Showing 1 words to 3000 words out of 40544 words
Chapter 1 - Aishah-Saddiqa book part 4 end Book complete by Sumayya Takori Kabara .pdf
AISHAH-SIDDIQAH
4
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
babbangoro2015@yahoo.com
TUNASARWA/JAN HANKALI
Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata
kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba.
Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa
cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da
kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa.
Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya
guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu
ga junanmu.
Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba.
Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa,
wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde.
In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko
mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi
Atqaakum”.
Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya
Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna.
Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage
shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu
hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da
haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a
kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama
cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada.
–Takori Sumayyah AbdulQadir.
SADAUKARWA
Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI’S
LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki.
KIYAYEWA
Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce
kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma
abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali.
GODIYA DA JINJINA
Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari,
tacewa da gyarawa. Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad,
Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira.
In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa
namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH.
KAFIN MU FARA INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a
wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements
ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control?
Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA
LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da
kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo
ku bani labari.
-Takorinku
AISHA SIDDIQAH 4
H
aseenah na ganin fitowarsa ta mike tsaye with great excitement a kan fuskarta. A take sai Aisha
taga Hamma ya wani irin daure fuska. Gabadaya ya koma babu annuri. Ya fito a basarakensa
sosai. Yau sai taga ma Hamma yafi mata kama da yarbawa akan Fulani. Fuskar nan ba rahma
ko kadan ko kankani. Yace cikin wata irin murya. “What are you doing here?” Haseenah tace “kayi hakuri Prince, just give me few minutes of
your time. Ta’aziyya ce nazo nayi maka na Emir. Aunty Taiwo ta gaya min kana Argentina,
nikuma na zo yin wani project daga office dinmu, nace zan zo har gida in yi maka ta’aziyya
kuma in yi amfani da wannan damar in baka hakuri Prince. Am sure she told you sakon dana
bata gareka”.
Sai Hamma ya zauna gefen Aisha yana kokarin cooling anger dinsa, ita kuma Aisha taji
kamar an kada mata kararrawa a cikin kanta, domin nan take ta ayyana itace tsohuwar
budurwarsa Haseenah Ambursa, wadda Kiki ta bata labari. Don haka nan take sai ta mike,
amma sai Hamma ya rike hannunta, ya saka idanunsa cikin nata yace “ina zaki mu da zamu fita
kuma?” tace “naga kayi bakuwa ne Hamma, zan kawo mata ruwa da lemo ne in baku wuri”.
Sai Prince yace mata “zauna, ba shan ruwa ya kawota ba, yanzu zata tafi”.
Ya mayar da ita zaune inda ta tashin, zuciyar Aisha tayi mata nauyi, ba don komai ba sai don
tuno soyayyar da ake bata labarin Hamma ya yiwa Haseenah, har shine silar da yaki aure
shekaru goma sha uku, a zuciyarta tace ita daman matar cushe ce a gareshi, kila yanzu
Haseenah ta dawo rayuwarsa kenan, dan bond din da suka fara developing ita dashi zai bi iska.
Zai tashi a banza. Mai wuri ya zo mai tabarma sai ya nade kayarsa.
Sabon takaici ya lullubeshi na yadda akayi Haseenah ta samu address dinsa na Argentina
gun Taiwo, ta shigo gidansa na Sunnah bada izninsa ba. A ran sa yana ayyana yadda zai ci
uwar Pareto ciki da waje, da yake budewa kowane kare da kowanne doki gidansa ba tareda ya
masa izni ba.
Haseenah ta roki samun privacy na tanaso suyi magana ita da shi, wani asararren kallo yayi
mata yace.
“I have got nothing to hide from my wife”.
Nan duk Haseenah tabi ta sha jinin jikinta, cewa wannan sabon Prince Kehinde
Abdulrasheed ne, ba wanda ta dade da sani ba.
Jikinta yayi mugun sanyi. Ala dole ta fara fadin abinda ya kawota akan idon Aisha.
Na farko ta bashi hakuri, kan abinda ya faru shekaru sha uku a baya, tace babu ranar da
bazata wayi gari ta kuma wuni tana nadama ba, amma bata da excuse, bata ma son kawo shi.
Ta yarda kaddararsu ce tazo a haka amma ba don rashin so tayi masa abinda tayi ba”.
Sai Haseenah tayi shiru, sannan ta kalli idanunsa tace “Kehinde, you will always be the one
that has got my heart, and I am so sorry for being the reason you stayed this long without a
wife.
Na tabbata nima hakkinka keta bina na kasa aure sai yanzu, ina ji a raina kullum in har ba na
nemi gafararka ba zan fara rayuwa ne akan karya. Ka yafemin. Yarinta ce da shaidan suka taka
rawarsu gareni a lokacin.
Amma na maka alkawarin cewa na dau darasi na domin Tokumbo bai aure nib a bai kuma
kara waiwayata ba bayan ya gama kwasar rabonsa a tare dani”.
