Showing 1 words to 3000 words out of 46523 words

Chapter 1 - Aishah Saddiqa Part 3 by Takori Kabara .pdf

 AISHAH-SIDDIQAH



​​ 3






SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
babbangoro2015@yahoo.com


TUNASARWA/JAN HANKALI
Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata
kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba.
Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa
cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da
kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa.
Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya
guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu
ga junanmu.
Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba.
Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa,
wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde.
In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko
mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi
Atqaakum”.
Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya
Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna.
Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage
shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu
hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da
haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a
kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama
cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada.
–Takori Sumayyah AbdulQadir.
SADAUKARWA
Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga mambobin TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah
ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki.

KIYAYEWA
Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce
kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma
abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali.
GODIYA DA JINJINA
Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari,
tacewa da gyarawa Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aishatu Muhammad,
Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira.
​ In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa
namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH.

(INA TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a
wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements
ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control?
Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA
LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da
kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo
ku bani labari.
​ Takorinku
April, 2024

AISHAH - SIDDIQAH 3
A
isha-Siddiqah na cikin farin ciki mai yawa a yau, kasancewar yau ne ta zana paper dinta ta
karshe a sakandire lafiya. Kuma ga dukkan alamu mahaifan Abdulrasheed basu yi asarar
makudan kudadedn da suka kashewa Aisha ta jona karatunta na sakandire ba a makaranta mai
tsada da yaransu ke yi, har yau da Allah yasa ta kammala cikin kudurarsa. Lokacin tafiyar Nenne aikin Hajj na wannan shekarar ya kusa, ta fara shirye shiryen tafiya,
wannan karon tareda Nanin Gombe zasu tafi Hajjin bana, wato mahaifiyarta Hajiya Oummana,
don haka za’a dauko Nanin daga Gombe, zuwa Lagos, sai su hadu su tashi ta Lagos State
Pilgrims. Sun yi waya da Haj. Zainab ta gaya mata batun tafiyar tata, nan Umman Siddiqah take gaya
mata suma acan Gombe suna shirin tasowa, kuma cikin ikon Allah wannan shekarar ma har da
ita Umman, ta kara samun kujera daga ofishin su Malam Yunus. Nenne tayi murna sosai da
sake haduwarsu a Saudi, karo na biyu, har take cewa cikin tsokanar Umman. “Abin Allah sai kiga wata shekarar kuma war haka, saimu sake haduwa a masarautar Ilorin,
muyi wankan jegon Petel dinki”.
Dariya Haj Zainab tayi cikin jin kunya, na Nenne tace “to ta share dakin Petel, tayi wake da
da shinkafa da salad da yajin maraba, Petel zata zo musu sallama, don itama wajen mijinta zata
koma kafin tashin nasu aikin Hajj, tunda ta gama makaranta.
Da wannan Nenne da Umman Siddiqa suka yi sallama cike da kaunar juna.
Haj. Zainab ta gayawa Malam Yunus maganar zuwan Petel ganin gida da sallama, wai zata

