Showing 3001 words to 6000 words out of 18685 words

Chapter 2 - AMANI PART 4 FREE BOOK END COMPLETE BY SUMAYYA TAKORI.pdf

manna shi a cikin jikin
ta, tana fatan su dawwama a haka. Tana fatan kada gari ya waye.
A haka suka kwana, da asubah Mukhy ne ya fara tashi da kyar ya raba jikin sa da na Amani
saboda yadda ta bi ta makale shi cikin jikin ta, wadda ya gama jikawa da gumin jikin sa jagab, ji
tayi kamar ta rike shi ta hana shi tashin, don ta fi so su dawwama a haka. Mukhy ya je yayi
wanka da ruwan sanyi kana ya dauro alwallah ya fito, yana mamakin abinda ya same shi jiya
kamar farfadiya kamar bugun aljannu, ita sai a lokacin ma ta samu barcin ya zo mata.
Mukhtar ya soma kokarin tuno abinda ya faru da shi a daren jiya da mamakin ganin Amani
kwance a kan gadon sa, don ya manta ma yadda aka yi ta shigo tsabar yadda zazzabin ya
buge shi jiya. Amani ta ji alamar tsayuwar Mukhy a kan ta don haka ta bude ido tana kallon
Mukhtar a hankali da idanun ta da ke cike da barci, shima yana kallon ta da kyawawan idanun
sa yana kara son komai nata, mace kamar ita tayi wa kanta halitta komai nata mai ban shaawa
ne da daga hankalin da namiji. A hankali ta lumshe idanun ta cikin nasa, tana jin karin son sa a
ran ta, sai hawayen suka dirgo marasa dalili bare madafa.
Mukhtar ya dauke kai kamar bai ga hawayen ba, ya kada kai ya wuce ga sallayar da yake
sallah a kai, ya ce mata.
Tafisu ki tashi ki sallah haka!.
Daga kwancen da take ta ce ciki raunin murya Ya Mukhy ka yafe min? Na yarda banida kirki,
na yarda bani da hali, na yarda ban fi kowa ba, na yarda wanda yafi kowa shine wanda yafi
kowa tsoron Allah, na tuba na bi Allah na bi ka! Kada ka sake tafiya ka bar ni, I promised to
become a changed person. Muryar Mukhtar wannan karon cikin jin dadi da tausayi. Ya ce cikin
kwantar da idanun sa a kan ta.
Kiyi sallah Amani, sai ki zo mu yi magana ta fahimta, bana so wannan ramar da kike faman
yi, kin ji?
Gayun ma duk kin daina, haba Tafisu ni ina son gayun ki fa!”
Dadi ne ya kama ta, tana son tashi amma ta kasa janye bargon daga jikin ta, sabida rigar ta
da Mukhy ya cire cikin zazzabin da ya makanta shi jiya. Daga ita sai bra da panty din ta.
Cigaba da kwanciyar tayi har sai da ya tada sallah, sanan ta yi maza ta dauki rigar barcin ta
ta maida amma bata daura zanin atamfar ba, ta wuce nata dakin don ta shirya sosai.
Sosai ta zauna ta cancada kwalliya, gayu iya gayu, cikin wani (swiss lace orange colour) da
aka yi wa dinki riga sa da siket matsatstsu, ta fesa turaren ta na dindin watau Elizabeth Arden.
Ta yi alkawarin yau ko kofar gida bazata bar Maina ya fita ba, jinyar sa zata yi da tarairayar
abun ta, in an neme shi zata ce ai bai da lafiya, sai ta tabbatar ta wanke duk wata tsatsar ta
dake ran sa, in dai ta amsa suna Amina-Amani, Aminatu Mamar Manzo, ba wai sauran mata ta
rako duniya ba kamar yadda ake goran ta mata ta koina. Zata gwada nata diyaucin na ya mace da kissar da ake cewa da ita aka haife kowaccen mu.
Amani ta yarda za ta bada hakuri yau, ta duk hanyar da zata iya da irin nata baiwar da Allah ya

