Showing 1 words to 3000 words out of 18685 words

Chapter 1 - AMANI PART 4 FREE BOOK END COMPLETE BY SUMAYYA TAKORI.pdf





AMANI

4

Littafin



SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
takorikabara@gmail.com
MUKHTAR

H
ar ya isa sassan Ummami yana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin sa da Amani yan
mintunan da suka shige. Mukhtar yace a ran sa kenan gatan iyaye ma wani abu ne mai girma
ga dan adam! Da Maimartaba bai bijiro da zancen bashi Sa-daka ba, da bai san ranar da Amani
zata yi nadamar halayen ta har da abubuwan data yi masa irin haka ba, don shi har yanzu jikin
sa bai karbi ikirarin Amani tana son shi yanzu ba, ya dai ji ta, and he was puzzled, ya dai fi
yarda da cewa gudun kishiya ne ya ruda ta.
Bai dawo gidan ba ma don baya son ta sake saka shi gaba da kukan ta da fitinar ta, sai
lokacin da ya kintata cewa ta yi barci, don baya son ta kuma saka shi a kwana kada tayi saurin
samun lagon sa, da raunin zuciya ya wuni yau, sabida kasalar da nadamar Amani da kukan ta
suka saukar masa. Sai da ya dauke takun sawun sa kamar mara gaskiya da ya shigo falon da ya raba nashi da
nata. Kuma yana shigewa dakin sa ya rufe a hankali har da key, ba tare da Amani ta san
dawowar sa ba sam.
So yake ta koyi son nasa da gasken gaske, har ta zo tana kewar ganin sa, mai yuwuwa in ta
daina ganin sa ta yi kewar sa, don ya ga canji mai yawa ranar da ya dawo daga Burkina Fasso.
Amani kamar tayi hauka, ganin har washegari Mukhy bai neme ta ba, ga dakin sa ya rufe da
key, ta kasa gane a gidan ya kwana ko aah? Jikin ta ya bata kawai watakila an kawo sadakokin,
a can wajen su Mukhtar ya kwana, to a ina aka sauke su bata da masaniya?
Kafin garin Allah ya waye in ka ga yar Daddy bazaka gane ta ba, ta zama kamar kudin
guzurin da kullum ake yafita yake karewa.
Haka Mukhy ya dinga yi mata wannan batan dabon har kwana uku, ko sassan Ummami bata
iya zuwa yanzu don ta san sai ta tambayeta me ke damun ta. don Amani bata saba da shiga
damuwa ba a rayuwar ta, shi yasa yanzu data sameta ta kasa controlling din ta, gashi in zaa
kashe ta idan an tambaye ta meye damuwar ta ta san ba abinda zata ce yana damun nata din
sai kewar Mukhy. Tunda ta ajiye damuwar sadakokin sa aside, ta bar musu shi, amma hakika
rashin ganin sa (for good three days) dinnan yana azabtar da ita yadda bata zato a zuci da ruhi.

