Showing 15001 words to 18000 words out of 46523 words

Chapter 6 - Aishah Saddiqa Part 3 by Takori Kabara .pdf


Aisha sai ta samu kanta da bin umarninsa, ta tashi ta shiga toilet ta kunna famfon wanka
(shower), tayi wankanta fes da kalkale jiki da sabulu, kasancewar akwai sabulai na ruwa (bath
gels) kala-kala a wurin wankan masu tsananin kumfa da dadin kamshi.
Saida tayi wanka ta ji ta sakayau ta zauna shan tea din da ya aje mata. Ta ci cakes din sosai
da dadin rai, kunnenta har motsi yake don dadin dandanonsa. Domin cake ne na musamman
da Prince ke sawa bakery suyi masa mai dan yawa, sai ya aje a firji yana ci kadan kadan in
baya son cin abinci mai nauyi. Zaka samu Sau tari yana cinsa da yamma haka yana korawa da ruwan gahwah mai zafi (hot
coffee). In kuma da dare ne yafi shan chamomile ko lavender tea.
Ta gayawa kanta bazata ke tambayar Prince ya koya mata amfani da wani abu a gidannan
mai sha mata kai ba kada yaga kauyancin ta. Da kanta zata koyi amfani da komai ta hanyar
amfani da basirar ta, na yadda zatayi surviving in this amazing and wonderful Ranch House.
Wanda ya hada da budewa kanta kofar fahimtar amfani da komai na gidan, ko in ta samu ya
hada mata wifi ta dinga tambayar google yafi mata sauki akan ta dinga yawan tambayar sa
watarana yace mata 'yar kauye.
Aisha saida ta tabbatar ta koshi, kafin ta zauna ta fidda kayanta daga cikin jakunkunan da ta
zo dasu tana mayarwa tana jerawa a wardrove, zuwa lokacin in ka ganta kamar ba itace mai
kuka face face da hawaye jiya ba, ta samu duk wata damuwa ta bar ranta. Self-confidence ya
maye gurbin ta. Ta yanke hukuncin karbar kaddarar ta da hannu bibbiyu, na reality din rayuwar ta kenan,
wato rayuwa da Bayeraben basaraken mijinta Hamma Abdulrasheed (Prince), wanda shi Allah
ya ga damar su rayu tare. Iyayenta kuma suka ga dacewar shine mafi alkhairi a gareta akan
Ishaq data qallafawa rai, shikuma ya wahaltawa soyayyarta da jiki da zuciya da aljihunsa. Bata so take tuna Ishaq ko kadan, (he's her past), Ishaq wanda basa taba haduwa su rabu
batare da ya gaya mata adadin son da yake mata ba, ba tare da ya gaya mata muhimmancin
da take dashi cikin rayuwarsa ba, ba tareda ya gaya mata tanadin soyayyar da yayi mata in
sunyi aure ba. Kalaman Ishaq kadai da kulawarsa gareta ke sawa take dada ninkaya a sonsa
kullum a wancan lokacin, har zuwa lokacin da Allah yaga damar raba su. Bata sanin lokacin da
tunanin nasa yake sadadowa cikin kwanyarta ba, tana kwatanta shi da Prince.
Sai taga ma kwatantawar bazata yiwu ba, domin ratar dake tsakanin comparison din auren ta
da Prince da soyayyar ta da Ishaq mai yawa ce. Tunda Prince bashi yaje har inda take ya ganta
yace yana son aurenta ba, ba da kwabonsa ko darinsa ya aurota ba, a'a auren gata aka yi
masa da ita. Don haka kada ta tsammaci komai daga gareshi bayan cin darajar iyayensa a gunsa. Itama
kuma bata saka aka ba. Babu komai a ranta game dashi banda girmansa da take gani saboda
kwarjini da kamalarsa mai sawa taji shi kamar wani kanin Babanta.
Duk da Siddiqah ta san bazata taba samun mai sonta a duniya kamar Ishaq ba. Prince ba

ajin aurenta bane ai wutsiyar rakumi ne da tayi nesa da kasa.
Wannan tunanin data soma in bata yakice shi ba yana son bata mata juriyar ta da yakanarta
data riga ta kudurta na karbar kaddara, don haka da karfin tsiya ta yakice tunanin Ishaq ta jefar,
ta cigaba da ninkewa da jera kayanta a wardrove din dakin ta jikin bango.
Tana cikin fidda kayan ne ta ci karo da sakon Nenne da akayi packaging a leda da kyau, wani
nau’in abincinsu ne wai shi WARA da Nenne ta ce mata na Hamma dinne, sai ta fitar ta ajiye
gefe da kayan girkin da Nenne ta hadota dashida kwalaben turaren wuta masu daraja sosai.
