Showing 3001 words to 6000 words out of 46523 words
Chapter 2 - Aishah Saddiqa Part 3 by Takori Kabara .pdf
Aisha ta karba ta mike ta hau hada komai nata a trollies din, hatta
brush da soson wankanta bata bari ba. Amma dai kwarai taso aje da ita Hajjinnan, ta dade tana
fatan ziyartar Shabbakin Ma’aiki SAW. Da kuma Masjid Haraam da Masjid Nabawy, wato dakin
Allah mai alfarma da hubbaren ma’aiki SAW. Tazo shigowa daki taji Nenne da Nani suna magana kus-kus, bata so ta katse su, sai ta dan
dakata, da nufin su gama sannan ta shiga ba da nufin yi musu labe ba, duk da kuwa har
sunanta taji ana ambata ga alama very sensitive magana suke yi akanta.
“To haka zaku aikata baku shiryata da komai ba? Ina nufin bakiyi mata shiri irin naku na
yarbawa ba, ga shiri namu na Fulani da ya kamata duk a hada ayi mata a samu a Abdulrasheed
ya karbeta da kima? Wannan da ya tuzurance ba aure sai hawa Doki ai matarsa sai an shiryata
da kyau”. Nenne tace cikin jin kunya “Nani! Nifa babu ruwana cikin sha’anin nan ‘yar kallo ce, rigimar
Dade dinsu ne tafiyar Aisha fa, amma ni tuni na zare hannuna daga lamarin nan wanda nasan
bazai taba haifar da Da mai ido ba, in dai aka yiwa Abdulrasheed kutse da mace cikin rayuwar
Polonsa. In don ta ni, Siddiqah ta gama zaman Kehinde a gidannan. Ina mata addu’ar samun wanda
ya fi shi komai da komai ne, ba za’a lalata kuruciyarta tayi zaman gadin gidan gona sanadina
ba”.
“Akul!” inji Nani Oummana, kada in kara jin wadannan kalaman sun fito daga bakinki Sappah!
Masu nuna kin yi fushi dashi yaje ya cigaba da abinda ya ga dama.
Kin sani zuciyarki kadai Allah zai kalla ya hukunta shi da fushin cikinta.
Ki sani Abdulrasheed yana cikin jarabawar ubangiji akan sha’anin aure, ba yin kansa bane ba
jifa bane, sannan ba shafar jinnu bane, amma da yardar Ubangiji ya kusa cinye jarrabawarsa.
Dade dinsu ya fi ki gaskiya. Ki tura masa matarsa daga nan ki fita sha’aninsu, in yaso ko
gunduwa-gunduwa zai yi da ita ya kawo muku ruwansa, idan ta shekara babu ciki shine zamu
tabbatar aljana ta aureshi da gaske, ko mu yarda babu lafiyar mazantaka a tare dashi.
Amma nima bana bayan ki bata komai na mata yanzu, kada a bar 'yar mutane da ciwon
mara. Don ba lallai ya kulata tashi guda ba wannan uban kasaitar da bunkasar. Barta taje haka
yanzun, can gaba in kin fahimci komai yayi daidai a tsakaninsu sai kiyi mata babban shiri na
yarbawa ". Aisha duk ta rude, ta rikice don bata dai gane takamaimai shirin me Nani da Nenne suke ta
magana akai ba, sannan ta kasa gane inda rabin wadannan zantukan nasu ya dosa, data gaji
da tsayuwa a wurin kuma taga basu da niyyar saka aya a maganganunsu, sai kawai tasa kai a
dakin gabagadinta, bakinta dauke da sallama. Sai duk suka yi shiru suna amsa mata.
Ta karasa gaban Nenne jiki a sanyaye tace “Femi tace an gama WARA din da kikasa aka yi
miki".
Da far’a Nenne tace "Kai madallah da Femi sarkin masu Himma. Warar ai taku ce, kice ta yi
packaging dinta da kyau, ki karba ki sata cikin kayanki,".
A zuciyar Siddiqa tace “Allah ya suttura taci Wara, wannan sai asalin yarbawan Ilorin. Har
gobe ita sai fura da nono. Kowa ya bar gida gida ya bar shi”.
Tun kafin kwana biyu tafiyarta Nenne ta gaya mata komai na shirin tafiyarta ya kammala, ta
gaya mata jibi zata tashi, kuma tace tayi hakuri cikinsu babu mai rakata. Haka Dade da Emir
suka tsara tafiyar tata.
Duk kokarin Siddiqa na boye rashin son tafiyar nan yau ta kasa boye karayarta cikin
idanunta, jin cewa ita kadai ma zata tashi daga Lagos zuwa wata kasa da bata ko sani ba.
Nenne ta bar wurin da azama don bata son Siddiqah taga tata karayar.