Da tunanin ta na yana can tare da sadakoki yana shan shagalin sa, shiyasa ta daina ganin sa a
sassan ta kwata-kwata.
Baba Sahura kuwa in ta zo bata ko bari su yi doguwar magana zata ce ta kyaleta ta, ta tafi
gunUmmami don Allah, bata son dogon surutu irin na Baba Sahura. Hatta Sugra da Tahirah sun
san uwardakin su ta shiga yanayi, ta ce kada ta kara ganin kowaccen su a gaban ta in ba ita ta
neme ta ba. Baba Sahura sai dai ta yi dariya, ta ce, ai wato shi Allah haka yake alamarin sa, duniya rawar yammata wai na gaba ya koma baya.
Amani ta zama daga kwanciya sai kwanciya bata umh bata umh umh, domin ta gama
gayawa ran ta an kawo sadakokin nan, an basu wani gidan, Mukhy yana can tare da su.
Da safe Baba Sahura ta shigo dakin ta don taga lafiyar ta yau da safe, ta same ta ta hada kai
da guiwa tana kuka tamkar marainiya, haushi mai tsanani ya kama Baba Sahura, sai ta kada
kai ta ce, lallai, aure mai ladabtar da mace, Uwa duk kin yi sanyi kamar ba Tafisun Alhaji ba, kin
koma talalabuwa, yo idan ma Sadakan ne aka kawo ai ba ta haka zaki gabza da su ba, tsaf kina
nan kina wannan doloncin zasu janye shi, ke kina nan kina cika bokiti da hawaye, ai ta shi tsaye
zaki yi ki zama kamar Ummami wajen karawa da kishiyoyi komin yawan su, in ya so mai karfi da
iya kissa da iya gado da iya kula da miji ta kwata.
Ba miji irin Maina ake sakarwa kwarkwarori a koma gefe ana kuka ba, ni wallahi duk kin
zama sullutuwa, wannan karfin ikon naki da izzar taki duk sun bar ki, a irin wannan lokacin
kuma suna da amfani, ni nafi son Tafisu ta baya ba ta yanzu ba da namiji ke neman kassarawa.
Sai ta ji tamkar Baba Sahura ta yi mata allurar sanya kuzari, da gaske kishi da soyayyar
Mukhtar ke neman kashe ta a tsaye in tayi wasa, ya gama narka Tafisu ya gama kashe lagon ta
da soyayyar sa, shi bai san ma tana yi ba, yana can yana murzar kuruciyara sa da kyawawan
yammatan abzinawa har biyu. Shin da soyyar sa da ke cin ran ta, da kishin Mukhy da ke
azabtar da ita zata ji ko da bakakaen maganganun Baba Sahura na yau daban na gobe daban?
A wani bangaren, ga kuma kwadayin son ganin fusatattar kyakyawar fuskar sa da ke addabar ta
a yanzu.
Don haka yau Tafisu ta kwarara zuciyar ta, ta kuduri aniyar ko zata kwana a zaune zata hana
idon ta barci zata yi hakan, don ta bincika ta ga inda Mukhtar ke kwana. Aka ce sa kai ya fi
bauta ciwo.
Kuma shima wani ikon Allah yau ya kasa yin daren da yake yi a gun Ummami don kan sa
ciwo yake yi kadan-kadan, kuma shi kan sa ya gaji da boyon da yake yi mata don yana takura
kan sa a daki ne, domin ya gane wahalar da yake baiwa zuciyar sa ba kadan bane, ko ya ki ko
ya so, yayi kewar kyawawan idanun Tafisu, masu kama da kwan zabo, koko dan itacen nan na
almond.
Murmushin ta da bata fiya yi ba sai wuri ya kure, da takun tafiyar nan nata mai kama dana
macen Dawisu don rangaji da iya takun tafiya mai daukar hankalin namiji.
Mukhy ya sa hannu ya rike kan sa da ke sarawa tamkar zai rabe gida biyu. Ya ce.
Wash!
Ummami ta juyo tana tambayar shi lafiya kake rike kai? In barci kake ji ka tafi ka kwanta
mana? Nima yanzu gun Mai zan wuce, kwana biyun nan na rasa gane kan ka, duk ka bi ka
hanani sakat da binbini, duk inda nayi sai ka bi ni cikin gidan nan Maina kamar yaron goye? Ni
ina matar ka ne ma kwana biyun? Itama na daina ganin gilmawar ta a sassa na sai kai uban
yan binbini, bita zai-zai.