Aisha ta fiddo wata gogaggiyar atamfarta super Holland cikin dinkunan da Nenne tayi mata riga
da zani da kallabinsu ta saka, ta yafa mayafin da ya shiga da atamfar wato orange kamar mai
shirin fita unguwa, ta saka wani flat shoe dinta dan Italy da ya dace da mayafin jikinta, ta fito
das-das da ita, tana taku a hankali zuwa sitting room din Abdulrasheed domin ta gaisheshi ta
kuma bashi sakon Nenne.
Tana fitowa kuwa ta hangi Prince din a zaune a dining yana karya kumallo. Ya daga manyan
idanunsa yana kallonta tana takowa zuwa gareshi dauke da kunshin leda. Kallon da yake mata
babu komai a cikinsa sai tausayinta. Aisha ta koma bashi tausayi na yadda da kuruciyarta aka
aura mata tsoho kamarsa (in his forties), yaji sassauci sosai a ransa tun wayewar gari bayan da
yayi addu’ar musamman akan lamarinta, da neman Allah ya bashi mafita, ta iya zama da ita ba
tareda ya cuta mata cikin gidansa ba.
Daga jiyan yaji a ransa bazai taba iya wulakantata bisa saninsa ba, tunda kuwa koba komai
zabin Nenne da Dade ce.
Da kuma darajar cewa iyayensa ne sukayi tattaki zuwa ga nata iyayen suka auro masa ita
cikin mutumci da karamci. Don haka shigowarta rayuwarsa a lokacinda bai shirya ba duk ba
laifinta bane tunda ba ita ta tsara hakan ba, iyayensu ne. Ya tabbata ko rantsuwa yai bazai
kaffara ba itama fin karfin ta akayi da bazata yarda ta auri tsoho kamarsa ba sai yaro sabon jini
dan uwanta.
Don haka shima kallon Kiki yake mata zai taya su rainonta, ya ajiye musu ita tare dashi
yadda sukeso har zuwa sanda suka ga ya kamata su karbi ajiyar tasu.
Don shima yanzu yana tababar cikar lafiyar mazantaka a tare dashi, don bai ji komai akan
Siddiqah ba wai don an ce matarsa ce, duk kyawun nan nata kuwa. Ga kugunta ya ciko kirjinta
ya daidaita komai nata masha Allah irin yadda Yoruba Demons ke son ganin mace. Komai nata
das, kamar ita ta zaba, amma hakan baisa yaji wani abu ya darsu a ransa gameda ita ba ko yaji
yayi mata wani kallo bayan normal kallo irin wanda yake yiwa Kiki ba
Ya aje mug cup din da yake sipping tea daga ciki, ya yima Aisha alama da hannu data zo
inda yake ta zauna, ta karasa a hankali ta isa gareshi, russunawa tayi akan guiwarta irin yadda
taga mahaifiyarsa nayi in zata baima Dade dinsa abu, ta mika masa kunshin sakon Nenne
kamar yaro ya kawowa Ubansa aike. Yaji wani iri da wannan ladabin tsofaffin da take masa, kafin ya karba sai da ya tambayeta da
turanci.
“Menene a ciki?”
“Sako ne daga Nenne”.
Sai ya karba yana juyawa kafin ya fara kokarin budewa, sai kuma yace mata ta hau kujerar
dake fuskantarsa ta zauna ta karya kumallo.
Ba yau ta fara hawa (dining table) tare da mutane ba a gidan Nenne, don haka sai bata ji

hakan a sabon abu ba, ta ja kujerar dake fuskantarsa ta zauna, duk da dai taji kamar tayi rashin
kunya yana bisa tebir itama ta haye bisa tebir. Saita tuna Dade dinsa ma ana hawa bisa tebir
din cin abincin iyalinsa aci tare dashi.
Tun daga kamshin abinda ke ciki Prince ya gane cewa WARA ce, his very own Wara,
tafiyayya tun daga Lagos din Nijeriya, Nennensa mai kula da abinda yakeso ta aiko masa.
Warar ta soyu da kyau, murmushi ya subuce masa don rabonsa da cinta tun zuwansa gida.
Ya kamata ayi warming dinta kafin yaci, but he can’t wait, a hakan ya dauko guda daya ya
gutsura ya tauna, sai suka hada ido da AISHA SIDDIQAH.
Aisha tayi saurin sunkuyar da kanta tana kokarin zuba ruwan zafi a kofi.
“Ko kin iya cin WARA in sammaki?”
Prince ya tambayeta da karamar murya kadan. "Naga kina satar kallona ina cin Wara, ko kin
sanni?".