Ranar tashinta zuwa Argentina Nenne tasa Siddiqa ta fiddo trollies dinta waje, Dade na
jiranta a mota zasu tafi airport, shi da kansa zai sata a jirgi. Masu aiki suka daukar mata
jakunkunan suka sa a bayan mota Lamborghini wadda asalinta motar Abdulrasheed ce da yake
hawa idan yazo gida Lagos. Nenne tazo har daki tace da Siddiqa idan ta gama shiryawa ta fita parking lot Dade na mota
yana jiranta. Nenne da wayau taki yarda su hada ido yau, kada taga karayar dake cikin kwayan
idanunta.
Ta miko mata wayar hannunta dake jikin caji tace ta kula da wayarta sosai. Sannan Nenne ta
matso kusa da ita kamar bata so wani yaji me zata ce, ta fadi wani abu, da ya kara daga
hankalin Siddiqah.
"Ki yi hakuri da duk yanayin da Zaki riski rayuwa dashi a inda zaki je.
Bai taba zama da matar aure ba a gabadaya rayuwarsa tun ta samartaka har girma, he will
find it difficult to cope with you at first. Idan na bata miki a hada wannan auren a bisa sani ko
rashin sanina ki yafe min Siddiqah.
Na yi ne da kyakkyawar niyya saboda kaunata da mahaifiyarki. Aure ya gaji haka, ba inda
baya kai diya mace kada ki damu da duk inda zaya kaiki.
Ki dinga yi masa uzuri kullum, uzuri na cewa duk shekarunsa shi yaro ne a hannunki tunda
bai taba dandana rayuwar aure ba, ba kuma sabida mu zaki dinga yimasa uzuri ba a’ah, sai don
kasancewar sa shima Dan Adam ne, ajizi, kuma miji a gareki mai tarin nakasu kamar kowanne
Dan adam. Idan ya bakanta miki bisa sani ko rashin saninsa, ban horeki da gayamin ko mahaifiyarki ba,
a'a ki gaya masa face-face tsakaninki dashi yanzu babu hijabi, ku fuskanci matsalar komai
tsaurinta, mijinki ya zama best friend dinki, confidant dinki, ya zama ba tsoro ba shakka a
tsakaninku sai yarda da cewa kowa zai iya batawa daya a bisa sani ko rashin sani. Ki kuma
dinga gayawa Allah a kowacce sallahr farillarki ya huwwace miki soyayyarsa.
Ki ce “Allah ga AbdulRasheed dan Idris Abdullateef Akanni, ka sanya masa soyayyata mai
girama".
Wata irin kunya ta kama Siddiqah. Nenne bata damu ba ta cigaba da cewa.
"Sannan ki hada da yin hakuri. Sabida shi wannan hakurin da nake ta jaddadawa a auren na
gani inaso ma shi ne ke tafiyar da rabin auren, balle aure irin naku da bashi ya gani yace yana
so ba, mu muka gano masa dacewar hakan.
Don haka hakurin da zakiyi da Abdulrasheed mai yawa ne Siddiqah, shine kuma zai zame
miki ginshikin zaman auren bakidayansa.
A sanin da nayi masa ko baya sonki bazai taba cutar dake ba, sannan bazai wulakantaki ba
saboda mu muka kawo ki cikin rayuwarsa, amma zai iya yi miki silent protest! Saboda
mummunar fahimtar da yayiwa mata gabadayansu.
Na roke ki Siddiqah, kiyi kokarin da zaki share wannan mummunar fahimtar da yayiwa mata
daga zuciyarsa, in kowa nasa ya rainaki saboda shekarunki da wayewarki da karancin ilminki ni
mahaifiyarsa ban raina ki ba, na yarda kema mace ce kamar kowacce mace mai fasaha da
hikima da iya tata kissar. Abdulrasheed ya riga yayiwa mata kudin goro, inaso ki nuna masa har
yanzu akwai nagari, akwai kuma masu soyayya ta saboda Allah.
Wannan tarbiyyar da Haj. Zainab ta jima tana baki yanzu ne zata yi miki rana, ki fiddo ta
sarari kiyi amfani da ita a gidan aure, ki fahimtar dashi cewa ba duka mata ne a cikin rigar da
yake kallon su ba, komai lalacewar da zamani yayi, har gobe akwai mata masu kyawun hali.
Na san bazaki samu cimma wannan nasarar a lokaci guda a tare dashi ba, sai kin yi
HAKURI mai dimbin yawa Siddiqah, na dameki da kalmar hakuri ko? Kada kiyi mamaki, shi
hakuri baya yawa, ribarsa ce kawai mai dimbin yawa.