koma inda mijinta yake zaune. Malam Yunus ba karamin dadin hakan yaji ba, a take ya ce
maza Sunusi almajirin dake zama da Umma tun bayan auren Siddiqah, ya gyara dakin Petel ya
share ya goge.
Lokacin da za'a taho daukan Nani Ummana sai Nenne ta gayawa Siddiqa ta shirya zasu
wuce Gombe tare, ta gaya mata zata kaita ganin gida ta gaida su Ummanta, in yaso ta yi kwana
uku, suyi sallama da su Ummanta saboda sunaso zata bi bayan mijinta (Hamma) cikin
watannan, wato lokaci yayi da zata tare a gidanta. Duk da Nenne ta yi mata wannan bayanin na dalilin da zata je sallama gida Gombe, Siddiqah
bata damu ba, murnar zuwa ganin gidan ya take fargabar maganar tarewar, wato sawun Giwa
ne ya take na Rakumi, ta hau murna da giringidishin shirin tafiya gida baji ba gani, kamar ta
sume don dadi. Yaushe rabonta da Umma da Abbanta? Ji take kamar ta shekara Goma rabonta da gida da
iyayenta.
Nenne dai bata yi mata bayanin yadda tarewar tata zata kasance kai tsaye ba, ta barwa Haj.
Zainab, don ta san Haj. Zainab zata fita iya lallashinta da convincing dinta ta tafi cikin dadin rai
ba tareda ta daga hankalin ta ba.
Kuma tun farko Haj Zainab taso daman a barta ta shirya Siddiqah tun kafin zuwanta Lagos
wato tayi mata gyaran aure amma basu bata damar yin hakan ba a lokacin. Nenne tana ganin
yanzu in taje gida kome Haj. Zainab takeso sai tayi mata yanzu ne yafi dacewa.
Tsaraba sosai tasa Seun da Firdausi suka hadowa Siddiqah, wanda zata tafi dashi gida,
turamen atamfofi da lesika na Ummanta da kannen Babanta mata dake Kumo, da shaddoji da
yadikan Maza masu daraja da turare na Babanta da Yayansa madaurin aurenta Baba Barau.
Itada Nenne da Firdausi suka taho Gombe ranar Asabar. Da suka shigo gari kuma tun kafin su tafi masarautar Gombe saida suka fara sauke Siddiqa a
gidansu dake Jeka da Fari.
Umman Siddiqah dama ta san da zuwansu, tuni ta shirya musu karba ta girma yadda ta saba
yima bakinta na musamman, Umma akwai karrama bako balle suruka irin Haj. Sappah, ta
tarbesu da abinci mai tsari da abin sha mai sanyi. Saida su Nenne sukayi kat, sukayi sallah
suka huta, suka kuma sha hira sannan suka fara shirin wucewa fadar Gombe. Umma na tsokanar Princess Firdausi da cewa, "yau dai gata ga Gimbiyar tagwaye kuma auta
sannan shalelen Nenne". Princess tayi murmushi tana sadda kai tace “Umma ai tuni Siddiqah ta
kwace min wannan fadar”.

Aisha-Siddiqah-Petel 'yar Ummanta, wadda tayi mul-mul da ita don kyau da koshi, na abincin
yarbawa mai gina jiki, wanda ya hade da samun gyaran jiki na subulai da mayuka masu kyau
da gyara fata, tana lafe jikin Ummanta sai zuba sassanyar kamshi take irin na matan manya, ko
minti daya taki sakin Umma ta tashi, duk kunya ta ishi Umman, in tayi korafi sai Nenne tace. "Don Allah barta kusa dake taji duminki Zainaba, ai Aisha tayi kokarin da ban zata ba, wata
nawa rabonta dake? Kin yi tsammanin zata iya wannan kokarin data yi? Petel ce fa! Kuma
Siddiqahr nan ‘yar Ummanta!
Yanzu kuma gashi kasar bakidaya zata bar miki, ai ta cancanci a barta taji dumin data yi
kewar ji".
Hajiya Zainab abin ya bata dariya sosai saida suka dara a tare. Petel ta sake sunne kai jikin