A ranta tace “nikuwa na sanka. Labarinka buhu – buhu kwando - kwando gareni daga
mahaifiyarka da ‘yar gaban goshinka, Kiki”.
A fili kuma sai ta kada baki tace “ai bana iya cin Wara nikam, duk kuwa da cewa nasan da
Nono ake sarrafata, bamu yinta a Gombe, da dai Awara da yaji ce, itane abincin Hausa Fulani”.
Tayi maza ta kai hannu ta rufe bakinta bayan fitar furucin, domin sai bayan ta fada ne ta tuna
Nenne ta haneta da wannan nuna kabilancin a zama dashi, haka Ummanta, domin koda Prince
bai yi kama dasu ba, tofa ba’a canzawa tuwo sunansa na cewa shi din Bayerabe ne jikan Sarkin
Yarbawa kuma. Prince yayi murmushi ya shafa lallausar gashin habarsa. Fatima ta taba gaya masa
something like that wasu watanni can da suka gabata akan wata bakuwa ta Nenne data dauko
daga Gombe mai nuna musu kabilanci, komai aka bata sai tace wai bata iya cin abincin
yarbawa, baya raba dayan biyun wannan yarinyar dake gabansa ce, mai amsa sunan matarsa. Sai cewa yayi da ita cikin dage giransa sama “kin manta cewa Bayerabe din kika aura? A
proud one!
Dole ki koyi cin WARA, har wani lokacin ki zabi Wara ki bar Awara”
Ya karasa da dan guntun murmushin motsawar sarauta.
“Me zaki ci for lunch in bada order tun yanzu? Suna da Gbegiri ko Efo Riro with Iyan, ko Oka
da Ewedu ko Eresi Eyin (Jollof rice with chicken)?”
Dan cije siraran lebbanta Siddiqah tayi, duk bata ji tana sha'awar cin su ba yau, ko don tayo
nesa da gida ne? Duk da babu wanda bata iya ci a ciki ba a Lagos, sun kuma taimaka mata
sosai wajen cikowar jukinta musamman kugunta, ita yau tuwon Semo da miyar kuka take
sha'awa. Prince ya zuba chips da plaintain akan faranti yana ci hade da boiled egg, a gefe ga kofin
mug dinsa sa cike da tea mai zafi, bai yi aune ba sai kawai Siddiqa ta sako masa Atishawa duk
da dai tayi kokarin karewa da hannunta.
Itama kuma bata san da zuwanta ba, kwace mata tayi unexpectedly sakamakon sanyin AC
dana kasar da suka hade suka cakude matawaje daya a hanci suke bugarta, wanda ga alamu
shi baya ji sam, saboda sabo, shi ya kunna AC dinma da kansa.
Tasa tissue kuma ta fyace hanci, bayan wucewar atishawar, saura kadan Prince ya saki kofin
tangaran din dake hannunsa don bayason a face hanci ko atishawa a gabansa, kuma a take
hakan yasa ya kware da abinda yake ci a makogaronsa.

Ya dubeta cikin takaicin abinda tayi masa dinnan (atishawa da face hanci) yana dan tari irin
na wanda ya kware, saida tarin ya lafa masa silently yace mata,
“Go back to your room, please!”.
Siddiqah ta dan russunar da ido cikin yanayi na rokon afuwa, tana fadin “kayi hakuri Uncle
AK. Subucewa kawai tayi ba bazato na, please kayi hakuri!”.
Ya mike ya dauki ledar Wararsa zai bar wurin yana cewa,
“in dai ke kazama ce mai atishawa da fatar hanci anyhow bazamu shirya ba”.
Murmushi Siddiqah tayi, bayan wucewarsa daga wurin, tasa a ranta ko kusa bazata dinga jin
tsoron Hamma don yana takamar sarauta ba, zaman aure ne ya kawo ta ba zaman Oga da
yaronsa ba. Ko yana nufin (as a human) shi baya Atishawa ne ko baya fyace hancinsa idan
bukatar hakan ta kama? Da rana kuwa abinda ya ambata dazu su Iresi Iyan (Jollof rice with chicken) sai lafiyayyen
Gbegiri soup da Eforiro su aka ajiye mata bisa dining, sai wankakkun kayan marmari a
yayyanke da casserole, to su kadai ta iya ci ta bar masa sauran abincin.
Siddiqah tana sallahr la'asar a dakinta Pareto ya shigo da kwandon kayan cefane da yayo,
yana jera kowanne a muhallinsa, na firji wato su kifi da nama da kayan gwari ya saka a freezer
ya fita.