yiwa kowacce diya mace. Ta koma dakin nasa ta same shi ya idar da sallah ya koma ya kwanta
don jikin sa ba karfi. Hidima sosai take ta yi da shi yana daga kwance yayi dai-dai wai bayan sa
ke ciwo, hatta tea yau har kan gadon sa ta hada masa ta kuma bashi da cokali a baki, har sai
da ya ture ya ce ya ishe shi. Amani ta koma taga an shirya musu kalaci kala-kala ta zubowa Mukhy farfesun koda da
hanta ta kawo masa, ya ce na koshi fa, bani dai magani in sha, sai kiyi min tausa a bayan nan,
duk jikina ciwo yake, akwai first aid box a cikin drawers din can, duba ki dauko min paracetamol,
Ta yi yadda ya umarta, ta dauko maganin ta ballo biyu ta hado da gorar ruwan Faro mara
sanyi ta kawo masa, a baki ta saka masa maganin, sannan ta kafa masa gorar ruwan a baki ya
hadiye.
Shi da kan sa bai yi marmarin fita ba yau, ganin yadda ake ta gatan ta shi, tuni zazzabin ya
sake shi sai bin Tafisu da kasaitaccen kallo yake daga kwance, ga kwalliya ta fece ta fita tsara
yadda yake son ganin ta, an yi daurin nan a kan goshi, irin dai yadda take yi a Katsina a lokacin
da take kan ganiyar ta ta TAFISU! Yana hangota daga nesa yana hadiyar miyau yana faduwar
gaba, domin babu karya Tafisu ta iya daukar wanka.
Abin mamaki shi da baya kashe wayar sa sam, amma yau sai ya samu kan sa da kashewa.
Duk wanda ya neme shi ta waya ya samu wayar Maina a kashe, yau har Ummami ya kasa fita
gaishe ta sabida uwargida ta murda kambu.
Ya Mukhy ka tashi muje na hada maka ruwan wanka ya kalle ta kasa-kasa yace ai na yi da
asubahi, ko ke zaki cuda ni yanzun? Amani ta kai tafukan ta ta rufe fuska cikin jin kunya tana
yar dariya, kuma sai ka tube a gaba na in hau cuda maka baya? Ai bazan iya ba kai ma bazaka
iya ba. Mukhy ya ce wa ya gaya miki bazan iya ba? Sai kace nima irin ki ne dan kauyen Faskari?
Yanzu dubi daurin da kika yi a kan goshi, yammatan yanzu basa yin irin sa, sai na acuci,
wannan daurin naki fa tun na zamanin Maryam Babangida
Amani me zata yi ba dariya ba! Bata san sanda ta tuntsire da dariya ba tayi ta yi, ta ce Ya
Mukhy! A ina ka san a cuci da daurin Maryam Babangida kai ba dan Najeriya ba?
Ya mika mata hannu ya ce zo in gaya miki ta rufe ido tana murmushi domin cinyar sa ya
gyara mata yana nufin ta zo ta zauna kai. Amani ta rasa inda zata sa kan ta don kunya, sai ta
bige da cewa.
Ya Mukhy yau bazaka je fada bane?
Wannan shine kora a fakaice. Kin taba sa ni zuwa fada? Inada fadar da ta wuce wannan?
Mukhtar ya fada tare da mikewa ya nufe ta da azama don ya fahimci neman guduwa take yi don
ta fara tsorata da idanun Mukhy yau, caraf! Ya ruko ta ta baya, ya kuma rungumota gabadaya,
ya kwantar da kan sa a kafadun ta, ya kai hannu ya shafi kirjin ta da ke zagin sa tun dazu, ahe
ko bra babu jikin su, yayi wata irin ajiyar zuciya yace.
By Allah you will be the death of me AMANI!.
Ya juyo ta suka fuskanci juna kafin ya sumbaci kirjin cikin lumshe idanu, sannan ya zuge zip
din rigar gabadaya. Amani ta runtse idon ta tana kiran sunan sa kafin ta soma tirjiya cikin jin
tsoron yanayin da Mukhtar ya koma mata yanzu, tuni ya balle bra din cikin dan lokaci da wayo
da dibara, yana mata hira mara kan gado a cikin kunnuwan ta, Amani ta soma kokarin janyewa
don ta soma tsorata, ya ce.
Oh Amani, Oh! Tafisu, don Allah kada ki bar ni yau, in kika yi min haka, zaki kashe ni da rai