Ki kauda kabilancin nan naki da kika bari ya samu muhallin zama a zuciyarki, in har kinason
a zauna lafiya, ina kara gaya miki Abdulrasheed Bayerabe ne, ki maida al’adarsa taki, shima sai
ya maida al’adarki tasa. Aure babu cikin kabilar da baya kai mace a addinin musulunci, ni
dinnan na isheki misali, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi Aishatu-Siddiqah, ya albarkaci
aurenki da zuri’a salihah, dayyibah”.
Nani Oummana tace “kisa himma kinji ko Indo wajen kula da mijinki, Aishoshi himma garesu
ta wannan fannin. A fannin iya kula da shimfidar miji ma basu dana biyu, sannan a komai sai
kinga sun zama zakaran gwajin dafi a wurinsa saboda albarkar sunan NANA AISHA, sannan
ababen buga misali ga mazajensu a duk inda suka shiga. Ina fatan Allah yasa shekara na zagayowa in ganki goye da magajin sarkin Ilorin, ko mai
sunan marigayi Uban kasar Gombe, kinji ko Indo Aisha?”
Siddiqah sai ta soma hawaye. Ko dai su Nenne sun gaji da zamanta tare dasu ne saboda
tana musu halin kabilanci? Shine zasu kaita inda suka san bazata taba iya zama ba, don
kabilancinta bazai barta ta iya zama da Bayerabe ba. Zuciyarta na tunasar da ita kada ta taba
yaudarar kanta, da tunanin ko mijin nata ne ya bukaci zuwanta, Hamma Abdulrasheed, (Prince),
mai sunayennan guda uku, bashi ya bukaci ta je inda yake ba.
Nenne bata iya cigaba da tsayuwa a dakin ba ta yi maza ta fice, ganin tashin hankalin da ya
bayyana baro-baro akan kyakkayawar fuskar Aisha-Siddiqah karara.
Princess Firdausi ta yi kamar bata fuskanci halin da Siddiqah ta fada ba, saboda tausayin da
ya kamata, ta kama hannunta zuwa (parking lot) na gidan inda Dade da Seun ke zaune cikin
mota suna jiran fitowarta.
Firdausi ta bude mata kofar bayan motar, jiki a salube Siddiqah ta shiga. Firdausi ta rufe kofar
motar tana cema Dade dinsu.
“A dawo lafiya Dade”, cikin harshen Yoruba. Dade ya daga mata hannu kawai. Princess
Firdausi na daga mata hannu itama haka har suka fita gate din gidan.
Seun, ya zaburi mota ya bar shiyyar Banana Island da Siddiqah Yunus da mahaifin mijinta
kwance a bayan mota.
**** **** ****
Suna tafe Siddiqah na tuno tun farkon zuwanta Lagos, daga zuwa ganin likitan Asthma ace
komai ya jirkice mata haka, sai kaddarar aure wannan na tarad da waccan.
Aurenma na masarautar Yarbawa, yarbawa da bata so tun bata san meye ma’anar kalmar
Yoruba ba.
Rayuwarta ta juye rana daya (upside-down) ta kutso cikin ta gaggan kabilar yarbawa din.
Zamanta a birnin Lagos ta san daga yau ya kare kuma. Yanzu ne zata fara rayuwar reality da
bayeraben miji, wanda shine hakikanin abinda ya kawota cikinsu, ya rabota da kowa nata. Ko
wace sabuwar kaddarar ke jiranta? Ko wadanne sababbin abubuwan kuma ke kiranta yanzun
Allah masani.
Bayan ta riga ta fara sabawa da duniyar Yarbawan data fado ciki rana daya, wadda zuwa
yanzu ta dade da bin jikinta. Ta na sunsuno cewa wata sabuwar rayuwar ce ta dumfarota, wato
rayuwar aure gabagadi. A baya tana amsa sunan auren ne ba tareda taje cikinsa ba, yanzu
kuwa kacokam an daukota ne an cuso cikin rayuwar Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni,
ta karfi da yaji ba tareda ya bukace ta ba.
Ko wacce irin tarba zata samu daga PRINCE ABDULRASHEED din? Ko zai yarda ya hada
rayuwarshi da ita? Ko zaiyi maraba da zuwanta cikin rayuwarsa? Akan karan kanta shin ko zata
iya sakewa ta rayu da wani da namiji a duniya ba Ishaq ba?
Wadannan sune tambayoyin da Aishatu-Siddiqah ke yiwa kanta a kan hanyar su ta zuwa
Airport, ba tareda ta san amsar ko guda daya ba. Sannan bata kuma da wanda zai amsa mata.
“Bashi da lokacin kowa a duniya irin Dawakansa. Ba abinda ya baiwa muhimmanci a duniya
bayan ibadah irin hawa Doki. Abdulrasheed yana matukar son Dawakansa, lokacin shi nasu ne.
He enjoys riding horses more than anything in his life!”.