Ummanta.
Bayan wucewar su Nenne fadar Gombe, Malam Yunus ya dawo daga aiki ya tadda babbar
bakuwar tasu AISHATU INDO SIDDIQAH, shima Abban na Aisha ya hau tasa murnar, yana
cewa,
"halan cusa ake miki da tebar yarbawa da Amala da Iyan, wannan kumari da kikayi a ina
kika samo shi Indona? Keda kike kamar a bushe ki".
Dariya suka sa itada Umma, ya mikama Aisha kunshin balangun da yayo mata guzurinsa,
mai zafi da ruwa-ruwansa, yaji yajin balangu irin yajinnan mai citta, da yankakkiyar albasa da
kabeji abin sai wanda ya gani ko ya dandana.
Da doki da kewa Aisha ta karbi balangun Ayuba mai nama ta soma ci tana fadin, "kowa ya
bar gida Umma gida ya barshi.
Nayi kewar balangun Ayuba sosai, nayi kewar Arewa gabadaya".
Yau dai Aisha da iyayenta kwanan farin ciki sukayi, sun sha labarin Lagos kamar ba gobe,
itama ta sha nasu labarin. Na surutun da aka yi tayi akan aurenta. Musamman da Ishaq ya
dawo daga bautar kasa ya tarar an yi mata aure. Abba yace Ishaq kuka yayi tayi a gaban su
kamar karamin yaro kuma ya gaya masa bashi da laifi da yadda suka yi da mahaifinsa duk ya
gaya masa. Yace tun daga lokacin Ishaq ya bar Gombe don yayi bakin ciki da abinda Babansa
yayi masa, ya koma zama hannun Kawunsa a Kano. Shikuma ya saka shi a harkar kasuwancin
da yake yi a Kantin Kwari, na sayarda atamfofi. Yace zuwa na karshe da Ishaq yayi Gombe
kayan abinci ya kawo musu turum! Yace yana jin dadin zaman Kano kuma yana neman aiki
acan sannan kasuwancin da yake taya kanin Babansa yana garawa sosai.
Aisha taji wani irin yanayi na tausayin Ishaq na ratsata, amma bazata ce komai ba kada Abba
ya daina bata labarinsa.
Tun a daren Umman Siddiqah ta dama tukudi mai kyau ta soma baiwa Aisha da sabaya don
nononta ya kara cikowa.
Auren ne yazo mata ba shiri. Amma tuntuni tanada niyyar bata ‘sabaya’ in za'a yi mata aure
don nononta data bige don ya tsahirta ya cicciko. Kwanciyar hankalinta da Aisha bata tare ba
har lokacin ashe, tun lokacin karatu take yi. Koda Nenne tace zata yiwa Aisha gyara irin nasu,
ita tafison ta bata tukudi da sabaya shine nasu na gado. Umma ta gaya mata da kyakkyawan lafazi cewa da sun koma Lagos zata tare gun mijinta,
sukayi mata nasiha mai shiga jiki kuma mai ma'ana. Suka bata kwarin gwiwa mai yawa suka
karfeta. A karshe suka nemi yarda da amincewarta kan hakan.
Cewa ta yarda zata tare? Ko tukunna bata amince ba su gayawa Haj. Sappa a kara mata
lokaci kan wanda aka bata?
Aisha taji dadi a ranta iyayenta basu yi mata dole ta tare ba, basu tursasata ba kamar da,
yanzu lallabata suke, don haka ita kuma tayi kudurin zata kasance mai biyayya ga dukkan
umarninsu.
Ta yarda zata je duk inda aka umarceta don tayi zaman aure, ko bangon duniya ne zata je ta
zauna da wanda bata sani ba, bata san halinsa ba. sannan take da tabbacin Bayerabe ne
kabilar da bata so din.
Duk da cewa tasan in ta tafi yes, tabbas zata yi kewar Ummanta da Abba, zata yi kewar
Nenne kuma. Kai har Dade dinsu Firdausi ta san zata yi kewarsa, mutum mai kirki, mai sake
mata da janta a jiki kamar surukuwarsa ba, shi dasu Fatima da Firdausi ba wanda bazatayi

kewa ba. Duk da ba shiri suka cika itada Fatima ba, amma sun zauna tare tsayin lokacinnan da
dadi ba dadi sun zauna tare a gida daya, ta san zatayi kuka na barin gida da sabon data yi da
gidan Nenne da daukacin mutanen cikinsa su Femi chief cook, Seun driver da sauran
ma'aikatan gidan data saba dasu duka. Amma hakan bazai hana reality na cewa su duka ba zamansu take ba, zaman aure na
wanda zataje wajensa.
Kwanan su uku suka juyo Lagos, tareda tsohuwar Nenne wato Nani Ummana.
**** **** ****