Prince ya kalleta sai yaga tana share hawaye, a zuciyarsa yaga zallar nadama a tare da ita
da talalar Ubangiji bayyananniya. Haseenah duk ta tsofe, wannan kyan duk ya dushe. Ba dai
cikin wahala take ba, amma kuma duk kyannan na kuruciya babu shi a tareda ita.
Sai kawai ya daga kai ya kalli Aisha, a take sai yaji duk wani bakin cikinnan na Haseenah
yana ‘melting’, har ya zamo babu shi babu sauransa ko kadan a tare dashi.
Yayi duba ga irin kyawun da Aisha tayi a gabansa, tana sanye cikin shirin atamfa ‘super
exclusive, looking beautiful and innocent, yaga cewa in bai yafewa Haseenah bama kamar ya
yiwa Allah butulci ne. Saboda ya bashi abinda ya fita sau dari. Wannan shi ake kira “blessing in
disguise”. Da wannan tunanin sai kawai Prince ya dubi Haseenah yace.
“Haseenah Allah ya yafe mana bakidaya, yes I was hurt, amman in gaya miki gaskiya I have
no ill feelings towards you now, Allah ya wanke min zuciya yayimin sakayya da
AISHAH-SIDDIQAH...”.
Ya dan kalli Aisha da itama shi take kallo, yace “na yafe miki Haseenah ko don albarkacin
Aishah.
Saboda ba don kinyi abinda kika yi din ba, da ban hadu da ita Aisha ba, so in this way, I must
say a big THANK YOU! Allah kuma yasa ku zauna lafiya keda mijinki din”.
Prince sai yaga Haseenah tana kallonsa kawai, ta sake share hawaye tace “thank you”. A
ranta tana mai kissima babban rashin datayi na Prince Kehinde, wanda ta tabbata ko shugaban
kasar Ingila taaura bazata maida kamarsa ba.
Prince ya mike ya dubi Aisha yace “muje ko?” Sai Haseenanma ta tashi tace “to na barku
lafiya, Madam Aisha bye, till next time”. Prince yace “a’ah Haseenah babu next time, please,
kamar yadda nace “I have no ill feelings towards you, haka babu alaqa, na yafe miki, but please
don’t show up in our house again”. Tace “in sha Allah. You really deserve to be happy, Aisha congrats to you, you don’t know
what God did to you!”.
Daga haka sai tayi wani murmushi mai daci ta tafi.
Aisha a ranta taji dadin yadda Hamma ya hanata tafiya, ya girmamata a idon Haseenah,
amma duk da haka wani irin kishin Haseenah take, ta hau ayyana irin mugun son da Prince yayi
mata, data tuna hakan sai taji wani bala’in haushi a makogaronta.
Ta koma tana cewa a ranta meyasa ma take jin haushin? Itada ba son Hamma take ba. wata
zuciyar tace “ai dai mijinkine da so ko babu SO. Haka dai, duk ta zama confused, taga cewa ko
Ishaq da take ikirarin ta so, bata jin wannan zafin zuciyar a kansa da wata.
Haseenah na fita, Aisha ta zame hannunta daga na Hamma, ya kalleta yace “muje” tace
“nidai na fasa zuwa ko’ina, sai ka dawo kawai, I don’t feel like going out any more” Hamma
yace, “Why?” tace “hakanan, ban jin dadi sai wani lokacin”.
Ta soma warware daurin kallabin data yi.
Nan Hamma yaso ya gane meke faruwa. Ya tuna ranar da yaji tana maganar Ishaq, abinda
yaji a ransa, balle ita yau dungurungum Haseenar ce tazo. Sai yace.
“Aisha listen to me, Haseenah wata long chapter ce a rayuwata da bani ko son tunawa, don
Allah ki fahimta, don’t read too much into it”.
“Bakomai” inji Aisha. “Ba sai ka min bayani ba Hamma, matar so ce tazo ban hakuri, love of
your life akace ko…. so don’t owe me any explanation.
Ni daman ai matar huce haushi ce, so me zai kai nima jin zafin zuwanta? Har zaka tsaya
bayanai. Ba komi Hamma bari in yo sallah”.
Ta wuce.
Prince yana kiran sunanta “Aisha, Siddiqah…Aishah…” tace “ba komai Uncle”.
A ransa yayi tsaki yace shi dai Allah ya isa tsakaninsa da Taiwo, ya samu sun fahimci juna
yana zaman zamansa ta kwanto masa kura.
Yace to wai ita Aisha yanzu har ta san kishi? Ko dai itama ta fara sonsa ne? sai yace “shima
fa haka yaji ranar da tayi maganar Ishaq.
Haka Hamma ya zauna yanata tsaki buhu-buhu shikadai.
Yaje dakinsa yayi sallah ya dawo dakinta yayi knocking, tun kafin ta bashi iznin shiga yasa
kai.