Mukhy yayi murmushi bai ce komai ba yana kara dafe kan sa da ya kara sarawa.
Na rasa dalilin da yasa kake yin dare yanzu a waje na ko wajen Mai, kai da aka ajiyewa
amarya ko sati bata rufa ba, amma sam baka dokin ta, anya Maina? Lafiya?.
Murmushi ya sake yi kadan, ya ce Ummami ai kanwa ta ce wane irin doki kuma? Ni kanwa
nake yi da ita, ba amarya ba.
Tun daga nan Ummami ta ke fahimtar wani abu is fishy a tsakanin su a kwana biyun. Ta
fahimci tun ranar da aka yi zancen sadakoki ne Amani tayi mata batan dabo. Don itama Tafisun
kwana biyu da ya tsiri shigowar ya jima mata a sassa har wani lokacin yayi barci ya farka, ita
kuma ta daina shigowa kwata-kwata. Baba Sahura dai ta tabbatar mata Amani lafiya take, shakiyancin ta ne ya motsa ko kofar falo
ta daina fitowa. Ta kori su Sugra ma.
Ya shiga gidan sa ko in ce bangaren sa cikin jin ciwon kan na karuwa masa, shi kan sa ya
san akwai matsala a tare da shi yau, don duk dauriyar sa ta kare, da gaske daurewa kawai yake
amma tunanin Amani da yake kwana da shi yak e tashi da shi da son kasancewa da ita ko sau
daya ne a rayuwar su, ya fara haifar masa da rashin sukuni a cikin jikin sa, zai ratsa ta falon
karshe wanda a nan dakunan barcin su suke, ya ga Amani zaune firgai-firgai tana dakon jiran
shigowar sa, ta ki shiga dakin ta balle ta kwanta, ta yi rantuwa yau sai ta ga gadon barcin
Mukhy da sadakokin sa.
Sai ya sa kai zai wuce ta ba tare da ya ce mata komai ba, but hes touched da ganin yadda ta
rame ta yi zuru-zuru kamar ba yar gayun nan Amani Faskari ba, hakan ya taba zuciyar sa sosai,
kuma hakan yasa nan take ya tuna Alhaji, da yadda yake lelen abar sa, sai ya ji kamar baya
kyautawa abinda yake mata, kamar yana cin amanar Alhaji Usman, duk da haka har yau Amani
bata yi hankalin da yake so ba, shi kuma in har ba ya tabbatar da canzawar ta da halayen ta da
baya so, ko da ba duka ba, tunda ance hali zanen dutse ne, amma a kalla ta cire wanda Allah
baya so (girman kai), izza da fariya da tunanin ta na ta fi kowa, yana so ya tabbatar da cewa
tana mishi so na hakika na fisabilillah irin wanda zata sake da shi a shimfida da zuciyar ta da
gangar jikin ta bakidaya, ba don shaawar gangar jikin ta na yar adam ba, sai don so da kauna
na domin Allah, sannan ne zai iya sakin jiki da Amani su fara rayuwar da yake musu tanadi shi
da ita.
Makeken Gadon sa ya haye ya kudundune yana amsar zafin da jikin sa ya dauka, jikin sa har
yana rawar dari, domin tuni zazzabi ya kawo masa hari, ya ja bargo ya kudunduna har kan sa.
Amani duk da bai kula ta ba, ya wuce ta ne a zaune sai bata yi kasa a gwiwa ba wajen biyo shi
dakin, ta yi saa bai saka key din ba yau, don bai san inda kansa yake bama, amma kuma bata
ga wata sadaka a dakin ba sai shikadai.
Amani har da sauke wata lafiyayyar ajiyar zuciya, rigimar da ta shigo da ita ta nema ta rasa,
ko don irin kwanciyar da taga Mukhy yayi da kudunduna cikin duvet kullihin sa ko AC bai kunna
ba. Sai jikin ta yayi dan sanyi, kuzarin balain data shigo da shi yayi kasa sosai, ko daga irin
kwanciyar da Mukhy yayi yau zaka fahimci bashi da lafiya. Farar rigar barci ce a jikin ta iya guiwar ta mai santsi, amma ta daura zanin atamfa a kai,
gashin kan ta ma duk ya susuce babu taza, babu kitso, tafi dacewa da a kira ta da birkitacciya
Amani yanzu ba yar gaye Amani Faskari ba, sabida yadda ta koma sam ba nutsuwa da walwala
da farin ciki a tare da ita, duk a dalilin rashin samun kan Mukhtar Issouffou Massaoudou. A lokacin da zuciyar ta ta afu a kan sa, da son ganin su a wani matsayi na cikakkun mata da