Siddiqah ta tuno wasu daga cikin kalaman mahaifiyarsa akansa, a lokacin data ke yawan
gaya mata ko wanene dan ta Prince Abdulrasheed Kehinde da halayensa, wannan har mijin da
yake da lokacin mace ne a rayuwarsa, balle ita karan kada miya Siddiqah Yunus?
A wancan lokacin da Nenne ke yawan bata wadanna labaran nasa, ta kan zama bored da
sauraronsu, har ta tambayi kanta ko meye alaqarta da labaran da Nenne ke yawan bata akan
shi da rayuwar shi?
Yanzu ta gane cewa Nenne na bata labarannan ne don ta san cewa ko ba dade ko bajima,
tana raye ko bata raye tunda aure ya riga ya shiga tsakaninta da Prince, watarana irin wannan
na zuwa, wato ranar da rayuwarta zata shige sukuf! Cikin ta Dan Nenne wato Hamma
Abdulrasheed (Prince), a daidai lokacin da bata zata ba kuma bata shirya ba, shima kuma ta
tabbata haka tarewar tata zata zo masa bagatatan.
Bata gushe ba tana ta wadannan tunane-tunanen har suka iso iyafot din Murtala Mohammed.
Seun, shi yayi tsayuwar tsayin daka akan kayanta, har aka gama checking aka aunasu a jirgi.
Ya rage dan lokaci jirginsu zai tashi, sannan ne Dade ya bata tikitinta da Fasfo dinta a
hannunta.
Yace da ita “nan da awanni 22 zaku sauka a kasar Argentina.
Kada ki damu, na riga na gaya masa karfe nawa zaki taso, da lokacin saukarki.
Kina sauka zai zo ya daukeki da kansa a filin jirginsu.
Inji dai zaki gane kamannin Yayannaku? In ma baki gane shi ba na tura masa hoton ki, na
jikin pasfo dinki, na tabbata shi zai gane ki”.
Siddiqah ta gyada kai, tana fakar kallon Dade tana hadiye hawaye har wasu suka ballo kan
kuncinta suka ki hadiyuwa, ta sharesu da gefen gyalenta.
Dade ya lura kuka Siddiqah take yi kasa-kasa, yaji babu dadi a ransa, nan yaji duk guilt ya
kama shi da bazai kama hannunta ya kaita har gaban Abdulrasheed da kansa ba, ya hada su
yayi musu nasiha ya bashi amanarta, amma Emir ne ya ce masa kada yaje, ita kadai ya yarda a
tura, in yaso a gaya masa ta taho, yaje ya dauketa da sun sauka, dattijon Bayeraben mai ran
karfe shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan. Amma anya ba Prince din ya kamata su takurawa ya tako ya zo ya dauketa da kansa ba?
To amma basu da mafita sai wannan guda daya, don iyaka tunaninsu sun san ba zai zo ba
din, duk iya kiran da zasu yi masa in dai akan mace ne. bazai ce bazai zo ba amma zai yi ta
zamewa ne cikin hikima ba tareda ya bata musu rai ba har sai sun gaji sun rabu dashi.
Dade ya dafa kafadun Siddiqah a hankali yace “Be strong my daughter. Allah yana tareda ke
kin ji, addu’o’inmu na tare dake, daga tashin ki har ki sauka ba matsala. In sha Allah.
Ki fuskanci mijinki da karfin zuciya kada ki karaya da komai zaki gani akansa, kullum ki tuna
cewa zaman jihadi ne zaki yi babba, na gyara rayuwar Abdulrasheed ya karbi rayuwar iyali.
Ke ce kadai zaki sa ya goge tabon da yayiwa mata daga ransa, ko yaci gaba da yi muku
kallon da yake yi muku bakidaya.
Siddiqah ke kadai zaki sa Abdulrasheed ya gane ya kuma banbance cewa yana missing wata
rayuwa mafi girman daraja daga wadda ya baiwa amanna a rayuwarsa; wato tsakanin rayuwar
aure da tara iyali da kowanne dan adam mai lafiya ke yi, koko ta neman duniya babu wadanda
zasu taya shi ci da morar duniyar, ke zakisa ya yarda akwai abinda zai bashi pleasure in this life
fiye da hawa Dawakansa. Wuce ki shige ana kiranku, Allah yayi muku albarka bakidaya”.
Da baya da baya take tafiya tana kallon Dade, mutum mai tarin karamci da kulawa a gareta,
hawaye fal idanunta, shikuma Dade bai bar wajen ba, haka bai gushe ba yana aika mata
murmushin karfafa gwiwa har ta shige cikin boarding passengers.
***** ***** *****
Lokacin da jirgin Argentinian Airways wato (Aerolineas Argentinas) ya daga da SIDDIQAH
YUNUS tana daga zaune jikin tagar barin dama na jirgin, idanunta a