na!
Mukhtar ya gama saddaqarwa yau in Amani ta zuqe masa a wannan halin, ko ta yi amfani da
damar ta ce zata rama abinda yake yi mata itama a kwanakin nan, babu shakka gawar sa zaa
dauka.
Tun tana neman zuqewa yana riko ta cikin lallashi da shafa gashin kan ta zuwa tsakiyar
gadon bayan ta, don ita bata tsammaci wannan a yau ba, don ta san bai da cikakkiyar lafiya
kuma, tsakanin ta da Allah jinyar sa ce tasa take yin duk abinda take yi, ba don ta ja hankalin sa
ba. Shi kuwa Mukhtar a yau kam duk wasu EXPERIMENTS DA YA DORA AMANI A KAN SU, YA
YARDA AMANI BATA FADI KO DAYA BA!!!
Don haka ya yarda wannan safiyar ta zama first morning din su maimakon first night da ake
cewa. Don ji yake kamar an kawo sabuwar lafiya an kara masa.
Kafin kace meye wannan har Amani ta soma yin laushi, sumbar da Mukhy ya soma mata ta
soma shigar ta, ta ratsa har cikin kwanyar ta. Saura kadan Amani ta sume sailin da Mukhtar ya
susuce a sumbatar kirjin ta, sai zuba sambatu yake cikin hargitsa gashin kan ta, cikin rokon ta
shima ya tuba. Ya daina muzanta mata. Can na jiyo Mukhy da wata yar murya tamkar ba tasa ba, yana fadi wa Amani cikin kunnen ta
Ya bi Allah ya tuba, ya mayar da duka kalaman shashasha, ballagaza, rakiyar mata da yake
kiran ta da su a baya, yayi rantsuwar cewa yau ya mayar dasu cikin cikin sa!.
Hawayen farin ciki suka zubowa Amani, ta dora hannayen ta a kan kafadun sa ta ce MUKHY,
I LOVE YOU YA MUKHY! Ta soma mayar masa da martanin sumbar kaunar da yake mata,
Mukhy ya karasa rikicewa Amani, don bai zaci wannnan alfarmar daga gare ta ba, ya ce.
Pls Tafisu hug me today, it is the beginning of our blessings, the truth which I. I must confess
loudly.
“ TAFISU KIN FI SAURAN MATA A ZUCIYA TA!.
Sai hawayen farin ciki suka shiga tsere suna diga dis-dis, daga idanun Amina-Amani, zuwa
kan kyakkyawar fuskar Mukhtar Issoufou Massaoudou, kawai sai Mukhy yasa halshesa yana
dauke mata su, silla-silla, wannan ya kara rikita Amani, ta kara sakar masa jikin ta sosai, ya
shiga yin yadda ya ga dama da komai nata, domin kalamai ne da bata taba zaton ji daga
Mukhtar ba. Tunda shi kullum burin sa shine yayi kasa da ita, don ya rage mata jin izzar wannan
perception din nata na tafi sauran mata!!!
Sune kuma kalaman da suka fidda duk wani tsoro da fargabar abun da ke ran ta, ta mika
wuya ta bashi damar da ya dade yana nema, wato ya tara da ita a lokacin da take son sa, so na
hakika. Ta mallaka masa zuciya da ruhin ta da gangar jikin duka a tare. Ta kuma karbi kowane
tayin sa da hannu bibbiyu. **** **** ****

At last, bayan komai ya lafa Amani na jiran Mukhy ya lalace a tarairaya da lallashin ta, ta
daga sabuwar shagwabar data kakalo, da kukan rakin da take sake babbakowa (bayan fa ta
gama taya shi komai an mori kuruciyar tare), cikin taimakon juna da kaunar juna, wannan karon
kukan nata na zallar shagwaba da raki ne, na azabar da ke ziyartar ta ne yanzu bayan kanwa ta
kar tsami, kwannafin su duka ya kwanta in ji hausawa, kishin sadakoki bay a gaban ta yanzu
sabida ita kan ta ta san a yanzu kam ta yi wa sauran mata zarrah tayi wa kowacce mace

fintikau! A zuciyar Mukhtar.
Ko da bai fada cikin nutsuwar sa ba, a yau ya fada cikin shidewar sa a soyayyah.