miji cikin kauna da soyayya kamar kowadanne maaurata, ba wannan matsayin da suke kai a
yanzu ba, kamar dai Mai Diffa da Ummami, kai bazaka ce sun tsufa ba, kullum cikin kaunar juna
da tattalin juna suke, da ka zauna da dayan su sai ka ji ya ambaci dayan a cikin zancen sa na
koyaushe, ta hanyar bada misali da kyautatawar da dayan su ke yi masa. Yadda son Mukhy da kishin sa suka taru suka sukurkuta Amani sai ta koma kamar ba yar
gayun nan kuma yar kwalisa (wanke hannu kafin ka taba) da ya sani a gidan Hon. Usman mai
suna Amani Usman Faskari ba.
Amma yanzu kam fama yake da kan sa da ya tambaye ta dalilin wannan ramar haka, da
dalilin susucewar ta, to ko magana baya son yi, ya rasa dalilin wannan masassara data same
shi yanzun nan, jikin ta duk yayi sanyi da yanayin da ta gan shi a ciki na rawar dari don bata
taba ganin sa cikin irin sa ba, sai ta zauna a gefen gadon jikin ta ya dau rawa itama, murya a
sanyaye kuma tana yar rawa ta ce.
Ya Mukhy are you alright? Why are you shivering?!
Ya ce umh cikin karfin hali, sai ta zauna a daidai kan sa ta ce. Na ji dadi yau ka dawo da
wuri, amma kamar baka da lafiya sai itama ta soma karkarwa, ta tambaye shi da me zan iya
taimaka maka? Akwai magani a dakin? Ya sake cewa umh da murya irin ta mai jin zazzabi,
Amani ta gama firgita, ta yi kwanciyar yan bori a kusa da Mukhy don ta gane ba kalau yake ba,
ko ta hanyar saukar numfashin sa da ke sauka a kai-akai cikin hucin zafi, don haka ta ji ta kasa
korafin ina yake kwana da ta so yi, ko tambayar sa an kawo masa kwarkwarorin ne ta daina
ganin sa yana kwana a nan?
Maimakon hakan, sai ta samu kan ta da cigaba da nacin tambayar sa Yaya Mukhy, don Allah
da me zan iya taimaka maka? Kwarai a wannan yanayin yana bukatar taimakon nata, amma
kuma...
Im not well! Ya bata amsa da kyar, ta kara matsowa daidai kan sa, bakin ta tasa daidai
kunnen sa ta ce me yake damun ka Ya Mukhy? A gajarce yace sanyi. Amani sanyi nake ji, wani
irin sanyi har cikin bargo na, duk da na rufa, amma kamar ina ciki kankara still, ko dai mutuwa
zan yi? Amani ta kara gigicewa ta mike a sukwane to bari in kashe maka A/Cn, ta mike da
niyyar tafiya kashe AC sai taji Mukhtar ya riko ta da hannnun hagun sa da ya dauki dumi da
karkarwa, ta juyo ta dube shi idanun ta sungama kwalalowa, cikin karkarwar jiki ta tsaya, domin
gabadaya ta rude ta rasa abin yi, sai ta ji muryar Mukhtar a hankali yana fadin.
“Amani sammin dumin jikin ki, it wil be absolutely okay for me.
Ta so ta gane me yake nufi wato dumin jikin ta yake so, shi kadai zai taimaka masa ya samu
rangwamen sanyin da yake ji, amma da ko kusa bata kawo hakan a ran ta ba kuma a rude take,
sai bata gane me yake nufi din da dumin jikin ta ba, don haka ta tsaya tana dawurwura, sai ji ta
yi Mukhy ya ja ta a hankali ya kwantar, ba tayi musu ba ta bi umarnin sa, sannan ya daga bigilar
rigar jikin nata ya cire ta ta sama, ya warware zanin jikin ta da kyar cikin rawar hannu ya jefar da
shi a kasa, da wata irin azama Mukhtar ya manna Amani a jikin sa, wuyansa da sajen fuskar sa
cikin nata wuyan. Ya kuma kudundune su cikin bargon tare. Wato su sha zafin zazzabin tare. In
ma mutuwa zai yi, yana fatan ya mutu manne ciki jikin ta.. Ko hakan ya sa su tashi tare ranar
lahira a matsayin mata da miji, tunda a duniya Allah bai yi zasu rayu tare ba.
Kusan zafin jikin Mukhy jikin Amani ya dinga komawa, irin yadda ya mannata a jikin sa ya sa
komai nasa ya fara sauyawa, hatta saukar numfashin sa ya sauya, Amani ta samu kan ta da
kara rungume Mukhtar, suna raba zazzabin nasa tare. Duk da cewa kuwa ba karamar wahala

take sha ba, ga zafi kamar ya kashe ta.
Sai tsakar dare suka samu zazzabin ya soma sauka, ta gane hakan ne da yadda ya soma
yanka gumi yana jika ta, amma hakan bai sa Amani ta tashi ba, duk kuwa da cewa ba barcin
take yi ba ita har tsayin lokacin. A yau ji take wata irin nutsuwa na shigar ta, kasancewar ta cikin
wannan intimacy din na body contact tsakanin ta da mijin ta Mukhtar Diffa, soyayyyar Mukhtar
da wata gigitacciyar kaunar sa na kara ratsa ta, yanayin jikin ta ya soma sauyawa itama ta kara
kankame shi, shi kam zuwa lokacin ya samu barci mai nauyi, sai ta kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login