Nani Oummana ta iso gidan surukinta Engnr. Idris Akanni lafiya, saboda soyayyar Kaka da
matar jika ko kuwa soyayyarta da Prince Nani yi take kamar ta hadiye Aisha-Siddiqah, tsohuwar
mai ran karfe komai takeso bata saka kowa a gidan tun isowarsu saidai kaji tace.
“Indo jikata miko min kaza, ko yimin kaza”.
Da daddare kuma da Nenne tasa aka gyara mata dakin ita Nenne inda ta saba sauka in tazo
gidan, aka zo daukar kayanta za’a shigar dasu dakin Nenne. Ummana tace “ai kawai ki rufe
dakin ki, ki tafi turakar mijinki, ki barni nida Indo-Siddiqah zan kwana”.
Siddiqah taji dadin son nan da Oummana ke gwada mata. Don haka gladly ta barwa Nani
Ummana gadonta tana murnar yau taga na gida bayan Nenne (bafullata) ita kuma ta shimfida
Dunlop a kasa ta kwanta.
Har dare ya raba suna hirar gida Gombe, Aisha ta samu kanta sosai da sakewa da tsohuwa
Oummana, tana bata tarihin masarautar Gombe.
Aisha kuma tace tun suna yara suke zuwa kallon hawan sallahr idi gidan sarki. Nani
Oummana an sosa mata inda ke mata kaikayi don lokacin da Aisha ke fadi lokacin mulkin
maigidanta ne uban kasar Gombe Sarki Ahmadu Jalloh Umar, nan ta hau baiwa Aisha labarinsa
da irin girman abokantakar dake tsakaninsa da Sarkin Ilorin, wato Sarki Abdulrasheed
Abdullateef Akanni, har da bata labarin yadda taki yarda da auren Sappa da Waziri Idrisu a
baya, saboda a ganinta Yarbawane, tace “amma Uban Kasa Allah ya jaddada rahma agareshi
bai saurareni ba”. Oummana tace,
“sai gashi yau kaf! Cikin zuri’ar sarkin Gombe da ‘yan uwan Sappa da suke uba daya babu
wanda yayi dacen aure da soyayyar miji irin wanda Sappa tayi.
Tace “Bayeraben mutum akwai rikon aure akwai iya soyayyah”.
Daga nan ta koma bata labarin gwagwarmayar data sha da kishiyoyi da kwarkwarori.
Daga nan ta gangaro ga baiwa Siddiqah labarin yarintar Prince Abdulrasheed a matsayinsa
na jikan farko a lIorin Emirate, da son hawa Dokinsa.
Anan ma Siddiqah ta kara gane cewa Hamma Abdulrasheed, favourite jika ne again a gurin
Kakarsa ta wajen Uwa da Kakansa na wajen Uba.
Washegari ta raka Nani da Nenne wajen finger print na visar tafiya aikin Hajjinsu, akasa
itama tayi a wani wurin daban bayan an gama nasu.
Siddiqah ta soma tunanin da tarewar da akace zatayi gidan mijin dama aikin hajjin suka tafi
da ita don ta kula da Nani Oummana, kasancewar komai ita take mata a gidan tsohuwar bata
da kwari.
Har ta fara hango kanta ta sako hakorin Makkah ta dawo Gombe da tsarabar Umma
rankatakaf! Makwabta nata shigowa barka da zuwa bayan ta dawo. Sunanta ya tashi daga

Siddiqah zuwa Hajiya Aishatu-Siddiqah Indo.
Ashe dai duk hasashe take yi, kuma bata hasaso daidai ba. Domin an yi haka da kwanaki
kadan rannan da daddare Nenne ta shigo mata da manyan trollies guda biyu babba da karama
da zata tafi dasu, tace ta hada kayanta da duk abinda ta san zata bukata a gidanta a cikin
jakunkunan data kawo mata dinnan. Da mutuwar jiki mai yawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login