Mukhtar ya fito daga toilet yana goge kan sa da towel, ya kalle ta tana kwance tana sharer
hawayen da yaki tsayawa, ta kudundune jikin ta cikin duvet din sa, ta dauka zai lalace a
lallashin ta ta cigaba da shagwabewa yadda take so, amma Mukhy sai cewa yayi,
ragguwa kawai, sakaltatta, zaki tashi ki wanka ko bazaki tashi ba? Ko kina nufin daukan ki
zan yi in kai ki toilet din? To tun farko ni nace a yi? Ba ke kika ce kin yarda ba? Ni da bani da
lafiya ma, amma baki yi laakari da hakan kin tausaya min ba, ba saida kika yi disvirgining dina
hankalin ki ya kwanta. Amani ta daga kai tana kallon sa baki bude, hawaye na zuba, Mukhtar ya ce eh mana. Kin sa
yau na tashi daga suna na mai dadi Mukhy na koma Daddy (Baba). Besides, ni kam ai ban
shirya sallama daga kuruciya ta a yau ba, so na yi sai kin yi hankali mai yawa, kin kara nutsuwa,
kin tabbatar da Allah guda daya ne, amma yarinyar nan sai da kika san yadda kika yi kika
seducing mara lafiya, kika kayar kasa warwas, saboda kin samu sarbadeden saurayi a bagas!
Bayan duk cin mutuncin da kika gama yi masa, amma duka yau kin manta, kika saka shi a
daki kika more.
Ya yi mata murmushin sace zuciya, Anyway, AMANI you are a DARLING! Ko Sadaka sun zo
a bayan ki suke.
Ya sunkuya ya sumbaci goshin ta ya ce I love you with all my heart Amani, tun gani na da ke
na farko kin sani, na fara son ki ne from the very first time I saw you, ranar da na dawo daga
France ke kuma kika zo wani hutu, sai ya zamanto na fuskanci halayen ki sun saba da nawa,
na gane bazamu taba daidaitawa ba da wadannan halayen naki, don na tsani mutum mai
GIRMAN KAI, FARIYA, TAKAMA DA IZZA, a takaice halin ki ne kawai bana so Tafisu, tun daga
wancan lokacin, amma ba ke ba.
And today, Amani I love you more than any worthly earthly possessions, for the wonderful gift
I received from you, for the love we shared, it will continue to linger in my memory.
Ya sake kai mata wata warm sumbar a kasan cibin ta, wanda yasa Amani rufe idanu da
hanzari, cikin kunya da kuma jin dadin kalaman sa.
To amma me, duk ciwon nan da take ji a cikin jikin ta, Mukhtar ko ya sani ko kuma bai sani
ba? Zata iya cewa Mukhy ya so kan sa da yawa, duk da ya taba cewa he will not be selfish a
kan hakan, yau kam yayi son kai, don ta san bata yi healing from the first ba, lokacin da ta gane
neman tafiya karo na biyu yake yi duk kuwa da yana lallashi, yana yana kuma bada hakuri ta
hanyoyin nuna kauna da dama. Duk ta san kauna ce ta sa hakan, amma hakika ta tausayawa
kan ta domin ta ji jiki ba na wasa ba.
Tana so ta ce aa, tana so ta yi korafin ya bar ta ta samu hutu, at least ko zuwa gobe, amma
da ta tuna ‘sadakoki masu zuwa da abinda Ummami ta ce mata a kan halittar su, ai sai ta
gyagije, tare da bada sabuwar himma, wajen nuna rashin gajiyawar ta duk kuwa da cewa
Amani ta jigata yau a hannun Mukhy, ya mori auren sa da yayi missing sama da watanni biyu a
wunin ranar yau kadai.
The whole day for Mukhy!

***** ***** ****

Haka daren yau ma bakidaya Muktar ya hanata aikin komai sai nashi, bai bar Amani ta huta
ba har washegari yana amarci, haka basu je koina ba wunin yau, sun bawa juna lokacin su
gabadaya, ta yarda auren ibada ne da gaske, ibada mai zaman kan ta, ba wai zata ce jin dadi
ne zallah a cikin sa ba, kamar yadda take tunani a baya, akwai takura musamman da bata saba
ba. Amani ta yarda cikin kowacce ibada kuwa sai an saka juriya da sadaukarwa ga juna.

**** **** ****

D
uk yadda ta so da safe Mukhy ya gaya mata ya fasa karbar Sadaka, ko don wannan aikin
bajinta data kwana ta wuni yi masa, wuni guda da dare guda Mukhtar na shan amarci kamar
bazai ragewa gobe ba yadda yake so, ba tare da ya yi laakari da cewa, itama kamar shi, shigar
fari ce cikin situation din, kusan har ta ce ta samu tear, a yadda take jin radadi a tare da ita.
Abun na Mukhy duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login