su, bacin rai ne yasa shi fadar hakan, i
don't think he mean it, amma fushin fari ba naka ba ne Ya Uwais.

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login