Bayan ta sallame sallahr tayi addu’a ta shafa, bata manta da rokon Allah ya cire mata
shakkar Prince Kehinde ba, ko ta samu damar zama dashi cikin sukunin zuciya yadda iyayensa
keso ta kasance tare dashi.
Tana bukatar shiga WiFi dinsa bata san ina zata je ta same shi ta fada masa ya jona mata
ba, ya shige masterbedroom dinsa ya rufe yana ramuwar barci, da bai samu yayi ba daren jiya
saboda rudun zuwan Aisha da ya kwana a ciki. Shikuma barcin ba’a cin bashinsa a zauna
lafiya. Ko motsinsa bata kara ji ba, tun bayan gama break fast dinsu. Ta mike da zummar taje kofar dakin nasa in yaso tayi masa sallama, ko tayi knocking ta gaya
masa bukatarta na ya hada mata wayarta ko ta samu ta kira gida.
Sai gashi ma ya fito da kansa cikin shirin fita shan iska, ya dau wanka iyakar dauka (casual
wear) da yafi sawa a gida, riga da wando marasa nauyi masu saukin sakawa ne a jikinsa.
Wadanda kullum suke taimakawa wajen zaftare adadin yawan shekarunsa.
Kai tsaye inda take tsaye ya nufo, cikin takunsa na kasaita. Ya mika mata daya daga cikin
wayoyin da yake amfani dasu.
“Nenne ta min maganar in baki waya tun jiya domin ki rika kiransu kina gaisawa dasu".
Hannu biyu Aisha tasa ta karba da jin dadi a fuskarta sosai sannan da girmamawa tace.
“Nagode Uncle”.
"Gashi bansan yadda ake amfani da ita ba ko zaka hada min tawa?"
Hamma ya dan dakata yace "wannan din nayima Nenne alkawarin zan Baki. In kin bi komai a
hankali zaki gane". Daga haka ya fice.
Ficewa yayi kawai ba tareda ya bata amsa ba. Amma kwarai ta burgeshi domin bayan son
mutum mai zurfin ciki da nuna iya abinda bai iya ba.
Siddiqah bata ji gwiwarta tayi sanyi ba, wai don Prince bai tsaya ya koya mata operating
wayar ba, ita kanta ta jinjinawa karfin halinta na yin doguwar magana dashi haka. Tana kuma
addu’ar ta dore da karfin halin nata, don bata son tsoro da jin shakkarsa su zama su suke
jagorantar mu’amalarsu itada shi, tunda yanzu mu'amala ta riga ta zama dole tsakaninsu.

Yana fitowa Pareto ya far hangowa daga can nesa dashi yana yiwa Doki Saheeb wanka. Sai
yayi tsayuwar da ya saba daga nesa yana kallonsu. Pareto ya kula dashi ya bar abinda yakeyi
ya wanke hannunsa ya iso gareshi, don in yaga ubangidan nasa yayi irin wannan tsayuwar
daga nesa yana kallonsa yasan magana yake so zai yi dashi. Sahib ya ankara da fitowar mamallakinsa nan da nan ya soma haniniya da zambarwa. Koda
Pareto ya iso gareshi ce masa yayi.
“Wancan sabon Criollo Horse din mai ciwon kafa an duba shi? Pareto ya amsa cike da
girmamawa cewa tun jiya ya kira vetrenary doctor dinsu ya duba shi, kuma ya bashi magani tun
a lokacin ya fara warewa. Pareto yana so ya tambayi ubangidansa ko matarsa ce wannan din
ya auro daga Nigeria? Don dai bata yi masa kama da irin masu biyo shi har gida ba, haka bata yi kama da
mutuniyar banza ba, ko ‘yan uwanshi mata dake zuwa wadanda duk ya sansu farin sani.
Amma Prince kaman ya san haka, sai ya hade giran sama dana kasa ya daure fuska sosai,
ta yadda babu fuskar ma da zai jefe shi da tambaya akan Siddiqar, don shi a wurin shi karshen
abin kunya nema yace da Pareto wannnan ‘yar kankanuwar yarinyar da bata fice ‘yarsa Kiki ba;
matarsa ce. Prince ya isa ga Saheeb yana masa gaisuwar yammaci irin yadda ya saba da yarbanci, ta
hanyar yi masa hira cikin native yaren nasu, yana yi yana shafa kwantaccen gashin wuyansa,
dokin yana haniniya yana zambarwa irin yadda ya saba in yana tareda Prince.
Daya bayan daya yake duba lafiyar sauran dawakan dake cikin stable. Pareto na biye dashi a
baya suna zaga tsakannin Dawakan suna maganarsu kadan-kadan cikin yaren kasar Argentina,
ya gaya masa zai tafi kasar France yin Wani tournament kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login