Yana shigowa tana fitowa wanka daga ita sai tawul, ta juya a firgice zata yi baya ta koma tace
“Subhanallah Uncle lafiya?” A ransa yace “wato Haseenah ta zo, kalmar Uncle ta dawo, kai!
Taiwo Allah ya isa!”.
Ashe a fili Hamma ya fada, yana bude ido sai ya ga Aisha bata nan ashe ta koma toilet din ta
rufe ta bar shi a wurin.
A wunin ranar bakidaya abun duk ya dameshi, gashi Aisha taki yarda ta tsaya ma yayi mata
bayani.
Ta zama wata sumu-sumu a gidan. Ta takure kanta, abin duk yabi ya addabeshi.
In ya tuno kalmar nan ta “Haseenah matar so” da tace sai yace “Omooo!”
Daga ranar da Haseenah tazo, dan taya shi kwanan da ya samu ana yi duk an daina. Ta
koma dakinta bakidaya.
Yau Hamma ya dawo can dare, ya zo ya sameta a falo tana barci a kujera, ya tasheta yace
“Aisha tashi muje daki ki kwanta mana” Aisha ta bude ido fal barci, tace “yau dai ka kwana a
gadonka Uncle”.
Ya rasa yadda zaiyi da ita dole ya wuce ya kyaleta, don ta kwashe dankwalinta ta koma nata
dakin.
Washegari Nenne ta kirata Aisha ta amsa suna gaisawa, Nenne ta ji ta wani iri, da ta matsa
da tambayar meke damunta? Aisha tace bata jin dadi ne.
Hajiya Nenne mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta dauka ciki ne keda
Aisha ta soma murna baka da zuci.
Ta kira Prince tace “Hammansu ashe Aisha bata jin dadi?” Sai kawai yace “eh” sai gata ta fito
falon domin ta dora abinci, yana kallonta lokacinda take fitowa suna wayar shi da Nenne.
Sai yace da Nenne gatanan ma ta fito, ina jin girki zata yi”.
Sai Nenne ta hau fada “itada batada lafiya zaka sa girki? A barta ta huta. Naji muryarta tayi
kasa sosai. Kai da zakayi ta lallabata Hammansu, kasan me juna biyu hutu takeso”.
A ransa Prince yace “me Nenne ke nufi ne?”
Ita Aisha bata ji ba, yace “juna kuma Nenne? What’s that?” tace “kunje asibiti?” yace Nenne
daga kwana uku ne zuwa yau fa” Sai Nenne ta hau fada tana cewa “har kwana uku tana fama
da ciwo baku je asibiti ba? Ina Aishar? Bani ita” yace “gata” yana karasawa kusa da ita da
wayar a kunnensa. Nan Prince ya mikawa Aisha wayar, Nenne ta hadasu su duka tana surfesu da fada, “Aisha ki
ajje sokoncin nan kuje a dubaki, haka zaki zauna da ciwo? To dai ciki ba’a masa haka, Allah ya
raba ku lafiya”.
Ai jin ciki sai Aisha ta yanke da kakkaifar wukar hannunta bata sani ba, tayi maza ta jefar da
wukar, tsabar firgici, shima Hammah yace “ciki kuma Nenne?” tace “eh mana. Ba shine ba?” Sai
yayiwa Aisha wani kallo, ya kece da dariya.
Yace “Nenne yaushe tace miki ciki ne da ita?”
Sai Nenne tayi shiru, sai kawai Hamma ya sake fashewa da dariya ya kashe wayar.
Aisha itama abin ya dan bata dariya, ta dan dara ba shiri, ta kalli Hamma yana kara
kyalkyacewa (he looks amazing), kamar bai ma san kalar kyan da far’a take yi masa ba.
A wannan dan dakikan da take kallon Hamma Prince, sai taji (her whole world feels
complete). Wannan din mijinta ne da ya hada komai da dan adam ke burin samu, kyau da
nagarta, nasaba, ilmi da arziki da kuma kyan hali.
Sai kawai zuciyarta ta hasaso mata haka yayi rayuwar soyayya da Haseenah, ita to da aka
cusa masa ma ya sake yanzu yake kula da it aba karamin dadi take ji ba, to wannan wane irin
dadi Haseenah tayi ta ji a ranta sanda suke tare suke soyayyah yana kula da ita?
Sai kawai far’arta ta koma, Siddiqah ta mayar da annurin fuskarta ta sake dinkewa tsaf.
Ganin haka sai ya kashe gass din data kunna, ya kama hannunta suka wuce (sitting room).
A tare suka zauna a two seater, Hamma yace “Aishah, bana son mu gina rayuwarmu akan
zargi da rashin communication.
Ko me nayi miki banso kina fushi dani, just tell me. Kina ji na?” Aisha tace “yes” don taga ya
kawar da wasa, he is serious now.
Yace “menene yake damunki tun ranar can kike ta attitudes?” tace “babu komai” “ko ki fada
min ko in kira Nenne, ita in ta tambaya na tabbatar zaki gaya mata”